ANYI TARON TUNAWA DA SHAHIDAI A ABUJA 07/03/2021

RANAR SHAHIDAN HARKA ISLAMIYYA

Muhd Idris

A yau ne aka gudanar da bikin tunawa da shahidan harka Islamiyya da aka saba yi duk shekara a garin Suleja karo na 30.

Shugaban Mu'assar ta kasa Sheikh Abdulhamid Bello ne ya kasance babban bako mai jawabi inda ya jaddada ma yan uwa nauyin da ke kansu na sauke hakkin shahidan na harka. Malamin ya ankarar da cewa har kawo yanzu dai abin mamaki ba a sauke shi wannan hakki kamar yadda ya kamata. 

Tun kafin haka sai da ya kawo matsayin shahada da kuma shi kansa shahidi a musulunci, da ya dawo ga azzalumai kuma ya ce na da can ma ba su iya hana harka ba bare na yanzu, ya zaiyano yadda azzaluman kasar nan suka rika aukar da waki'a daya bayan daya ana samun shahidai har kawo yanzu. Ya kuma kara kira ga yan uwa wajan kokarin sauke hakkin Jagora a kansu.

Farfesa Abdullahi Danladi shi ya gabatar da takaitaccen jawabi tun da fari kan aiyukan ita wannan Mu'assar ya kuma yi godiya ga yan uwa kan kokarinsu gareta.

Kamar kowace shekara mawakan harka sun rera wakokin shahada da shahidai masu kayatarwa sai kuma faretin girmamawa mai ban sha'awa ga shahidan wanda Hurras na harka Islamiyya suka yi.

Shi irin wannan taro Jagoran Harka Islamiyya Sheikh Ibraheem Zakzaky ne ya assasa shi shekaru 30 da suka wuce domin tunawa da shahidan harka abin da ya jawo kafa Mu'assa mai zaman kanta don kula da wannan lamari wanda kuma ke da alhakin tsara da shirya komai da ya shafi shahidan ciki har da tsara wannan irin taro.

Dubban yan uwa da dama ne daga bangarorin kasar nan suka samu halarta duk kuwa da cewa ita Mu'assa din da kanta ta dan takaita taron don wasu dalilai. Haka nan wasu cikin manyan malaman ita harka din sun samu halarta kamar Sheikh Sidi Muneer, Sheikh Muhd Abare, Sheikh Aliyu Tirmizi Kaduna sai Sheikh Sidi Badamasi Ya'akub. An dai yi taron an kuma tashi lafiya.

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky