YAU SHEIKH TURI YA CIKA SHEKARA 59

 

Yau Shaikh Muhammad Turi Ya Cika Shekaru 59


— Saifullahi M. Kabir


Yau 15 ga Safar, 1442 tayi daidai da irin ranar da aka haifi Shaikh Muhammad Mahmoud Turi a shekarar 1383Hijiriyya.


Shaikh Muhammad Turi, wanda tun yana yaro dan shekara 14 ya hadu da Shaikh Ibraheem Zakzaky, kuma ya sallama masa dari-bisa-dari, ya samu tsananin kauna da soyayya tsakaninsa da Jagoransa, har ta kai ma ga Jagoran ya furta cewa ya ji yana kaunarsa.


"Kuma raina ya zauna da Malam Turi tun bayan wata magana da ta gudana tsakaninmu muna kurkuku n Kaduna tare, kuma na ji kaunarsa ya shiga zuciyata. To na ji cewa ba wanda ya kamata lallai ya rike wannan al'amari face Malam Turi, saboda wasu dalilai wanda ba zan bayyana su a nan ba, ba ma zan gaya wa kowa ba." Inji Shaikh Zakzaky (H).


Malam Turi, gwarzo ne sadauki, a lokacin Abacha, bayan kama Shaikh Zakzaky, shi ya rika jagorantar yan uwa Muzaharori ba tare da razani ko tsoro ba, har zuwa sadda aka kama su suma. Haka ma ya sha fada cewa duk sadda ka ji labarin za a kai hari ko an kai gidan Jagora, to baka da bukatar kiran waya ka tambayi wani cewa ka je ko ka jira umurni? Wannan ya sa ya aikata hakan a aikace a lokacin Wakiar Gyallesu.


Shaikh Turi na Kano aka fara Waki'ar Gyallesu, har kusan 12nd, ya sa yan uwa a Kano da sauran garuruwa sun fito Muzaharar Allah wadai da harin, yana cikin sahun Muzaharar ya ji bai natsu ba in bai taho Gyallesu a daren nan ba. Don haka ya bar sahun Muzaharar, karfe 2:30 yana Gyallesu.


Ko da Shaikh Turi ya zo Gyallesu, bai tsaya kokarin sai ya ga Jagora, Shaikh Zakzaky ba, bai zauna ba ma, kai tsaye ya wuto wajen Banaden ne, inda nan Sojoji suka labe suke harbi ba kakkautawa, ya nufi wajen da nufin fafatawa kamar yadda yan uwa suke ta fama, amma da aka tare shi aka ce ya yi hakuri ya juya, sai yace ai kawai yana so ya je ya gaisa da yan uwa ne da suke ta kokari tun dazu har kuma ana samun Shahidai a cikinsu. Sai da Malam Qasim Umar ya kira Jagora ya shaida masa halin da ake ciki, Jagora yace a cewa Malam Turi ya bar wajen ya dawo, sannan ya bi.


An ce har bayan Sallar Asubah, Jagora ya wa Shaikh Turi magana, cewa ya ji an ce ya tunkari Sojoji, ya san yana son Shahada ne. Amma ita Shahada in lokacinta yayi za a yi ta ko ba a tare ta ba. Shaikh Turi yacewa Jagora 'Raina ya zama fansar rayuwarka'.


Fitowar Shaikh Turi a safiyar Lahadi ya rika nanata cewa 'Kar mu yi sake su kai ga Jagoranmu face bayan sun gama da mu. Mu daure, yau ranar cika alkawari ne.' A haka Shaikh Turi ya dake tun ana gaban Transformer yana tsaye yana karfafa yan uwa, har aka tarwatsa yan uwa ya zama yanzu ana kofar gidan Jagora ne kadai, bai gushe ba a kofar gidan Jagora har wani la'anannen Soja ya bude masa wuta ya fadi yana ambaton Allah.


Sadda yake tsaye ana harbi, idan wani ya zo yace Gafarta Malam ku dan shiga daga cikin rumfar nan mana ko a dan tsuguna. Ya kan ce wa za a tsugunawa? Ina zan je? Ni ba dan uwa bane? Dakakken Namiji Jarumi! A lokacin kuma idan ya ga wanda bai kai shi juriya ba ya kan tausaya masa ne ya bashi uzuri. Na ga mutum biyu da Shaikh yaga suna kuka saboda girman bala'in da suka gani, amma Shaikh Turi yana basu uzuri da cewa su daure su yi shiru kar su raunata zukatan wasunsu. Yace ma dayan, har yanzu akwai damar barin Unguwar nan, idan tsakaninka da Allah ka ga cewa iya abin da za ka iya kenan, ba tsanani, kana iya bi ta makabarta ka fita daga unguwar, Allah zai dubi zuciyarka ya baka lada daidai sa'ayinka, kuma kai ba abin zargi bane, amma dai yau ba ranar kuka bane, ranar cika alkawarin da muka dauka ne. A daure. Sai mai kuka ya ji nasihar ma'abocin Nasiha, ya share hawaye ya mai da kansa cikin masu juriya. 


Wani bawan Allah ne Shaikh Turi da ya gama sanin hadafi da asalin manufar Jagoransa, Shaikh Zakzaky (H), na tuna, Malama Maimuna mai dakinsa ta taba bani labarin cewa bayan fitowar su Malam (H) a lokacin Abacha ya fada musu cewa ya so Malam Turi su riga shi fitowa saboda akwai wasu abubuwa da suka tattauna a kurkukun, wanda shi Malam Turi zai aiwatar kafin fitowarsa. Amma dai abin da Allah Ya nufa shi ya kasance. Ku dubi yadda Jagora kan wakilta shi a wurare daban daban ba tare da fargabar gazawar wakilcin ba. 


Abin burgewa ga Shaikh Turi shine, siffantuwarsa da kyawawan dabi'u ta yadda kowa yabonsa yake da su, har makiyansa kuwa. Ko da yake a wajen Malam Turi bai ma yarda cewa yana da makiya ba, ya riga ya taka wani matsayi wanda a wajensa da mai yabo da mai suka duk abu guda ne, ya ma fi ba da hankali ga suka idan an yi don ganin idan ya yi kuskure ne ya gyara. Ma'abocin sa da zumuncin da ya mamaye dukkan manyan gidajen Malaman Kanawa da manyan garinsu cikin kasa da shekaru 15. 


Ma'abocin saukin kai da taushin hali, dattako da yafiya, kau da kai da mance sharri, yaba alkairi da girmama hatta na kasa da shi, kyauta da tausayi, kankan da kai da mutunci. Bisa zabin Allah, ya sanya soyayyar Shaikh a zukatan bayinsa, har aka wayi gari da Shaikh Turi Kanawa ke tsira, a kanshi suke Fitinuwa.


Addu'armu a irin wannan rana ita ce, Allah (T) Ya tsinewa duk masu hannu a sanadin fakuwar su Shaikh Turi da dukkan yan uwanmu daga gannanmu. Ya karbi Shahadar Shahidanmu ya bayyana Mafkudai, ya amintar da su cikin kariyarsa. Allah (T) Ya kara albarka a zuriyar Shaikh Turi, ya amintar da su, ya basu ikon gado halaye da dabi'unsa su wanzu a kansu har abada.


Happy Birthday Abbah🌹

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky