HARISAWA SUNYI BIKIN DIYAR ANNABI (S.A.W.W) A KATSINA
*HARISAWA SUNYI BUKIN MAULUDIN DIYAR ANNABI (S) A KATSINA.*
Bin Yaqoub Katsina.
Hurras na harkar Musulunci karkashin jagorancin Shaikh Zakzaky (H) yankin Azzahra (A.S) Zone Katsina da kewaye, sun gudanar da gagarumin Mauludin Sayyida Zahra (A.S) Wanda suka saba gabatarwa duk shekara.
Taron dai an fara shi ne da safiyar yau Lahadi 21/2/2021 a filin samji cikin garin Katsina. Bayan bude taro da addu'a da karatun Alkur’ani gami da wake daga mawakan Harisawa, sai aka gudanar da addu’a ta musamman kan jagora Shaikh Zakzaky (H) tare da rokon Allah Ya gaggauta kwato shi daga hannun azzalumai.
Wannan Mauludi dai an kayata shi ne da nau’oin bukukuwa kala-kala wanda aka soma tun ranar Asabar inda aka fara da wasan kwallon kafa, sannan gasar wake sai makala (Paper Presentation) wanda kwamitin Ilimi Na Harisawa ya jagoranta. Zuwa ranar lahadi nan kuma aka kammala da faretin ban girma ga Sayyida Zahra (A.S).
A wannan Gasar dai da aka buga an samu Unit 6 sun halarta a karkashin zone din da ya hada da Katsina, Malumfashi, Kankiya, Funtuwa, Daura sai kuma Maradi. A karshe dai Katsina Unit ne suka yi zarra a mafi yawan gasar da aka gudanar, inda funtuwa tazo na 2 sai kuma Daura suka zo na 3.
Da yake jawabin a taron M. Yakub Idris ya bayyana cewa; Harisawa na da bangarori kala-kala kuma ayyukansu na taimakon al’umma ne ciki hada aikin gayya gyaran makabartu da sauransu. Haka nan ya ce wannan taro ba a Katsina kadai ake yin irinsa ba, a’a duk inda Harisawa suke a Fadin Kasar suna yi idan ranar Haihuwar daya daga Imamin da suke amsa sunansa a zone dinsu ta zo.
Daga karshe Shaikh Yakubu Yahya Katsina ne yayi jawabin rufewa kuma shi ne ya karbi faretin, haka kuma babban bako a muhallin. Shima a jawabinsa ya jinjinawa Harisawan da irin kokarinsu a wannan Harka, kuma ya ce wadannan Harisawa da su ne gwamnati ke tsoronmu suna ganin muma kamar mun zama gwamnati ne ko muna son kawo tashin hankali a kasa ne, ‘Kai da ace mu ’yan tashin hankali ne, ko kuma mu ’yan ta’adda ne kana jin za a kai yanzu bamu rama abinda gwamnati tayi mana kan jagorammu ba?; Inji Shaikh Yakubu.
Daga karshe kuma ya bankade asirin Malaman maja da suka sako Shaikh Abduljabar gaba, da nufin wai suna tuhumarsa da batanci ga Annabi, inda suka kira yin Mukabala, sai dai Shaikh din ya tona asiri da cewa ashe saudiyya ce ta gargadi Malaman gami da ganduje ka a soke wannan mukabala domin ba a mukabala da dan shi’a bai yi nasara ba, Shaikh Yakubu ya fada.
Anyi taron lafiya an tashi lafiya bayan mika kyautuka ga dukkan wadanda suka yi zarra a gasannin da aka gabatar, sannan akayi addu’a kuma aka Sa sahun Mazaharar #FreeZakzaky daga filin Samjin zuwa tsohuwar stadium da ke round din ladan wapa. Daga nan aka sallami kowwa ya kama hanyar komawa gida.
#HurrasMauludZahraKatsina1442
@MediaForumKatsina.
Comments
Post a Comment