"Duk Wanda Ya Yada Hoton Mace Babu Hijabi Yana Da Kamasho A Cikin Zunubin Da Ta Aikata..." - Shaikh Adamu Tsoho Jos
"A 'yan tsakanin nan mun ga mutane ciki har da wasu 'yan uwa masu ta'ammuli da shafukan sada zumunta suna ta yada hotunan wata da aka ce 'yar wasar Hausa ce ba tare da Hijabi a jikinta ba. Yin hakan ko da kuwa da sunan yabo ne, kuskure ne. Ya kamata a yi yabo ne da abin da Allah ya halatta. Ana iya ambaton suna, ba sai an yada hotuna marasa Hijabi ba. Bai kamata a samu 'yan uwa cikin hakan ba.
Ya kamata Muminai su sani cewa duk wanda ya yada hoton Mace ba tare da Hijabi ba, yana da kamasho a cikin zunubin da ta aikata na rashin cika umurnin Allah (T) kan suturce jikinta. Domin ita Mace dukkan jikinta al'aura ne in ban da fuska da tafukan hannu. Kuma an wajabta mata boye ado da sanya Hijabi daga dukkan ajnabanta.
Abin takaici ne yadda muke ganin har wasu 'yan uwa su kan turo hotunan iyaye ko 'yan uwansu Amawa babu Hijabi. Da ma yadda ya zama wasu 'yan uwa din, musamman matasa Mata, suna daukan hotuna tare da ado suna yadawa a kafafen sada zumunta, wanda hakan kamar yana kokarin rushe tarbiyar riko da Hijabi wanda addini ya karantar da mu. Hakika in muka yi hakan, ba mu taimaki kanmu ba kuma mun ci amanar addininmu, mun ci amanar su Malam (H) kan turbar da suka dora mu a kai a wannan 6angaren. Hakan kuma ba abu ne mai sauki ba.
Comments
Post a Comment