LOKACI MUHIMMIN ABU NE GA RAYUWAR DAN ADAM

LOKACI MUHIMMIN ABU NE A RAYUWAR DAN ADAM

Inji Shaikh Adamu Tsoho Ahmad
A yayin da yake tsokaci dangane da cikarsa shekaru 59, a jiya Lahadi a wajen Mauludin Amirulmuminin (AS) a garin Jos, Shaikh Adamu Tsoho Ahmad ya bayyana cewa: “A lokacin da ake murnar tunawa da ranar haihuwa, bayin Allah kuma kan tuna da cewa ajalinsu na kara kusantowa ne.” 

Yace “Kamar yadda Imam Khumaini ya kawo cewa, da zaran mutum ya kai shekaru 37 ake kammala siffar halittarsa, da ya cika 40 shikenan ya kammala cika mutum, hankalinsa ya kammalu, daga nan zai rika baya ne a komai, ciki har da ji da ganinsa, da kuma karfin jiki.”

Shaikh Adamu yace, rayuwar mutum na da iyaka, kuma iyakan nan ne lokaci, lokaci yana da muhimmanci, shi yasa ma Allah (T) ya rantse da lokaci a Alkur’ani mai girma.

Ya cigaba da cewa: “Lokaci ya kasu uku; dazu, wanda ya wuce, imma ya zama hujja a gareka ko a kanka. Sannan akwai yanzu, wanda shine naka, ana mafani da shi wajen shiryawa dazunka. Sannan akwai anjima, wanda shi wannan na Allah (T) ne, in ya so ya barka ka kai, ko ya dauke ka kafin lokacin.”

Don haka yace, Mai hankali shine wanda ke amfani da yau dinsa wajen gyara jiyansa da shiryawa gobensa. Domin kuwa babu wata riba da mutum zai samu a rayuwarsa kamar ya shagaltu da bautar Allah Ta’ala a cikinta baki daya. 

Shaikh Tsoho yace: “An bamu lokaci tsakanin rayuwarmu da mutuwarmu ne don a jarabce mu, a ga wane ne a cikinmu zai kyautata aiki ya yi amfani da wannan dama da aka bashi. In mun munana aiki to baa bin da zai riske mu face asara da tabewa.”

A karshen jawabin nasa, ya bayyana ni’imar samuwarmu a karkashin Maulana Sayyid Ibraheem Zakzaky a matsayin babban ni’ima. Yace: “idan muka yi wasa da wannan ni’imar da aka mana, kamar mun ci amanar Sahibul Asr ne, hakan kuma cin Amanar Manzon Allah (S) ne, cin amanar Allah Ta’ala ne.”

Don haka sai ya jaddadawa yan uwa cewa: “Imani da Iklasi da jajircewa ne kawai za su sa mutum ya iya tabbata a tafarkin shiriya har karshen rayuwarsa.” Sannan ya yi addu’ar Allah ya tabbatar da mu a tafarkin tsarkakan bayi (AS) a karkashin Jagoranmu Shaikh Zakzaky (H).

— Saifullahi M Kabir 

Tun da farko kafin isowar Shaikh Adamu Tsoho muhallin taron Mauludin wanda ‘yan Media na yankin Jos suka shirya, sai da Dr. Ibrahim Sulaiman Rinji da Saifullahi M. Kabir suka gabatar da jawabai a kan maudu’ai daban-daban.

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky