WACECE SAYYIDATU NISA'IL ALAMEEN??

SAYYIDA ZAHRA (SA)
Lokacin da masu jawabai ke jawabi, su ce ita ce kaza, ita ce kaza, da suna son takaita bayani kawai kamata ya yi su ce ita ce yardar Allah (T), ita ce kuma tsokar jikin AnnabinSa (S).

Ƙurewar matsayi ba abin da ya kai cewa da yardarta Allah ke yarda, da fushinta yake yin fushi. Duk abin da Sayyida Zahra ta yarda ta aminta da shi, ko ya faranta mata, kai tsaye haka yake a wajen Madaukakin Sarki. Haka ma duk wanda Sayyida Fatimah ta ƙi, ko ta yi fushi da shi, ko ya bata mata, ba wani maraba da ƙi, fushi ko ɓatawa Allah Ta'ala.

To, mafi soyuwa kuma fiyayyen talikai a wajen Allah Ta'ala, shine Annabi Muhammadu (S). Sayyida Zahra tsokar jikinsa ce. Tsoka wane iri? Annabi (S) yace ita zuciyarsa ce. A wani waje kuma yace ita ruhinsa ce. A gangan jiki zuciya ce jigo, a gudanan jiki baki daya ruhi ne jigo, duk Zahra (SA) ce wadannan bangarorin na Manzon Allah (S). Ashe ita ce shi, shi ne ita kai tsaye.

Idan mutum ya raina 'ya'yanta, sai yace ai ita ce uwar wadannan yaran; Hasan da Husain (AS), duk kuwa da cewa su ne Shugabannin duk wani wanda zai shiga Aljanna a duk halittu Allah in banda Annabi (S), Amirulmuminin da uwarsu, Sayyida Zahra (SA). To ba kawai ita uwar Imam Hasan da Imam Husaini (AS) bace, ita uwar Manzon Allah (S) ce.

Ga shi dai ba sunan mahaifiyar Annabi take da shi ba, ba Aaminah aka saka mata ba, bare ace irin na Hausawa ne, su kan ce wa mai sunan mamarsu Mama, ko da su suka haife ta. Shi Manzon Allah (S) kai tsaye ya ke kiran Sayyida Zahra da 'Ummu Abiha', wato Uwar Babanta (S). Sai ka rasa ma'anar hakan, in ma abin ka tambayi malamai ne sai dai su ce maka, ai ta daukewa Annabi (S) duk wani nauyi da uwa ke daukewa ɗanta ne. Hakan ma girma ne, amma tabbas abin da ke bayan wannan al'amari ne da Allah (T) da ManzonSa da Ma'asumai ne masanansa.

Ya ishi Sayyida Zahra (SA) girman matsayi cewa sunanta Faɗima, ma'ana fansa ga duk wanda yake sonta a ranar Alkiyama. Na ce waye masoyin Sayyida Zahra (SA)? Sayyid Zakzaky (H) ya bani amsa da cewa, ana son Sayyida Fatimah ne ta hanyar tausaya mata kan zaluntar da aka mata, kuma ana sanin zaluncin ne ta hanyar karanta tarihinta sahihi da gane macutanta da yi musu bara'a na har abada. Nace Na'am Ya Abbah. Na ji na yi bara'a ga macutanta, kuma ki mai biyayya da kauna a gare ta ne. Yace in hakan ya samu, to saura ka yi kokarin koyi da koyarwarta da na yayanta tsarkaka (AS). Allah ka mana wannan Arziƙin. 

Ya Allah Ka sa Sayyida Zahra ta yarda da mu. Ka sanya mu cikin wadanda za ta ceta a ranar firgici da fargaba. Allah ka sa soyayyarta ta amfanemu duniya da lahira.

— Saifullahi M Kabir

Comments

Popular posts from this blog

TARIHIN SHEIKH ABUL FATHI MAIDUGURI

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA