MAULUDIN IMAM ALI A MARKAZIN 'YAN'UWA NA KATSINA @2021
MAULUDIN IMAM ALI (A.S) YA CI GABA A MARKAZ KATSINA.
Daga Bin Yaqub Katsina
Yanzu haka Shaikh Yakubu Yahya Katsina na ci gaba da jawabin Mauludin Imam Ali (A.S) da yammacin nan na ranar Alhamis 13,rajab1442 dai dai da 25/2/2021.
Bayan mawaka sun gama wakokin yabon Imam Ali (A.S) sai Shaikh Yakubu Yahya Katsina ya ci gaba da jawabinsa.
Da farko dai Shaikh ya gode ma Allah bisa wannan babbar ni’ima da Allah yayi ma al’umma da duniya baki daya. Har wa yau Shaikh din ya dora karatunsa na yau ne a kan Kore shubuhar da aka rudi al’ummar Musulmi da ita na cewa; Baban Imam Amirul Mumineen (Ali) ba musulmi ya rasu ba, wato Sayyid Abu dalib.
Shaikh ya ci gaba da karyata wannan shaci fadin zance inda yake cewa “Manzon Allah (S) shi ne ya sallaci Abu dalib kuma shi ne mutumin farko da ya fara shaidawa da Annabtar Annabi tun Annabi na karami, (a wajansa)”.
Comments
Post a Comment