DUK ACIKIN SAHABBAI IMAM ALI YAFI KOWA DARAJA

Duk Cikin Sahabbai Imam Aliyu Yafi Kowa Daraja Bayan Manzon Allah (Saww).

    Inji Sheikh Adamu Tsoho Jos. 
Bayan bayyanar Annabcin Manzon Allah (Saww) daga wurin Ubangiji Allah Ta'ala, Sayyida Aliyu ne ya fara karban musulunci kafin sauran Sahabbai. Har ma yana cewa daga cikin kususiyyar daraja da Allah ya mishi, yayi Sallah tare da Manzon Allah  shekaru 7 tare da uwargidan Manzon Allah Sayyida Khadija a lokacin da babu wanda yake Sallah a duniya sai su.

Da yawa yawancin mutane basu fahimci ƙadiya nasu Ahlulbait ba, wanda ake musu mummunar fahimta ta yadda duk abin da aka faɗa akan su sai mutane su ga ana fifitasu ne akan sauran Sahabbai. Shi yasa har yanzu kamar muna marhala ta farko ne na bayani akan su wanene Ahlulbait da matsayin su da kususiyya su.

Idan muka koma tarihi zamu ga cewa da Manzon Allah (Saww) da Sayyida Aliyu tushen su ɗaya ne, asalinsu ɗaya ne. Menene asalin Manzon Allah (Saww)? Shine faɗin Allah (T) da yayi a cikin Alkur'ani ce wa, "Asali Manzon Allah Haske Ne Daga Allah" to, wannan haske shine ya gangaro tun daga Annabi Adamu, tsatso bayan tsatso. Kuma hasken Manzon Allah bai taba shiga wani tsatso wanda ba tsarkakakke ba.

Manzon Allah yake cewa Imam Aliyu kai Ɗan'uwa nane duniya da lahira, Manzon Allah ya faɗibhaka ne a lokacin da ya ƙulla 'ƴan'uwantaka tsakanin Sahabbai. Manzon Allah ya bayyanar da matsayin Sayyidina Ali inda yake ce wa, Ni Allah ne ya tarbiyantar da ni, Sayyidina Ali kuma tarbiyya nane. A lokacin sa aka fara yiwa Manzon Allah wahayi Sayyidina Ali yace Ya Rasulullah wannan ƙaran da naji ƙarar menene ? Sai Manzon Allah ya ce Aliyu kaji wannan ƙara?  sai yace na'am Ya Rasulullah!
                Sai Manzon Allah yace ƙarar Iblis ne, saboda bakin cikin wahayi da ya soma yi. Yasan cewa yanzu kuma a duniya ya tashi daga abin bauta shi yasa yayi wannan ƙara. Sai Manzon Allah ya ce wa Sayyidina Aliyu ashe kana jin abin da nake ji, kana ganin abin da nake gani sai dai kai ba Annabi ba ne. Wannan duk Sahabbai na Annabi babu mai wannan daraja ko kususiyya nan sai Sayyidina  Aliyu Bin Abuɗalib (As). 

Matar da Sayyidina Aliyu ya aura Sayyida Fatima (As) ba a taba matar da ta kai ta ba, tun daga Hauwa'u har koma bayan Hauwa'u. Itace sarauniyar matan duniya da lahira,  kuma ita kaɗai ce yazo a ruwaya ce wa, a ranar da 'Yauma Ta Kumu' tun daga Annabi Adamu har al'ummar ƙarshe zuwa ranar da za a tashi duniya nan, a hadu da mutane da aljanu da Mala'iku da dukkan halittar Allah, a wannan rana mala'ika zai yi kira daga "Farfajiyar Al'arshin Allah" yace kowa ya rintsa idonsa ya sunkuyar da kansa ga 'Ƴar Manzon Allah Sayyida Fatima zata wuce ta shiga Aljanna. 

Daga cikin jawabin Sheikh Adamu Tsoho Jos wanda ya gabatar a wajen Mauludin Imam Aliyu (As) a ranar 06-March-2021 a wajen Mauludin Imam Aliyu (As), Wanda Dandalin Matasa Garin Jos suka shirya a Layin Zana.

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky