TUNAWADA WAƘI'AR ZARIYA 2015

 TUNAWA DA WAKI'AR ZARIYA 2015



— Saifullahi M Kabir 


Dukkanmu mun ji cewa a ranar Alhamis, 28 ga Safar 1437, daidai da 10/12/2015, bayan kammala zaman juyayin ranar wafatin Manzon Allah (S), Shaikh Zakzaky ya bayar da sanarwar taron saka tutar Maulud, wanda yace za a gudanar a yammacin ranar Asabar 1 ga watan Rabi'ul Awwal, 1437 (12/2/2015).


Wanda a shekarun da suke gabanin wannan shekarar, sojoji sun saba gabatar da bikin yaye sabbin kuratan sojojin a Zariya a duk karshen shekara, a ranar Juma'a da safe. Sai dai a wannan shekarar, sai suka mai da bikin yayen nasu zuwa ranar Asabar 12 ga Disambar 2015, kuma da yammaci, maimako Juma’a da safe kamar yadda suka saba gabatarwa a tsawon shekaru. 


Wannan ya ba su damar ya zama rana da lokacin bikin nasu ya yi daidai da na taron sauya tutar Mauludi da Harkar Musulunci ta ayyana za ta gabatar a Husainiyyah Bakiyyatullah a wannan ranar.


Harka ba ta yi tunanin dage taronta a wannan ranar ba, ko daukar wani mataki na musamman, ganin cewa wuraren da za a gudanar da taruka biyun ba kusa suke ba, don haka babu wani abu da zai hada masu gudanar da taron sauya tuta da masu yayen sabbin kurata. Kuma su wadannan sun saba yi ne da safe, bikin sanya tuta kuwa ana yi ne wajen karfe 5:00 na yamma.


Sai dai wani abu da ba a yi zato, ko tsammani ba, don in ma hari ne, za a tsammaci za su kawo shi ne a daidai lokacin da aka fara taron. 


Amma kawai da misalin karfe 12:15 na ranar Asabar din, wata babban motar Sojoji ta zo ta sauke wasu dandazon kuratan sojoji dauke da bindigu, tare da akwatunan harsashi, a daidai gaban Husainiyyah Bakiyyatullah. Don haka abin da ya yi matukar ba 'yan'uwan da ke wajen mamaki.


An yi kokarin tuntubar su dalilin kawo su gaban Husainiyyah a daidai wannan lokacin, amma sai suka fara harbi a sama. Daga baya sai suka fara kewaye wajen suna harbi, yayin da 'yan'uwa suka bukace su, su matsa daga gaban Husainiyya.


Bayan kamar awa guda da faruwar haka, misalin karfe 1:00 na rana, sai ga tawagar Janar Tukur Yusuf Buratai ta biyo ta wajen Husainiyyar da sunan wucewa. Kai ka ce tawagar ta Shugaban rundunar sojojin Nijeriya ba ta san abin da ya faru a wannan wajen kimamin awa guda da ya gabata ba, wanda ka'idar tsaro zai tilasta masu barin bin hanyar, su koma su bi inda babu kowane irin barazana.


Zuwan Sojojin, tare da masu daukar hotuna cikin kakin sojoji, sai suka shirya wani abu kamar wasan kwaikwayo. Suka yi fuska, tare da nuna rashin sanin faruwar wani abu da wasu kuratan sojoji suka gabatar a wajen kafin zuwan su. 


A yayin da wasu 'yan'uwa suka tunkare su don su ji ko da me suka sake dawowa wajen? Sai wasu jami'an tsaro a cikin rigar 'yan'uwa Musulmi (kamar yadda Shugaban DSS na Zariya ya bayyana a gaban JCI cewa akwai mutanensu a cikin 'yan'uwa a wannan ranar a Husainiyyar) suka rika ihu, tare da daddaga sanduna. Nan take sojojin suka bude wuta kan mai uwa-da-wabi.


Bayan bude wutar, tawagar ta Buratai ta wuce, sai wadancan kuratan sojojin da aka kawo da farko suka ci gaba da kewaye Husainiyyah, aka rika karo masu karfi. A yayin da suka bi suka kwashe gawawwakin wadanda suka harba, suka tafi da su barikinsu tun a wannan lokacin.


Na san duk abubuwan da suka faru a Husainiyya a kan idon wasu ma daga yan uwa da ke wannan zauren ne. Don haka in abin wata rana mu basu dama ne za mu ji bayanai daki-daki akan abin da ya faru din.


Duk da wannan abin da ya faru a zahiri, cewa Sojoji sun kawo mana hari ne, amma a shirin rana na BBC a wannan ranar, sai ga hirar Kakakin rundunar soja na wancan lokacin, S.U Kukasheka, inda yake bayyana cewa, wai an yi kwanton-bauna ga Shugaban rundunar sojoji ne, har ma ya tsallake rijiya da baya. 


Kamar yadda duk muka gani cikin cikakken bidiyon wannan harin da Harka Musulunci ta saki daga baya, Soja sun ci gaba da kewaye Husainiyyah, tare da harbin duk wanda suka samu a kewayenta, har zuwa karfe 5:00na yamma, lokacin da Gwamnan Kaduna, Nasiru Ahmad El-Rufa’i ya zo wajen. Bayan magana da ya yi da Jagororin Sojin, sai ya yi gaba. Wucewarsa ke da wuya suka kara tsananta harbe-harbe a Husainiyyar, tare da yunkurin shiganta ta kowane hali.


An ce Elrufai ya kira su Malam (H) a ranar da yamma kafin ya zo Husainiyya wajen Sojojin, da ya kira, ya gabatar da kansa ga Malam, sannan ya masa magana a kan cewa ya ji wani abu na faruwa a Zariya. 


Malam ya bashi amsa da cewa muna da taro ne na saka Tuta a Husainiyya, kuma bikin ba zai wuce minti 30 ba, daga 5 zuwa 6 na yamma an gama. Amma yanzu muna da labarin Sojoji sun zo gaban Husainiyya, sun kewaye ta, kuma har ma sun harbi yan uwa da dama, sun sace wasu bayan sun harbe su sun ji musu rauni, sun tafi da su.


Elrufai ya cewa Malam yana hanya zai zo Zariyan, kuma in ya zo zai nemi Malam din. Amma tsinannen mutumin nan da ya zo sai bai kira din ba, bai je ba. Sai aka ga ya je wajen Husainiyya ya yi magana da Sojoji, ya wuce Bariki sannan ya bar garin.


Har ila yau, Jagora (H) ya je Makabartan Darur Rahma don ziyarar Shahidai a ranar Asabar din da yammaci, a daidai lokacin da Sojoji sun yi harbi sun kewaye Husainiyya. Ya fita daga gida ya je wannan ziyarar, har ma aka ce ya shimfida musu Tutar da za a dora din ya yi Addu'o'I kamar yadda ya saba.


Bayan dawowa, su Malam (H) suna ta tunanin ko za a samu fita zuwa saka Tutar, don sam ba a yi tsammanin mutanen nan sun shiryawa yin barnar da ya wuce tunani haka ba. 


Amma daga baya aka tabbatar da ba hanyar tafiya zuwa Husainiyya, don haka ba zai yiwu a je ba. Har Magrib ta yi, aka yi Magariba da Isha, aka cigaba da jira.


Waki'ar da ta faro a Husainiyyah da ke PZ da rana, kwatsam karfe 10:30 daidai na dare sai ga Sojoji sun kawo hari gidan Shaikh Zakzaky a Gyallesu, suna zuwa suka fara harbi ba kakkautawa, har suka kunna wuta a wani shago da ke wajen Banaden, wanda suke amfani da wannan hasken wutan suna seta yan uwan da ke kan Layin suna harbewa.


Zuwa karfe 11:30, awa guda kenan, sun harbi yan uwa kusan 40, kuma cikinsu 11 sun yi shahada an iya kawo gawargwakinsu an aje su. 


Cikin Shahidan na farko a Gyallesu har da su Malam Hamza Yawuri wanda ya je tare da wasu Ba'adin yan uwa, da nufin ko za a samu magana da Sojojin a ji me ya kawo su. Sai suka bude musu wuta, suka harbe shi a kai, nan take ya yi shahada.


Zuwa karfe 12 na dare muka gani a 'Internet' ana ta Muzahara a ofishin jakadancin Nijeriya da ke London, na Allah wadai da abin da ke faruwa a Nijeriya na yunkurin kashe Shaikh Zakzaky. 


Ba jimawa sai yan uwa na Kano ma suka fito Muzaharar, tare da Shaikh Turi, can sai sauran garuruwa ma yan uwa suka fito birni da kauyuka suna ta Muzaharar Allah wadai da harin. 


Amma duk abin da ake din nan, da sanin duniya baki daya a kan halin da ake ciki, bai sa jabberan mutanen nan sun janye ba.


Wani abu da bana mantawa da shi sam, shine yadda ya zama ba a yi awa biyu muna ganin hotunan Muzaharar yan uwa a Kano tare da Shaikh Turi ba, can zuwa karfe uku saura na dare sai ga Malam Turi ya zo Gyallesu. Kuma yana zuwa sai ya wuto kai tsaye zuwa can wajen Banaden, ya fuskanci Sojojin a yayin da suke harbi ba kakkautawa. 


A daidai wannan lokaci, suna saka Tociloli ne masu haske suna haska tsakiyar Layin, suna ganin mutum a tsaye sai su Saito shi su harbo shi. Muna kwakkwance sai muka ji ana cewa ku tashi, Malam zai wuce. Ku ba su kariya.


Gabana ya fadi sosai. Wane Malam din kenan? 


Muna tashi muka ga ashe Shaikh Turi ne. Ya dage yana so a bar shi ya je inda sojojin suke. Muka ce Malam ai ba zai yiwu ba. Har wani dan uwa yace masa, Malam dazun nan fa su Malam Hamza suka je da nufin su tattauna da mutanen nan a ji me ya kawo su, kan su karisa suka bude musu wuta suka kashe shi. Ku yi hakuri Malam, da ma da rana ne, ido na ganin ido dai mu barku ku je.


Malam Turi yace, zan je ne na wa 'yan uwa bangajiya a kan dakewarsu, ana ta kokarin ba da kariya, gashi ana ta Shahada, ina so na je na yi bankwana da su. Wani Haris (ana kiransa Tall Man) yace masa Malam in da rana ne za mu bari ka je, amma yanzu a yi hakuri don Allah yanzu a koma.


Ana wannan tattaunawar a tsaye, ana harbi ana dauko yan uwan da aka harba ana baya da su, sai Allah ya kawo Malam Kasim. Ya cewa Malam Turi, Allah Ya gafarta Malam, su Malam sun ce ace ku komo. 


Malam Turi yace masa, wane Malam din? Na Sokoto? Sai Malam Kasimu yace, A'a Malam (H) dai gafarta Malam. 


Malam Turi yace masa kun yi magana da Malam da yaushe? 


Malam Kasimu yace masa mun yi magana a waya, sun ce sun san kuna son Shahada ne, amma a dawo dai tukunna.


Malam Turi ya juya, dake da duhu ba ganin fuskar mutum ake ba, amma ga alama damuwa na lullube da shi sosai. Yana cewa, ko da rana din ne za ku ce da da duhu ne. Da kuma ba ku fadawa su Malam komai ba. Sannan Ya bi umurni ya koma.


Haka aka kwana ana harbi, yan uwa sun dake, ana ta kashewa a dauko mutum a kawo shi gida, a yayin da Malam Auwal K/Mashi ke ba da Slogan din "Ya Mahdi" yan uwa na amsawa. Ya zama Sojojin nan har zuwa Asubah, in suka dan tsagaita bude wuta to na Mintoci biyar zuwa goma ne.


Ga matsanancin sanyi, amma maza da mata, yan uwa sun dake sun ki bari sojojin nan su shigo Layin gidan su Malam. Wanda sun so ne tun farkon zuwansu su wuto gidan kai tsaye su yi abin da suke so nan take a gama.


Har zuwa bayan Asubah, gari ya dan fara wayewa, kai kace idan gari ya yi haske, mutanen nan za su ji tsoron kallon duniya, su janye daga wannan kisan kiyashin. Amma ina, sun rantse.


Sai na ya zama sun karo karfi ne a Gyallesu da Asubah din nan, suka zo suka rika ruwan wuta ta ko ina. Kisan ba ji ba gani kawai Malam.


Yanzu gari ya waye, ido na ganin ido, da masu bindiga, RPG, Igwa da Bomb, da kuma masu Kabbara da kare kai da duwatsu. Sojojin nan suka hau kisan ba ji ba gani ta kowane lungu, suna kashewa tun ana iya dauko wasu gawargakin da aka harba, har sai da ta kai ma ga ana kashe kowa ne suna kara matsowa cikin Layin, gawargwakin yan uwa jere a gefen Titin Layin Banaden zuwa gidan Malam, ba damar dauka.


An ce da Asubah an yi jam'in Sallah a gidan Malam kamar yadda aka saba, har ma kuma bayan da aka yi Sallah din su Malam suka yi magana da Malam Turi sannan suka shiga gida. 


Me suka ce? Allah Masani.


Wani dan uwa yace min ya ji su Malam Turi bayan hakan suna cewa, "Rayukanmu fansa ne ga rayuwar su Malam. Mutanen nan kisa kawai suke nufi a kan Malam, kuma ba za mu bari su kashe shi muna raye ba InshaAllah."


A daidai sadda ake harin Gyallesu, dama Husainiyya na kewaye da sojoji, muna iya jiyo karar harba Gurneti da Sojoji ke yi a Husainiyya alhali mu muna Gyallesu, musamman wajajen Asubah. 


Wanda na san in abin a ba da dama ga wadanda suka tsinci kansu a Husainiyya din ne, za mu ji labarai daban-daban na yadda abubuwa suka faru.


Kuma da Asubah din ranar Lahadi din nan, sojojin suka nufi Darur Rahma, inda nan ma suka samu wasu yan uwa a wajen suka bude musu wuta, suka kashe su.


Zuwa karfe 9 na safe Sojoji sun gama cimma yan uwa, sun kashe yan uwan da ke gida, wasu sun zagayo ta baya ma sun kewaye gidan, har zuwa kamar 11 na safe, inda suka cinna ma gidan wuta, suka fara baje bangaren gidan ta baya da tanka.


Tsinannun Sojoji suka saka Fetur a kan gawarwakin yan uwanmu, da jikkunan masu rauni da basu iya tashi, da aka cika gidan Harisawa da gidan Malam da su, suka banka musu wuta. Suna rushe gida, suna karisa duk wanda suka gani a kwance. 


Hatta gawarwakin yan uwa da ke jere a kan layukan haka suka rika bi suna kara harbinsu da kisan ta'addanci.


Misalin 12 na ranar Asabar, Suka saka Speaker suna ihu, suna cewa Al Zakzaky ka fito, duk wanda ke cikin gidan nan ya fito in ba haka ba za mu bombing din gidan baki daya. Za mu rusa shi a kanku. 


A yayin da wasu suke cewa "Ba Shia ba Kayanta. An gama da Al Zakzaky. A je Iran a yi Shi'a." Izgili kala-kala.


Tsawon yinin nan sojoji na kewaye da gidan Malam, suna farautan yan uwa a gidajen makwafta, sun kama wasu suka tafi da su. Amma Allah bai basu damar shiga cikin gida har su kai ga inda Jagora suke ba sai a ranar Litinin 3 ga Rabiul Auwal 1437H.


Labarin yadda su Malam (H) suka kasance a cikin gida tare da iyalinsa da wasu yan uwa yana nan a cikin hirar da ALMIZAN ta yi da Sayyida Suhaila. Har ma an Wallafa shi a littafin Kisan Kiyashin Zariya; Daga Ganau ba Jiyau ba. Da kuma littafin Yunkurin Kashe Shaikh Zakzaky a shekaru 10, na Cibiyar Wallafa jawaban Malam (H).


Haka ma Labaran Waki'a din baki daya, daga bakunan yan uwa daban-daban da suka ga abin, duk Almizan ta wallafa littafin Hirar nasu. Yana da kyau ya zama an nema an adana.


A takaice, labarin isar Sojoji ga inda su Malam (H) suke, abu ne mai ta da hankali na gaske. Nan ne muhallin girman bala'i.


Ko da suka buga suka bude kofar da karfi, suka ga su Malam (H) a ciki tare da mutum kamar 10, ciki har da wani karamin yaro mai suna Ibrahim wanda already an harbe shi a kafa, na ganshi bayan waki'ar nan Allah Ya raya shi, abin tausayi. 


Sai kawai wani Tsinannen Allah (T) ya ja baya, ya seta su da Bindiga mai jigida, ya fara harbinsu farrrr, ba kakkautawa. Ya turnuke su Abbah da ruwan harsasai, kawai jini suke gani na zuba a jikinsu. 


Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. 


Da aka tsagaita da harbin, Nan yan dakin suka lura da an harbi Malama a ciki sosai a kokarinta na baiwa Malam (H) kariya.


Nan Suka lura an harbi Abbah (H), a idonsa na hagu, har kwayan idon ya fice ya koma gefen kunnensa na hagun. Abbah ya dauko kwayan idanun ya maida shi cikin kurmin idon ya manna. 


Hannunsa duk jini, ya shasshafa gemunsa da jinin yana mai shirin ko zai koma zuwa ga Allah a wannan lokacin. Har a sannan Khalil (H) bai bar addu'a ba.


Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. 


A nan ne suka lura da an ragargaza hannun hagun Abbah (H), tun daga guiwar hannun zuwa tafin hannu da harbi sosai. 


Ya zama baya ko iya motsawa da wannan hannun, a sannan har share jini da hannun dama kawai yake iyawa. 


Haka ma kafarsa na dama, sun harbi Khalil (H) a cinyarsa sun huda.


A nan suka lura da an riga an kashe Hammad Da Humaid, daya an fille masa wuya da harsashi, daya an fasa masa kai a goshinsa duk sun yi Shahada. 


Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un


Hankalin Sayyid Haidaar ya tashi sosai, ya mike yana rokon su Malam su masa izini ya fita ya tunkari sojojin nan. 


Fitan Ali ke da wuya suka harbe shi a ka, suka daga shi suka wurga shi. An gefe.


Kamar yadda Sayyida Suhaila ta ba da labari, bayan duk wannan ne aka yi wayoyin da Sayyid (H) ya ba da Wasiyyoyi ga su Malam Kasimu da Sayyid Muhammad. Wanda suma wasu daga Wasiyoyin, Sayyida Suhaila da Malam Kasimu sun ambata su a hirarrakinsu.


Ciki akwai Wasiyyoyin Malam a kan dakewa a kan tafarki. Da kuma inda za a Bizne wasu yan uwa da sauran yan uwa da aka karkashe, yace a Darur Rahma, da Shaikh Turi da yace a mai da shi Kano, yace sauran Wasiyoyin za a ji a wajen Sayyid Muhammad, ya riga sanar da shi.


Ana haka jini na zuba a jikin su Malam (H), Sojoji na kewaye da su sun saita su da Bindiga da RPG, har zuwa sadda ya zama Malam ya gama galabaita. 


Sojojin suka fara jan yan uwan da suka yi saura suna fita da su, suka ja Su Malama Zainab, da Sajida da Sayyida Suhaila suka fitar da su. 


A nan wani Tsinannen Allah ya fincike Hijabin Malama Zeenah suka ja ta suka fita da Ummah.


Sun cire mata Hijabi irin yadda kakanninsu suka wa su Sayyida Zainabul Kubra a Karbala. Soji biyu suka rike kafofin Abbah (H) guda biyu, suka rika jan jikinsu mai albarka a kasa suna izgili. 


Suka samo baro suka jefa shi a ciki, suka kunna waka suna ji suna bi suna izgiliwa addini da tsarkakan bayi.


Wasunsu na daukan hotuna, a tunaninsu yada hotunan izgili ne ga Malam. Basu san dauka ne a gare shi ba, duk wanda ya gani zai ce bawan Allah nan an masa irin abin da aka wa kakansa Manzon Allah (S) a Da'ifa da Uhudu. 


Amma Sojoji suna ihu suna cewa sun gama da Shi'a, sun gama da Zakzaky.


Jagoranmu bai gushe ba a wannan halin yana addu'ar Sayyida Zahra da ke ba Allah zabin alkairi tsakanin rayuwa da mutuwa. "In da ba mu san cewa an yanke kan Husaini ba...


"Da abin da akai wa Malam Zakzaky sam ba za fa mu gane ba."


A haka suka kawo mota suka wurga Abbah, suna ta izgili gare shi da Tafarkin tsarkakan bayi. 


Tsinannun Allah suka cire zobensa, suka sace shi da duk abin da ke aljihunsa, har 'Belt' din jikinsa Sai da wani tsinanne ya zare shi. Suna ce masa sun kawo karshen Shi'a. Malam ya fada a ransa Saboda ko ya fada da karfi ba za su ji ba a yadda ya raunana, yace *"Da kashe wani zai kawo karshen Shi'a da kashe Imam Husaini (AS) ya kawo karshen Shi'a tuntuni."* kamar yadda shekaru uku da rabi da suka gabata na taba kawo labarin a wani rubutu.


Kamar yadda Sayyid Badamasi ya shaida min a wata hira (Interview) da na yi da shi kwanakin baya, yace bayan da suka dauko su Malam (H) daga Gyallesu, sun kai su Depot din soji ne na Zariya.


Daga nan, suka dauke su zuwa Kaduna da yammacin ranar. Suka kai su Asibitin 44, a nan su Malam (H) suka kwana, cikin daren akai musu aiki, da kuma daurin karaya (POP) da sauransu.


Daga nan 44, washe gari da Talata ba ko hutawa suka sake dauke su zuwa Abuja, aka kai su Asibitin Soji. 


Wanda wani ikon Allah da aka je asibitin Abuja din kuma, aka kuma duba su Malam, suka ce Sam-Sam ba karaya a jikinsu.


Haka suka cigaba da zama a nan asibitin har zuwa ranar Asabar 19 ga January 2015, inda suka kuma daukarsu zuwa Lagos, domin yin aikin idonsa.


Malam Badamasi yace mana, a lokacin da aka kai Malam Asibitin ido a Lagos, kafin su yi aiki sun gwada suka ga Malam sam bai da jini. Suna ta mamaki ya aka yi mutum yake rayuwa ba jini haka?


Amma dai suka yi wasu dabaru suka yi aikin idon a haka, sannan daga baya suka karawa Malam (H) jini.


Bayan an yi aikin na ido a Lagos, alhali kafin a yi aikin Malam (H) na gani da idonsa daya tangaran, amma da aka yi aikin idon sai ganin ya dan dusashe masa, ya zama bai gani kamar da. Amma aka ce bayan wata kamar shida za a sake yin aikin idon. Wanda kuma tun bayan da aka yi aiki na biyun ne ya zama Malam bai gani sam.


Ko da yake daga baya bisa nufin Allah, ya dawowa da Malam (H) da ganinsa, duk da ba tangaran ba. Ba bisa son miyagun azzaluman nan ba. Alhamdulillahi.


A yi hakuri haka, Labaran wallahi ba daɗi. Kirji na ta bugawa.


Sanin hakikanin halin da su Malam suka shiga, sai Allah Ya fito mana da su InshaAllah za mu ji komai daga wajensu ko wajen su Ummah.


Allah Ya gaggauta kubutar Jagoranmu mana da shi.


ME YA BIYO BAYAN WAKI'AR ZARIYA


Duk mun sani. An samu Shahidai fiye da dubu. Iyalai sun rasa danginsu. Iyaye sun rasa ya'yansa. Mata sun rasa mazajensu. Yan uwa sun rasa aminansu. An kashe maza da mata da yara da manya. An kona wasu da ranau. An yi ramin bai daya, an bizne yan uwanmu a rami guda bisa zalunci. 


Jagoranmu ya wayi gari bai da ko rawani guda daya mallakinsa. Hatta Zobbansa sun kona. Bai da ko Tasbaha. Sun kona gidansa, wanda a ciki akwai abubuwan da ya tara su a tsawon shekarun rayuwarsa. Daga muhimman ciki akwai Alkur'anai rubutun hannu, wanda ya rubuta da wanda kakanninsa suka rubuta, ciki har da Alkur'anin da aka rubuta kowace ayar cikinsa tare da Alwalar musamman


Sun kashe ya'yansa a gaban sa, sun kona yayarsa, alhali tana kuka tana cewa bata son ta yi shahada har sai ta yi magana da dan uwanta. Sun banka mata wuta sun kona ta da ranta tare da sauran Muminai


Sun kama Jagoranmu a halin rashin lafiya shekara hudu kenan har yau suna kokarin ganin gawarsa ne.


Allah ka karbi rayukanmu su zama fansar kubutar wannan bawan naka daga wadannan tsinannun bayin naka. 


Allah ka tarwatsa su. Ka tozarta su baki daya. Manya da kanansu.  Allah ka jefa musu bala'i da masifa. Allah ka halaka su. Ya Allah don darajar hawayen Ummah Zahra (SA)


Mu yi hakuri da bitan abubuwan da suka biyo bayan waki'ar. Duk mun sansu.


Kawai mu tuna cewa babban abin da ke bin bayan Waki'a shine cewa har yanzu Jagoranmu na tsare a hannun azzaluman nan. Kuma ba suna nufin rayuwarsa bane. Suna nufin su kashe shi ne ta hanyar tsare shi da raunin jikinsa da suka hana damar magani.


Mu yi kokarin samun uzuri a wajen Allah ta hanyar yin duk abin da ke kanmu na kokarin ganin kubutar wannan Uba, Jagora gare mu.


Allah Ya girmama matsayin Shahidanmu. Ya bamu albarkacinsu. Ya tsinewa makasansu albarka.


Allah Ya tabbatar da mu baki daya a bayan Malam Zakzaky. Ya karbi uzurinmu a ranar da za mu riske Shi Madaukakin Sarki.


Wasallallahu ala Muhammadin wa alihid Dahireen.



Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky