Shekara 1 da yin wannan jawabin: fitowar 'yan'uwa daga kurkuku ba zai sa mu manta da abinda akai mana ba

Shekara 1 Da Wannan Jawabin !

Fitowan 'Yan'uwa Daga Kurkuku Ba Zai Sa Mu Manta Da Abinda Aka Mana Ba. 

   Inji Sheikh Adamu Tsoho Jos

Insha Allah nan da wani 'dan lokaci muna da sika muna da tsammanin Allah zai kawo mana karshen wannan jarrabawa na fitowan Jagoranmu Sayyid Zakzaky (H).

Duk da cewa sun kashe darurukan Almajiran Malam, kuma har yanzu suna kan yi, Alhamdulillah a ranar Alhamis sun saki sauran 'yan'uwa da suka kama tun lokacin wakiyar Zariya. Kuma a yankin Jos akwai mutane 4 da suka kasance cikin wanda aka saka.

Duk da yake muna magana ne akan Sayyida Fatima (As), abinda zamu yi koyi da Fatima (As) shine jajircewa ta tsayu ta sadaukar da rayuwan ta bata ji tsoron kowa ba. Duk abinda aka mata bai sa taji tsoron kowa ba, tayi tsayin daka wajen kare jagorancin Imam Aliyu (As).

To, dan haka hakki ne muyi koyi da ita wajen kare hakkin Malam (H). Abinda ya faru da Malam wajibin mune mu sadaukar da rayuwan mu da dukiyan mu wajen kare Malam. Wannan shine abinda Sayyida Fatima tayi aka shahadantar da ita. 

Menene dalilin shahadanta shine za'a kai ga Imam Aliyu (As) a cutar da shi ta tsaya a bayan kofa ta hanasu shigowa aka tokari kofar har ta kai ga cikin da ke jikin ta ya zube, kuma ya zama sanadin shahadanta. Don haka kare rayuwan Malam wajibi ne mazan mu da matan mu. Malam yana alamta koyarwa ne na Ahlulbaiyt shiyasa har yanzu suke tsare dashi.

Azzalumai basa son ganin mu muna cewa #FreeZakzaky, don haka hakkin mune mu cigaba da FreeZakzaky a kowanne gari musamman a garin Abuja. 

Ko fitowan da 'yan'uwa suka yi daga Kurkuku wasiyyan da Malam (H) ya musu shine 'A Cigaba Da Abinda Ake yi Kada A Bari ' daga karshe muna rokon Allah ya faran tamana rai da fitowan su Malam (H) domin su fita su samu lafiyansu.

Daga Jawabin Sheikh Adamu Tsoho Jos wanda yayi ranar 23-Feb-2020 a wajen taron Khataman Wuladan Sayyida Fatima (As) wanda 'Yan'uwa Mata Sister Suka shirya a Jos.

@Media Forum Jos.

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky