MUHIMMANCIN MALLAKAR LITATTAFAN HARKAR MUSULUNCI

ME YA SA AKASARIN JAMA'A BA SU DAMU DA KARANTA LITTATTAI BA?

Littafai: *SHAWARATA GA 'YAN UWA*

Lallai yana da muhimmanci sosan gaske kowane Buraza da ma Sista su muhimmanta sayen Littattafan da ake yinsu wadanda suke da alaka da Tarihin Jagora (H) ko Harkar Musulunci. Ko da muna ganin mu a kan idonmu ake yin abubuwan, kuma marubutan ma kila mun fi su sanin abin da ke faruwa a yanzu, akalla zai taimaki 'ya'ya da jikokinmu (zuriya) da ma al'ummar da za su zo nan gaba. 

Gaskiya na kan sha mamaki sosai ace duniyar 'yan uwa wanda ake lissafa miliyoyin mutane, amma in aka buga littafi kwafi 2,000 a kan Tarihin Harka ko wani abu mai alaka da hakan, sai ka ga ya dauki watanni bai kare ba. Tare da cewa ƙimar kudin da ake sakawa littafin ko rabin ƙimar littafin bai kai ba. Ko mene ne dalili? Ni na kan ba da cewa muna ganin ba mu da bukatuwa ga bayanan da ke cikinsa ne a yanzu, don haka ba sai mun mallaka ba, saboda in ma mun mallaka ba mu da lokacin karantawa a yanzun. Ba mu duba amfaninsa a can gaba. 

Kuma ba ma can gaba ba fa, a yanzu din, za ka sha mamaki ka ga wasu imma 'yan bokon cikinmu ne, malamai ne, 'yan Media ne, Harisawa ne, ko Burazu ne, suna yawan tambayoyi a kan, a wane lokaci ne ma aka yi kaza? Mene ne ma kaza? Don Allah taimake mu da sunayen kaza ko ranar da aka yi kaza ko bayani kan kazan, alhali duk wadannan abubuwan wanda zai basu amsar ya san shi ma ya karanta su ne a wasu littafan da tare aka muku tallarsu sadda ake saidawa. Ko kace mutun ya koma ya duba a littafi kaza sai yace ai kuwa bai sayi littafin ba. 

Ya kamata lallai mu farka. Littafan da ke da alaka da Tarihin Harkar nan sun yawaita zuwa yanzu, kuma wanda ya fi kowanne tsada a saidawa a yanzu haka ina ga SHINE littafin DA'AWAR HARKAR MUSULUNCI na Cibiyar Wallafa, wanda ya kunso Tarihin Harka da Waki'o'i da Fitintinu da abubuwa da dama, Naira dubu daya kacal ake saidawa, amma ina ga har yanzu ba za a rasa sauran na saidawa a cikin kwafi 2,000 da aka buga ba. Kuma babban littafi ne da ke da shafuka 400 cif. 

Gaskiyar magana shine idan masu bincike su rubuta ba su gajiya ba, bai kamata masu ba da dari kaza su fansa mu gaza ba. Ko ba komai duk masu Wallafa littafan nan, a daidaiku ne ko karkashin wata Lajana ce, za ka samu suna yi ne kawai a matsayin ba da gudummawarsu, amma ba Harkar neman kudi bane. Da yawa kudi bai fita bare a sa rai da riba don an buga littafi a duniyar Harkar. Kila saboda ba a sayan adadin da zai sa a samu riba din. 

Izuwa yanzu, akwai littafai manya da kanana da suke bayani a kan Shaikh Zakzaky da Da'awarsa wanda bai kamata ace kowanne dan uwa bai da akalla rabin adadinsu a akwatun littattafansa ba. Kowa ya duba ya gani, wanne ne bai da shi, wadanne suka wuce shi? Wadanne zai iya samowa da gaggawa? 

Daga irin wadannan littafan akwai:

1— BAYYANAR SHARAFUDDEEN na Al'amin Isa Assakwati. 
2— MALAM MALAM NE na Haruna Yusuf Shalleng.
3— YUSUFUZ ZAMAN na Ibrahim Potiskum
4— KARAMOMIN SHAIKH ZAKZAKY na Malam Yakubu Yahya da Malam Abubakar Abdullahi.
5— SHEKARU 60 MASU ALBARKA na I.M Publication (Almizan)
6— TARIHIN HARKAR MUSULUNCI DA SHAIKH ZAKZAKY na Malam Muhammad Sulaiman
7— TA'ADDANCIN GWAMNATIN ABACHA na Danjuma Katsina. 
8— WAKI'AR 19 APRIL A KATSINA na Aminu Bara'a
9— KISAN-KIYASHIN ZARIYA DAGA GANAU BA JIYAU BA na Mizani Publication 
10— DECEMBER 2015 MASSACRE; SURVIVORS ACCOUNT na Ibrahim Musa. 
11— COMPENDIUM OF THE SOCIAL STRUGGLE na Free Zakzaky Champaign Committee. 
12— MANUFAR DA'AWARMU na Shaikh Zakzaky (Cibiyar Wallafa)
13— HARKAR MUSULUNCI na Shaikh Ibraheem Zakzaky (Cibiyar Wallafa)
14— YUNKURIN KASHE SHAIKH ZAKZAKY A SHEKARU 10 na Cibiyar Wallafa. 
15— SHAIKH ZAKZAKY IKON ALLAH na Cibiyar Wallafa. 
16— DA'AWAR HARKAR MUSULUNCI na Cibiyar Wallafa. 
17— MUHIMMAN RANAKU 200 A TARIHIN HARKAR MUSULUNCI na Cibiyar Wallafa. 
18— KISAN-KIYASHIN ZARIYA DA ABUBUWAN DA SUKA BIYO BAYA (Dec 2015 — January 2021) na Cibiyar Wallafa. 

Wadannan wasu daga littafan da muka iya tuna an rubuta su masu alaka da Tarihin Jagora da Harkar Musulunci. Ta yiwu akwai ninkinsu da ba mu kawo su ba ma. 

Wasu a cikinsu sun bace bat ba a iya samunsu a yanzu, amma wasu daga ciki, musamman No, 6, 8, 9, 10, 13 da 16 har yanzu in mutum ya tsananta nema zai iya samu a kasuwa ko a wajen Mawallafansu. 

Haka ma littafai biyun karshe na Muhimman Ranaku 200 a Tarihin Harkar Musulunci, da kuma littafin Kisan-Kiyashin Zariya Da Abubuwan Da Suka Biyo Baya, yanzu ne ma za su fito kasuwa, ana sa ran a cikin watan Rajab din nan. Kuma kudin kowanne daya bai wuce Naira 500 ba kila, don haka bai kamata kowanmu ya yi sake su wuce shi ba. 

— Saifullahi M Kabir.

Comments

Popular posts from this blog

TARIHIN SHEIKH ABUL FATHI MAIDUGURI

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA