Wane Ne Sheik Abul Fatahi Maiduguri? Daga Aliyu Ahmad . Cikakken sunansa shine Sheik Ahmad Aliyu Yarwa amma ana yi masa lakabi da Sheik Abul Fatahi. Ya rayu a duniya shekaru 82, kenan an haife shi a shekarar 1919. Da rasuwarsa yau shekaru 17 kenna, domin ya rasu ne a shekarar 2003. . An haife shi a wani kauye da ake kira Sandiya amma an fi saninshi da Shanduwa a yanzu, a gundumar Konduga ta jihar Borno. A nan ya taso har ya iya hawan doki da al'adun kauye. NASABARSA: Sheikh Ahmad bin Aliyu bin Ahmad bin Aliyu bin Muh'd Mustapha bin Muh'd Mukhtar bin Adam bin Dawud bin Abdulganiyyu bin Zubair bin Abbas bin Hussain bin Suleiman bin Ishaq (ta kan wannan suka hada kaka daya da Sheik Ahmad Tijjani) bin Aliyu Zainul Abideen bin Ahmad bin Muh'd Nafsu-Zakiyya bin Abdullahil-Khamil bin Hasanul-Musanna Bin Hassan bin Aliyu wa Fadima Bintu RASULILLAHI SAW. . Ta bangaren mahaifiya kuwa jikan Yarima Zubairu ne Sarkin Adamawa, sunanta Aishatu bintu Alh Muh'd wa Hauwa'...
Tarihin Shaikh Yakubu Yahaya Katsina A Takaice. Da sunan Allah mai Rahma mai Jinkai. Tsira Da Amincin Allah Su Kara Tabbata Ga Fiyayyen Halitta, Manzon Tsira Da Iyalan Gidansa Ma'abota Shiriya Da Shiryarwa. Garin, Shekara Da Wajen Da Aka Haifi Shaikh Yakubu Yahaya Katsina. An haifi Shaikh Yakubu Yahaya Katsina a ranar 15 ga watan Rajab,1376 Hijiriyya (1955 Miladiyya) a Unguwar Adoro da ke gab da Unguwar-madawaki a tsakiyar birnin Katsina. Mahaifansa. Maihaifinsa Alhaji Malam Yahaya, haifaffen karamar hukumar Rimi ne ta Jihar Katsina. Malama Maryam, mahaifiyarsa, 'yar asalin karamar hukumar Mani din Jihar Katsina ce. Ita 'ya ce ga Malam Zubairu, shi kuma Malam Zubairu da ne ga Malam Aliyu, dukansu haifaffun Karamar hukumar Rimi ta jihar Katsina ne. Iyalansa. Yanzu haka Shaikh Yakubu Yahaya yana da Mata biyu da 'ya'ya shatakwas: Tara Maza, Tara Mata. Ya aurar da guda Tara (tsakanin Maza da Mata), Yanzu Saura guda Tara. Karatunsa. A farkon farawa Malamin y...
Saura Kwanaki 15 Shaikh Zakzaky Ya Cika Shekaru 70 -Saifullahi M. Kabir TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H) Ranar Talata 15 ga Sha’aban, 1372 aka haifi Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), a unguwar Kwarbai da ke birnin Zariya ta jihar Kaduna. Mahaifinsa shine Malam Yaqoub dan Malam Ali dan Sharif Tajuddeen, shi kuma dan wani babban limami da ake kiransa da Liman Husaini. Kakan Shaikh Zakzaky na uku ya kasance daga cikin mutanen Shaikh Usman Danfodiye, wadanda ya tura su garuruwa a matsayin wakilansa, sai ya zama shi Malam Muhammad Tajuddeen Shaikh Danfodiye ya turo shi Lardin Zazzau ne a matsayin mai ba Amir din Zazzau, Malam Musa shawara da taimakonsa wajen tafiyar da harkokin al’umma akan tsarin Musulunci. A wata hira da aka yi da Shaikh Zakzaky dangane da tarihin rayuwarsa a shekarun baya, ya bayyana cewa: “Mahaifina Malamin Alkur’ani ne, haka ma kakana shima Malamin Alkur’ani ne, haka ma uban kaka na. Sai dai shi uban ...
Comments
Post a Comment