Hunturun Bana: Kimanin Yara 887 Ne 'Yan Uwa Musulmi Suka Yi Wa Shayi Kyauta A Katsina.
A ranar Lahadi nan ta gabata 2 ga Rajab,1442H (14 ga Febrairun 2021) 'Yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Yaqoub Alzakzaky(H) na Da'irar Katsina, suka kawo karshen yi wa Yara shayi/Kaciya na hunturun wannan shekarar ta 1442H/2021M, bayan shafe kimamanin Sati takwas suna gudanar da ita kyauta ( in ban da Kudi kadan da suke kar6a daga hannun Iyayen Yaran don ssayen Bandeji da sauran kayan aiki) a da'irar ta Katsina.
Aikin yi wa Yaran shayin wanda ɓangaren lafiya na harkar Musulunci (ISMA) kan jagoranta duk shekara a irin wannan lokaci na hunturu, bana ma an gudanar da shi kamar yadda aka saba inda ya gudana a Markazin 'yan uwa Musulmi na katsina, inda a bana aka samu nasarar yi wa Yara kimanin 887 Shayin, adadin da ya zarce na bara da bara waccan da kimanin kaso 30 cikin dari (30%). An kuma kammala yi wa yaran Shayi lafiya, cikin nasara, ba tare da wata tangarda ba.
Tun farko da yake jawabin kaddamarwa gabanin fara yi wa yaran Shayi a ranar farko, wakilin 'yan'uwa Musulmin na katsina, Shaikh Yakubu Yahaya ya fara da yin wasu addu'o'i ne wadanda a kan so Iyaye su yi wa Yaronsu a lokacin da za a yi masa Shayi, daga bisani kuma kuma ya yi addu'ar samun nasarar farawa da kammala wannan aiki na Shayin.
A cikin takaitaccen jawabin da ya gabatar, bayan addu'o'in, Shehin Malamin, ya bayyana matsayi da kuma muhimmancin yin Shayi ga Namiji a tarihin addinin Musulunci, inda yace; "Yin kaciya na daga cikin sharuddan amsar Ibadar mutum Namiji, da kuma aikin Hajji."
Ya kara da cewa; "Kasashen da al'ummar da ba su yin kaciya, za ka gan su, nan da nan sai su kamu da cututtuka tare da kuma yada su."
Tun daga farkon fara yin Shayi zuwa lokacin kammalawa, al'ummar da suka kawo yaransu Shayin daga Makwafta da kuma na cikin gari, sun ta yin sam-barka da wannan aikin alkhairi da 'yan uwa Musulmin kan yi duk shekara wa Yaransu, tare da kuma yi masu addu'ar alkhairi da samun lada daga wajen Mahalicci.
Comments
Post a Comment