RASHIN ADALCIN DA AKAIWA SHEIKH ABDULJABBAR

BABBAN ZALUNCIN DA AKA WA SHAIKH ABDULJABBAR KABARA

Makiyansa na ta jone-jone da yanke-yanke ga karatuttukansa

Malamin nan, wanda asalinsa yana bin makarantar Sunnah ne, a tsawon shekaru yana gabatar da karatu a fannoni daban-daban na addini, kuma yana da almajiransa da suke tafiya tare da shi a karkashin wata inuwa da suka kira ta da Ashabul Kahfi.

Duk karatunsa a littafan Sunnah yake gabatarwa, bai taba dauko littafin Shi'a ya karantar da shi ko ya ba da hujja a cikinsa ba. Tare da cewa bai wofintu daga karanta littafan Shi'a din ba, kuma har ma yana ikirarin cewa akwai ruwayoyi da yawa a littafan Shi'a wadanda suke rage martaba da darajar Annabi (S) wanda in aka bashi dama ko in ya samu dama, zai waiwaye su ya warware su ya fito da rashin asalinsu da kuma ta inda suka shigo cikin littafan Malaman Shi'a din.

Sai dai wannan abin da ya kudiri aniyar yi, in abin ya zo yi ne ba lallai a samu wata matsala da shi a duniyar Shi'a ba, saboda dama Shi'anci bai taba kudurce cewa akwai wani Littafi Sahihi da duk ruwayar da ta zo a cikinsa ya inganta baki daya ba in banda Alkur'ani Mai Girma. Sauran littafan Hadisan Shi'a baki daya basu da ISMA ne cewa su Ma'asumai ne ba kuskure a cikinsu ko duk abin da ke cikinsu ingantacce ne kamar yadda Sunnah suke da wasu littafai har shida da suke ikirarin ingancin duk abubuwan da ke cikinsu.
Tunda Shaikh Abduljabbar na bisa turbar Ahlussunnah ne, kuma da littafan Sunnah yake ba da karatu, wannan ya bashi damar ya yi binciken kwakwaf a cikinsu, in har ta bayyana masa akwai wasu matsaloli ya fitar da wadannan matsalolin, ko da kuwa zai rushe Aqidar da aka doru a kanta na Ismantar da wasu littafan Hadisan Sunnah da nuna ba kusa cikinsu, tunda ba Fiyayyen Halitta (S) ne yace su Ma'asumai bane, ba wani wanda ya isa ya tabbatar da rashin kuskuren cikinsu.

Sai kuma aka wayi gari, makiya addinin Musulunci musamman a kasashen Turai, sun shagalta da zagi da cin mutunci da aibata Manzon Allah (S) da duniyar Musulmi baki daya, kuma idan aka titsiye su a kan su kawo hujjar wannan cin mutunci da suke yi, sai su karanto maka Hadisi a Sahihul Bukari, ko Sahihin Muslim, ko Abu Dawuda, ko Nasa'i da sauransu, ko su ce ka duba shafi na kaza cikin littafin kaza, an kawo ruwaya daga Anas Dan Maliki, ko daga Nana A'ishatu ko Nana Hafsatu cewa Annabin Musulunci (S) yana kaza da kaza.

In ka je ka duba, sai ka ga ruwayoyi birjik da suke nuna Manzon Allah (S) a matsayin wani mutum mai yawan sha'awa, ta hanyar da ya ga mace sai jikinsa ya fara rawa, ya maza ya je wajen matarsa. Ko ya kira wannan da ya gani din. Ko ka ga wani labari wai Ingantaccen Hadisi ne cewa Annabi (S) na wa Jikansa Hasan wasa har da tsotson azzakarinsa. Ko ka ji wani abu wai hadisi ne wai Annabi na zuwa kallon rawa shi da matarsa, har ya cincidata da kafadarsa suna kallo. Ko ka ga wani abu wai Hadisi ne ingantacce, cewa Annabi (S) na zuwa wajen wata mata da ba wanda ya taba saninta in ba a wannan hadisin ba, ba wanda ya san wace ce ita, wai sai ya kwanta a jikinta har ta rika karkade masa kwarkwata a kai.

Hadisai birjik na rashin kan gado a littafan Sunnah, kuma wai ingantattu ne a bisa wasu sharudda da wasu ne a can baya suka kirkire su ba Manzon Allah (S) ba. Ba ma Sahabbansa ba. Kuma suna cin mutuncin Annabi ne da sukan Musulunci da zagi ga addinin baki daya. Ace maka wai wata rana ana tafiya sai Annabi ya kware al'aurarsa ya kama fitsari a tsaye Sahabbai na kallonsa har ma suna ruwaitan hakan. Ko a ce wata rana Annabi na wa mata jawabi jikinsu a kwaye ba Hijabi, sai can ya ga suna jajjan rigunansu suna kokarin rufe jiki, yace ya aka yi? Sai suka ce ga Usman nan zuwa. Sai yace ai dole ku ji kunyar wanda Mala'iku ke jin kunya.

Da sauran labaran karya da kanzon kurege dai wadanda da su ne makiya addini ke fakewa suna sukan Annabi (S), kuma in suka soka ko Musulmi sun fita zanga-zangar, karshe dole su hakura saboda kafiran kan fito da hujjoji daga littafan Musulunci ne su yada, sai a ga ba su ne suke cin mutunci ba a asali, ruwayoyi suka gani a littafan da Musulmi suka ce komai da ke cikinsu daidai ne.

Wannan ne ya farkar da Shaikh Abduljabbar Kabara kan dacewar ya zo ya yi kokarin zakulo wadannan labaran izgili ga Annabi (SA) din, ya nemo asalinsu daga ina suka shiga littafan Musulmi har yau makiya musulunci suke amfani da su wajen sukan Musulunci da Annabin Musulunci din? Wannan aikin ya fado a tsawon shekaru akalla biyu ko uku zuwa yau. Wanda kuma Alhamdulillahi, Musulmin kwarai suna jin dadin yadda yake zakulo ruwayoyin ya kuma fito da hakikanin gaskiya kansu cewa kirkirarsu aka yi don a bata shaksiyyar Annabi (SA) da Iyalan Gidansa (AS).

Da wasu miyagun Malamai a Kano suka ga Da'awar Shaikh Abduljabbar na kokarin kore Hadisan karya da cin mutuncin Manzon Allah (S) na habaka, mutane na fahimta, har suna yabawa, suna kara cincirindo zuwa gare shi don samun ingantacciyar fahimtar addini. Addinin da bai yarda ya kai iyayen Annabi wuta ba, addinin da bai yarda da ingancin Hadisan da ke cin mutunci da izgili ga Annabi (S) ba, addinin da ke nuna Annabi (S) a matsayin cikakken Ma'asumi, tsarkakkakke dan tsarkaka, tsaftatacce daga tsatso tsafta, wanda yake bisa mafi kyawun dabi'u. Sai suka yi kokarin kirkirar sharri.

Sai kawai Malaman nan suka samo jawabai da karatuttukan Shaikh Abduljabbar, wanda yake karanto irin wadannan ruwayoyin na cin mutuncin Annabi daga littafansu na Sunnah, yana kokarin yi musu raddi da inkarin ingancinsu. Sai suka daddatse karatun, suka yayyanko suka hada shi yadda idan mutum ya ji, zai dauka Shaikh Abduljabbar din ne ke da wannan Aqidar na cin mutuncin Annabi (S), alhali ya karanto ne daga littafai, sun yanke bayanin yadda ya nakalto din. Alhali ya ma ruwayar raddi bayan ya kawo bayaninta, sai suka yanke inda yake raddin.

Ka ga mai ji da ya ji zai ce shikenan Abduljabbar ya ce Annabi na zagayawa wajen wata mata ya kwanta a jikin matan da ba muharramansa ba ta cire masa kwarkwata. Ka ji Abduljabbar yace Annabi na kware al'aura ya yi fitsari a tsaye. Ka ji Abduljabbar yace Annabi na fitowa ba ko riga a jikinsa, ko Sahabi kan zo gaban Annabi ba kaya a jikinsa shima su dade a tare. Ka ji Abduljabbar yace Annabi na kaza da kaza. Alhali an yanke bayanan ne, ba shi ke cewa hakan ba, karatu ne a littafan Sunnah ya karanto, ya kuma yi musu martani tare da kore faruwarsu gaba daya ma a hakika.

Irin wannan salon suka bi, suka yanka bayanai suka dasa, suka kaiwa Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, suka ce a matsayinsa na Khadimul Islam ya dauki mataki, Abduljabbar na zagin Annabi, ko yana fadan wasu abubuwa da za su iya sa Musulmi su tunzura. Shikenan Khadimul Islamu ya ce kai tsaye a rufe makaranta da masallacin Abduljabbar har sai an yi bincike.

Miyagun Malaman sun so ne kai tsaye gwamnati ta dirarwa Shaikh Abduljabbar da rusa gine-gine da kisa ma ko kamu da dauri gare shi da almajiransa nan take. Amma sai Allah Ya takaita, gwamnatin ta ba da rata ga wannan bukatar tasu. A wannan tsakanin ne kuma Shaikh Abduljabbar ya yi magana da gwamnati din, da neman ta ba da dama shi ya zauna da wadannan Malaman ya kare abubuwan da suke masa Da'awa wadanda a hakikanin gaskiya ba shine Da'awarsa ba. Gwamnati ta ce ta ji ta amsa, nan da mako biyu za a zauna.

Yanzu sai Malaman nan suna ta zuzzuƙewa, suna nuna ba amfani a yi wannan zaman. Kamar suna cewa ne kawai gwamnati ta gamsu da abin da suka kawo a tafi a haka, kar ta bincika ko ta bi matakan da za su fitar da gaskiyar al'amarin. Sai ya zama kai tsaye Malaman nan suna tsoron wani abu ne. Abin nan kuwa shine cewa sun yi sharri ne ga Shaikh Abduljabbar, wanda in aka zauna da shi za a ji akasin abin da suka gabatar ne.

Ba su so a zauna, saboda idan aka zauna, za a zauna ne a kan cewa Abduljabbar ka ce kaza da kaza a kan Annabi (S). Sai Shaikh Abduljabbar yace ba ni na ce kaza ba, Sahihul Bukari ko Ibn Maja, ko Tirmizi ne ya ruwaito daga wani mutum mai suna Anas Dan Maliki cewa Annabi ya yi kaza. Shine na yi martani ga abin, na kawo dalilai da suka tabbatar da wannan labarin da ke cikin Hadisin wanda yana cin mutunci da taba darajar Annabi (S) ne, bai auku ba, karya ne. Na yi bayani a karatu na kaza da kaza, ga bayanin kwamitin bincike ta je ta saurara ta ji martani.

Shaikh Abduljabbar zai ce ba aqidarsa bace sukan Annabi, aqidarsa ma ita ce kore miyagun Hadisai da tsaftace Shaksiyyar Annabi (S). A nan za a gano cewa ashe ba daga shi bane, ashe littafan Sunnah ne suke taba shaksiyyar Annabi din, shi Malam Abduljabbar na ba Annabi kariya daga miyagun Hadisan. Daga nan duk mai nufin shiriya, zai watsar da shirme ya rungumi inda ake kimanta Annabi (S). Ya yi kama da kasuwar Miyagun Malaman da suka rufe ido sai sun kare wadannan shirmen zai rushe face ga makafin mabiya. Kuma wannan suke gudu a yanzu.

Albishirinku shine, tunda kun gina Da'awarku asali a kan kirkirar karya da zaluncin yanke magana da jona ta ne, to gaskiya za ta warware karyar naku. Kuma kuna ruwa tsundum, kusa da.......

— Saifullahi M Kabir
16/2/2021

Comments

Popular posts from this blog

TARIHIN SHEIKH ABUL FATHI MAIDUGURI

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA