Yunƙurin Hana Al'majirci; Ga abinda Sheikh yaqub Yahaya yace...

Kokarin Hana Bara Da Almajiranci: Sakon Sheikh Yakubu Yahaya Ga Gwamnati
Sheikh Yaqub Yahaya

Daga: Bilya Hamza Dass

Sheikh Yakubu Yahaya, sananne Malamin Addinin Islama ne mazaunin garin Katsina, me karantarwa tsawon shekaru, kuma yana daga cikin Almajiran Sheik Ibraheem Zakzaky. Malamin ya aika sako ga hukumomi da Gwamnatoti a kokarin da suke na hana tsarin karantarwa na Almajiranci da Bara, inda ya bayyana ra'ayin shi da kuma yanda yake kallon yakamata ayi, yayi Jawabin ne a wata ganawa da yayi da manema labarai a jihar kwanakin baya.

“To abinda muke kallon wannan shine mukaddima na rufe makarantun Allon duk kasar nan baki daya. Domin yanzu abinda gwamnati ke babatu akan shi shine makarantun allo sun dame su da bara basuson bara. Bamuce bara addini ne ya kawota ba, bamuce bara dede ne ba, yin bara ba ba dede bane, amma menene ya sanya musulmi suka zama mabarata? ai da can kasar a hannun su take gidan Mallam ake biyawa aci abinci har a dauka akai gida, da bature yazo ya karbe komai a hannun Malami sai Malami yaga babu abinda zaiyi sai ya koma yana tsare addinin shi, yana bara yana cin abinci yana rayuwa wannan shine ya haifar da bara.

“Saboda haka idan anaso ayi maganin wannan matsalolin kamar yanzu wannan makarantu da aka rufe tinda ansan dasu tsawon shekaru ba rana suka bulla ba abinda gwamnati yakamata suyi inda sunada hankali sai ta rubuto takarda da   bayanai cewa; Allah gafarta Mallam muna ganin abubuwan da basu dace ba makarantar ka mun baka wata uku ka gyara haka mukeso da bayanan aciki. 

“Sai shikuma ya duba yagani idan zai iya gyarawa ya gyara idan baze iya ba sai ya sallami kowanne yaro yace sai na samu hali na gyara kudawo saboda bancika wadanan "conditions" ba wannan shine abinda yakamata suyi. Idan ba har yakasa tinda yana amfan jama'a iyayene ke kamo hannun yaransu su kawo, wasu manyan daraktocine wasu manya ne sune suke dauke yaransu saboda sun gagaresu su kawo su, su kuwa Malamai su kwancesu su koya musu karatun Alkur'ani da ibada har su zama mutanen kirki. Yana amfanan al'ummar unguwa kuma ansani a titi akeyi ba a gida akeyi a boye ba.

“Idan ana ganin dakunan da ake kwana yayi kadan wuri kaza-kaza to shikenan yanzu abinda za'ayi sai gwamnati ta temaka masa tasai masa wasu gidaje ko a bashi wani fili ayi gini ayi masa ajujuwa ayi masa komai da komai sai ace to dawo nan kaci gaba da karantarwan ka, kuma banda kaza banda kaza. Sai a rika aiko "supervisors" su rika bi suna ganin menene akeyi wannna shine abinda yakamata gaamnati tayi kenan.

“Amma tinda "UNICEF" ta sanyo almajiranci a gaba tana cewa wai akwai mutum miliyan goma sha, basu da ilimi suna yawo a arewacin Najeriya kaza da kaza almajirai suke nufi. Harma nake cewa almajiran allo su shirya tasu tana zuwa anfaro ne domin azo kansu, wannan shine gaskiyar magana anma idan ance ko ana luwadi da yara kaje makarantun Boko kagani menene ba'ayi? nan akeyin "lesbian" mata na auren mata maza na auren maza, 'yan mata da ciki hadama malamai suna temakawa.

“Kwanan nan bakuji a BBC anyi ra'ayi rigi ba? Malaman jami'a suna yiwa daliban su ciki. Saboda haka wannan abin kunyar da ake tuhumar makarantun dashi kaje na gwamnati canma anayi. Kaje gidan yari kaga yanda ake kwanciya kifi sadin iyakar kunci kenan. Mu bazamu bawa gwamnati uzuri ba tinda almajiran allo sunada amfani almajiranci yana da amfani duk wani limami ko wani babban malami ko wani mashahur, kaje gidan yari ka kirga kagani dan fashi da makami almajirin allo guda nawa ne? masu shaye shaye almajiran allo guda nawa ne? amma tambaya kaji dan Sakandire guda nawa ne? wanda yagama jami'a babu aiki guda nawa ne?.

“Mu bamuce makarantun allo su tafi yanda suke ba amma idan za'akawo gyara da cigaba bada karfin tuwo a keyi ba, lallashin mutane ake har su fahimta. Su Malaman a basu dama suyi magana a Radiyo kamar yanda akeyi da wayun su mana. Kullum duk mutane sunyi shiru Malamai da sarakuna kamar anbawa kowa rashawa domin yayi shiru. Su iyayen basu taba kai karaba cewa an cutar da yaran su amma wani daga nesa saboda "UNICEF" batason taga almajirai. To azo a inganta makarantun allo mana ayi musu Bohol, wajajen karatu, makewayi da tsafta ayi musu yunifom. Kaje tambaya kaji almajiran allo nawane cikin 'yan Boko Haram?”
#Repost

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky