ABINCIN RUHI
ABINCIN RUHI DA GANGAR JIKI
“Na farko akwai wannan jiki wanda ya kan rika girma, wanda ya kan fito yana jariri, ya rika girma, har ya tsufa ya tankware ya zama ba yi da karfi ya yi rauni. Shi ne kuma akan haka rami a saka in ya mutu. Shi gangan jiki ke nan. To, a cikin shi gangan jikin nan yana dauke da wani abu wanda ya fi gangan jikin, shi ne; rai. Shi ne ruhi. Akwai jikin mutum akwai ruhi. To, ruhin nan, shi ne; ake tashi da shi sama. Shi kuma yana sifan jikin mutum ne, amma kuma shi shara-shara yake. Inda abin mutum ya saka hannunsa ne a cikin ruhin zai ga kutsawan (zai ga ya shiga). Amma ko in gangan jiki ne ya tura hannu sai ya ji ya yi karo da shi. Ba jiki ne wanda yake karfaffa ba mai daukan nauyi. Domin shi anyi shi ne da haske. Shi wannan ruhin shi ne yake rabuwa da jiki ya yin mutuwa, sai mutum ya zama. An cire rai din, sai a dauki gangan jikin a haka rami a saka. Amma rai fa? Ya mutu? shi yana nan, shi rai ba ya mutuwa.”
“shiyasa ya zama shi ruhin shahidi, shi aka ce mishi kar a ce masa ma ya mutu. Saboda shi Allah yana yi masa jiki ne daban, shigen irin jikinsa na nan duniya. Sai yasa wannan ruhin a jikin. Sai ya bi shi aljanna. Saboda haka shi zai rayu ne da gangan jiki. Gangan jiki wanda zai ci ya sha. Ya rayu sosai yana ci yana sha amma ba a nan ba. A aljanna. Shi a nan duniya matukar ranka da jikinka suna hade tare, ko wanne yana bukatar abu na ci. Jikin mutum shi yana rayuwa ne da abinci da ruwa (ya ci ya sha). Da shi yake rayuwa. Kuma yana da al’ada na ba ya son wahala, yana son hutu. Kuma akan rika kula da shi ta hanyar wanke shi da saka masa riga. Mu kan wanka mu kan wanki, shafa mai, sa turare, don jikin mu ya yi kyau. Idan aka bar jikin mutum ba a kula da shi ba, zai shiga wari.”
“tunda yake a cikin jikin akwai rai, rai din yana amfana daga wadansu abubuwa daga jiki. Shi rai al’adarsa da dabi’arsa shi kyau ne ko muni. Shi rai ke nan. Da za a samu ran mutumin kirki, sai a ganshi haske ke nan, kal-kal-kal, fes-fes-fes, kyakkyawa. Inda kuma za a ga ran mutumin da yake mugu, to, sai a ganshi kamar wani dodo ba kyan gani. Duk a cikin halittun da Allah ya yi, Allah ya yi mana halittu daban-daban, za a iya ganinsu, su zama aya. Misali kamar; jaba, Alade da Dorinan ruwa “munana ne.” Idan Allah ya mai da mutane a wadannan siffofin. Ka ga mutum zaka iya gane shi amma kuma ba shi da kyan gani.”
“haka shi rai, idan mutumin kirki ne, sai ya zama kyakkyawa, idan mugu ne sai ya zama mummuna. Aikin da yake yi shi yake shafar Rai din. Idan mutum bai kula da rai kuma fa? Kamar ba ya ba rai abinci. To, rai ma yana cin abinci? Eh! Amma ba tuwo yake ci ba. Shi kuma abincinsa shi ne tuna Allah. Karatun Al-kur’ani ne, Sallah ne, addu’a ne, duk wadannan su sune abinci da ruhi yake ci, sai ya da da kyau. Da kuma abin kirki yana zuwa gareshi, shiyasa ake sa azumi. Azumi yana takura ma jiki, sai yasa ruhi ya yi kyau.”
“Manzon Allah ya siffanta salloli biyar da kamar ruwa a kofar gidan mutum yana wanka sau biyar kullum. Za a sami dauda a jikinsa? To, haka nan mai sallah biyar zai zama baya da zunubi. Fes-fes kullum. Haka kuma an tambayeshi ya zaka gane mutanenka a ranar lahira? Sai ya ce; wuraren da suke alwala zasu rika haske. Inda abin in tambayeku ne, in ce; “Mutum jiki ne kawai ko ko akwai wani abu a cikin jikin? Me zaku ce?” “me ye a cikin jikin?” To, shi ruhin nan yana cin abinci? To, me yake ci? Tuwo, Kosai da su Alale, ya sha Kunu? To, tambaya ina ilimi yake zuwa? Ina karatu yake zuwa? Mutum idan ya manta karatunsa zai matsa hannunsa ne ya fito da shi? A ina yake? Yawwa a jikinsa ke nan a cikin ruhinsa ne. Hhar wala yau ruhi yana da abinci biyu, banda zikiri akwai ilimi. Shima ruhi ilimi na gyara shi ne.”
Comments
Post a Comment