MAFIFICIN SUNAN DA ZAKA SAWA DANKA
MAFIFICIN SUNAN DA ZA KASA WA 'ƊANKA !
—Sheikh Adamu Ahmad Tsoho Jos
Daga Imam Ridha(as) yana cewa; "Duk gidan da akwai sunan Muhammad to ma'abota gidan zasu wayi gari cikin alkhairi kuma suyi marece cikin alkhairi. Imam Bakir(as):-"Yake cewa shi Shaidan idan yaji mai kira yana kira 'Ya Muhammad (S) ko ya Ali (As) to, Shaidan sai ya narke kamar yadda dalma take narkewa saboda girma da firgicin wadannan sunaye din, har sai in ya ji mai kira yayi kira da sunan makiyi(Ahlul Baiti), sai kaga yana fankama da takama yana jin dadi.
Hanyoyi da za'a bata wa Shaidan rai shine sawa sunan 'Dan ka ko 'Ya'yan ka sunan Manzon Allah (S) ko zuriyar Manzon Allah (S).
A wani Hadisi daga Abul Hassan ya ce:-" Talauci baya shiga gidan da yake akwai sunan Muhammad ko Ahmad Ko Ali ko Hassan ko Hussain ko Ja'afar ko Dalib ko Abdullahi ko Fadima.
Duk gidan da yake akwai irin wannan sunan to talauci baya shiga wannan gidan. Wannan kwadaitarwa ne akan mu sanya sunan Manzon Allah da sunan iyalinsa Ahlulbait ga ya'yan mu.
Imam Ja'afar Sadik yana cewa;" Ba za'a Haifa mana abin haifuwa ba, face mun sa masa sunan Muhammad, idan kwana bakwai ya wuce in mun so mu canza sunan daga Muhammad mu sa wani , in ko ba haka ba sai mu bar sunan Muhammad. Haka yana nuna mutum yana da dama ya sanya suna wa dansa bayan kwana bakwai sai ka iya canza wa.
Sannan ana son girmama duk wani mai suna Muhammad, in ka sa sunan 'Danka Muhammad to banda zagi banda duka banda hantara ana son ka girmamashi yaci albarkacin asalin mai sunan.
ADDU'AN DA ZAKA YIWA 'DAN'UWANKA IDAN AN MAI HAIHUWA.
Ana so ya zamo an mai addu'a da cewa; Godiya ga wanda ya baka abin haihuwa kuma Allah albarkace ka cikin wannan 'da naka da aka baka Allah ya rayar dashi ya kai matukan Girman shi, kuma Allah ya azurtaka biyayyansa wato ya zamo 'da mai biyayya.
Za'a iya cewa Allah muna maka godiya da kayi wannan kyauta ga wannan bawa naka, ka sanya wannan 'dan' ya zamo mai biyayya ga iyayen sa, kuma ka raya shi tsawon rayuwa cikin lafiya da imani.
Comments
Post a Comment