ALKALAMI KAFI REZA KAIFI tare da M.IGamawa

ALKALAMI KA FI REZA KAIFI

M. I. GAMAWA 0703 557 7745

Malaman Wahabiyawa: ’Yan mowa a wajen gwamnati, ’yan bora a wajen Allah
Malaman Wahabiyawa sun fahinci damfare wa Gwamnati na da nasa natijar a Duniya, musamman Gwamnatin zalunci wacce ba ta da tausayi ko mutumta rayukan ’yan Adam. Da ma kisa a wajensu abu ne mai sauki, kamar kwance kulli.

Shi Wahabiyanci ba shi da tushe, in ma akwai shi da tushe, bai wuce Ibnu Taimiyya Baharrane da Abdulwahab wadanda dukkan su daga lardin Najadu suka bayyana. Shi Ibn Taimiyya waren Gwanki ne a cikin Maluma. Domin shi ne wanda ya rayu har ya mutu yana shekaru sittin da bakwai bai yi aure ba. In ka ga dama ka kira shi tuzurun Shehi na Harrana. In Salafanci da Wahabiyanci na da tushe, to ga tushen nan.

Kama-kama har wannan muguwar akida ta shigo mana, ko muna so ko ba ma so. Ga shi yanzu ta zama mana jarrabawa mai tsanani. Wani hali na masu wannan muguwar akida ita ce, mannewa masu mulki. Sun mai da masu mulki iyayengijin da suke rayuwa da karfin mulkinsu. A kan haka suke furta kalaman ridda don biya wa Mulaka'u bukata. Su kuma Mulaka'u suna ganin Wahabiyawa a matsayin abokan tafiyar da ba don su ba, da kwanakin mulkinsu ba su kai ko’ina ba. Daga nan aka yi auren zobe. Ganin wannan auren zoben da ba addaura a Coci ba, sai Wahabiyawa suka dauki Gwamnatoci a matsayin masu biya musu duk wata bukata, har da kawar musu da duk wanda ba ya da'awa irin tasu. 

Wannan samun wuri shi ne ya sa Wahabiyawa ziyarar bazata fadar Gwamnatin Kano don kai kukansu na neman a kashe musu Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara. In ba za a kasha shi ba, to a hana shi Wa'azi, kuma a rufe masallacinsa. Haka kuma Ganduje Gwamnan Jihar Kano ya yi. Ya zartar da hukuncin da ko Fir'aunan Misira bai zartar da irin sa ba. 

Bayan halakar da Fir'aunan Musa, wasu sun zaci tasa ta kare, wato Fir'aunanci ya tafi da Fir'auna, amma ina! Duk da cewa ba a samu wanda ya ce shi ne Ubangiji madaukaki ta fuskar da Fir'auna ya fada ba, amma bakaken azzaluman da suka fi shi zalunci sun wanzu har zuwa yau, bilhasalima an samu wadanda suka fi shi zalunci a wannan lokaci. An samu wadanda suka kashe rayukan da Fir'auna bai kashe ba. Haka kuma an samu wadanda suke hukuncin da Fir'auna bai yi irinsa ba. Misali a lokacin da ya gaji da wa'azozin Annabi Musa, sai ya tara masa masu sihiri don su kure shi. Sun fada, shi ma Annabi Musa (rayuwar iyayena da nawa su zama fansa gare shi) ya fada. Duk da Fir'auna ya yi wa wadanda suka yi imani da Annabi Musa alkawarin azaba, akalla ya zaunar da su domin kowannen su ya baje kolinsa. Wannan Fir'aunan Misira ke nan. 

Satin da ya gabata ya zo da bakon abu, amma bai bai wa masu hankali mamaki ba. Da ma duk wanda ke jin wa'azin Shaikh ABDULJABBAR, in akwai addu'ar da zai yi masa ita ce nema masa tsari daga Wahabiyawa da iyayengidajensu Mulaka'u. Yalai kuwa daga jin yadda wadannan kaskantattu suka fara datse wa'azozinsa, suna kullawa, za a fahimci cewa an zo wurin. Kafin a ankara taurari biyu masu bindi, wadanda ganin su ba alheri ba suka ziyarci Gwamnan Kano Ganduje. Wadannan muggan baki sune Bala Lau da Kabiru Gombe. Tabbas sun fada wa Gwamna abin da ba haka yake ba game da Shaikh Abduljabbar. Shi kuma Ganduje, ganin yadda yake, ga shi ga kamar sa, sai ya dauki mataki, matakin da ko Fir'auna bai dauki irin sa a kan Annabi Musa ba. 

Da a ce akwai hankali, ko da irin na Masinjan Gwamna a jikinsa, da ya nemi jin ta bakin Shaikh Abduljabbar tun farko, amma ina! Sai ga Gwamna na huci kamar ’yan Kwangila sun hana shi Dola, yana fadin abin da ko a gidan giya ba za a jingina wa Shaikh Abduljabbar ba. Cikin abin da Gwamna ya fada wai Shaikh Abduljabbar na batanci ga Sahabbai da Fiyayyen Halitta. Har ya yi shagube ga Harka Islamiyya karkashin Sayyid Zakzaky. Hatta riga mai aiki ta zama abin ambato a gun Bawahabiyen Gwamna.

Bari mu bi kadan daga maganganun Ganduje mu ga shin da gaske yana kishin Annabin Rahama? Ba Ganduje ne ya biya diyyar wata kafira da ta zagi Manzo a shekarun baya bayan wasu dakaru sun hukunta ta ba? Diyya ba ta isa ba, sai da ya yi alkawarin biya wa 'ya'yanta kudin makaranta daga Firamire zuwa Jami'a da kudin jama'ar Kano. Wannan shi ne sakamakon da aka yi wa Kafirar da ta zagi Manzon tsira a wurin 'Kadimul Islam'. To, me ya sa hukuncin 'zagin' da Abduljabbar ya yi, in ma ya yi ya bambanta da na Arniya ’yar kabilar Ibo? Gwamna ya ce dama ana neman sheda ne a Kotu, amma me ya hana a tambayi wanda aka ba da sheda a kansa ko abin da aka fada a kansa haka ne ko a'a? Shin da an ba da sheda a kan mutum ya isa a hukunta shi, ba tare da an ji daga bangarensa ba? In haka ne me ya sa Ganduje ya kai yanzu bayan bayyanar sa a bidiyo yana karbar Daloli da sunan cin hanci?

Gwamna na gama wannan danyen hukunci, sai ya tura ’yan sanda suka rufe Masallacin Shaikh Abduljabbar. Ya ce wannan somin tabi ne. Ina wannan abin kunya zai kai Ganduje? Kodayake ai ya gama kunya tun sa'ad da aka nuna shi yana zura Dalolin cin hanci a aljihun rigarsa, in dai kunyar duniya ce. In zura Dola a aljihu ita ce kunyar farko, tabbas maganar Shaikh Abduljabbar ita ce ta biyu. Wani abin takaici, wai wannan Gwamna shi ne Kadimul Islam in ji Wahabiyawa masu addinin Kudi. Ina Gwamnan Zamfara da wadannan jikokin Bil'amu dan Ba'ura suka bai wa lakabin "Amirul Muminun" sun gama da shi, yau ko sunansa ba a ji a bakunansu. 

Haka shi ma wannan Kadimin ko Kha'inul Islam zamaninsa zai wuce, su manta da shi. 
Wani abin dariya a lokacin da Gwamna ke gaban wadannan asararrun mutane shi ne yadda ya ba su umarnin irin hudubar da za su yi a Juma'ar da ta tunkaro su. Ga dukkan alamu sun aiwatar da umurnin abin bautarsu. Hatta a Abuja an samu gayyar sodi daga cikin Limamai sun aiwatar da umurnin Gwamna mai Daloli. Yanzu mulkin Gwamna ya wuce gidan Gwamnati da kan tituna har ya isa mumbarin Masallatai. Su kuma suka ce sun ji, sun amince. 

Da wannan maganar Gwamna ta yadu a duniya, sai masu hankali da basira suka yi masa caa a kan wannan wauta da hukuncin Fir'aunanci da ya yi wa Shaikh Abduljabbar. Ganin haka, sai ya yi kwana, ya ce ya yarda a yi mukabala.

Da jin za a kira mukabala, sai cikin muggan "Maluma" ya duri ruwa. Na ga Shak Dosta Sani Rijiyar Lemo yana ba da hijjojin da ko mai karamin hankali ba zai karbe su ba. Na ga yana cewa, wai ba zai bata lokaci wajen share wa Shaikh Abduljabbar najasa ba. In kuwa zai yi haka, yaushe zai ba da karatu? Wannan magana ta fi ta Wawan Sarki ban dariya. Shin shekarun da ya bata yana zagin Shi’a da Darikun Sufaye, ya hana shi ba da karatu? Ya ce, kuma zai hada shi da dalibai yara su yi masa wankin babban bargo, su kuma manya su dauraye. In an yi haka wane ne babba, wane ne Yaro? A ko’ina babba shi ke yin wanki, musamman na Borgo. In dai Borgon ne, hatta daurayar ma Manya ke yi. Abin fahimta a nan Rijiyar Lemo ya tsorata, a ba shi Kunun Madaci, ya kuskure da na gyambo! Wani daga cikin su mai lakabin Zakin Sunna, yanzu ya zama Kiyashin Sunna, ya san ba zai tari Giwa ba. Sai ya ce Bin Usman ne zai fuskanci Shaikh Abduljabbar. Haka dai suka rika janyewa, daya bayan daya, ba kunya balle tsoron Allah Mahalicci.

Sai dai Gwamna ya tabbatar da cewa, za a yi mukabala a kofar fadar Sarkin Kano daga baya. Gwamna ya ce da ma Shaikh Abduljabbar ne ya ki, amma yanzu ya yarda za a kara. Wadannan maganganu da ke fita daga bakin Gwamna, sun nuna cewa Gwamna ya fi maida hankalinsa a kan Dalar Amurka fiye da wadanda yake mulka. Tabbas da hankalinsa na kan abin da ke faruwa da talakawansa, da ya san cewa Shaikh Abduljabbar ya yi wa masu sukar sa tayin Mukabala fiye da yawan shurin Masaki. Amma ina! Ba nan Gwamna ya sa gaba ba. Ko dai kaka, Gwamna ya yarda a yi Mukabala. Sai dai kafin mukabalar, dole a dode kofofin Kano, don kar wadannan masu amsa sunan Malamai su ranta a na kare kafin ranar ta zo. Haka kuma dole Gwamna ya umurci Malaman da suka kai karar su je filin Mukabalar da kansu, don kuwa tsuntsun da ya kira ruwa, shi ruwa kan doka. Shin da a ce Gwamna zai raba kujerin Makka, za su aika wakilai? Shin da Gwamna zai ba da koriyar Ambulan, da za su aika wakilai? Tabbas a'a! Da da kansu za su je. Wasu ma sai sun manta hulunansu. Ban ce rawani ba don ba sa sawa. 

Addu'a muke Allah ya kawo ranar, mu ga yadda gwanin rawa zai fadi. Su tuna cewa a ran nan babu Alaramma, da kansu za su jawo aya kuma su fassara. Wani abin da suka jahilta shi ne Banu Umayya ba su taba kure Banu Hashim a Mukabala ba. Abin da aka san Umayyawa da shi shi ne dauri da kisa. Wadannan muggan ayyuka su suka nemi a yi wa Shaikh Abduljabbar tun farko, ba Mukabala ba. Yanzu babu dauri balle kisa, sai dai a je kofar fada a baje koli in an isa. Su fahinci lokacin Kisa don mutum ya bayyana fahimtarsa ya fara zama wauta da rashin hankali. Wadanda suka kasha, suka kona a Zariya, Mahaukata ake kiran su. Su ma a yanzu sun yarda mai yawo tsirara ya fi su hankali, don haka mahukunta suna gudun maimaita kisan kare dangi irin na Zariya. Maimakon haka sai suka ce Wahabiyawa su taho da bindigar ilmi, a ga wanda bindigar ilimi za ta ragar wa, sa'annan a ga wanda za ta kashe. Yau ALKALAMI ya zama makidin a hada, amma ba makidin a raba ba!

Comments

Popular posts from this blog

TARIHIN SHEIKH ABUL FATHI MAIDUGURI

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA