Kasar Allah Sheikh Zakzaky yakeso ya kafa, kuma sai ta kafu Daram

KASAR ALLAH SHAIKH ZAKZAKY KE SON YA KAFA, KUMA SAI TA KAFU DARAM! 

— Inji Shaikh Yakubu Yahya Katsina a wajen Nisfu Sha'aban 1442H. 

"Abin da mutane ba su fahimta ba shine, Malam Zakzaky (H) kasar Allah yake so ya tabbatar. Addinin Allah a cikin bayin Allah shine abin da Malam Zakzaky ke son ya tabbatar. Kuma bai tilastawa kowa sai ya yi ba. Mutane suna ganin kamar abin da Malam ke kira ba zai taba yiwuwa ba, ko kuma suna da wani dalili, kamar su ce ya za a yi ai kasar ba ta Musulmi bace gaba daya, akwai kiristoci da Maguzawa da sauransu, in aka ce za a yi Musulunci to akwai matsala.

"Na yi magana da wani irin haka nan, sai nace masa ai muna magana ne a kan Kasar Allah ba kasar Bature ba, kai kana magana a kan kasar Bature mai kan iyakoki yamma da kudu, arewa da gabas da central government. In ita kake magana a kai, to shi Malam na magana ne a kan kasar Allah da yace "Inna ardhiy wasi'a fa'iyyaya fa' abuduniy", ita Malam ke magana a kai. Saboda haka daga kan iyakar kasar Allah, sauran inda  ya rage, kuna iya Sharan Nijeriyarku, sai ku bar kasar Allah, to nan shi Malam ke magana a kai. Kasar Allah wacce za a kafa hukuncin Allah komai kankantanta komai girmanta komai fadinta. 

"Amma a matsayinmu na Musulmi mu kafa kasar Allah mai shari'a da Alkur'ani sabon Allah ne? Wa muka sabawa ma? Bature. In muka ce za mu kafa kasar Allah to mun sabawa Bature domin akwai Kasar Bature, sunanta Nijeriya. Tana da kan iyakoki da federal government. In aka ce to za a samar da kasar Allah a cikin Nijeriya wa aka sabawa? Bature aka sabawa ba Allah ba. Ballantana ma tabbatar da kasar Allah ibada ne. Shehu Usmanu cikin kasar Sarakuna ya tabbatar da kasar Allah. Ka ƙara jin labarin Sarakuna? Yauwa, to shine magana. Malam Zakzaky na magana ne a kan kasar Allah ba kasar bature ba, in kai kasar bature kake gani.

"Akwai wadanda suke cewa, idan aka ce za a tabbatar da kasar Allah to za a yi rigima, za a shekara da jinanai da kashe kashe da sauransu. Sai mu ce kwantar da hankalinka, dauki misali, ba akwai wasu mutane suna nan suna so a kafa Kasar Oduduwa ba? To su sun sadaukar da rayuwarsu da jinanensu da dukiyoyinsu da mutuncinsu don su kafa kasar Oduduwa ko mutum nawa zai mutu, ko me za su rasa sun yarda. Akwai wadansu sun yarda su kafa Kasar Biafra, yanzu haka ma ana karkashe su, duk sun sadaukar da rai, da dukiya da mutunci a kashe don Biafra ta tsaya.

"Idan muka ce za a kafa kasar Allah sai wani abu mai kama da wannan ya faru me ka yi asara a ciki? Ibada ka yi, Shahada ka yi. To yaya mai Oduduwa zai sadaukar da kansa da rayuwarsa ya kafa Oduduwa State, mai Biafra zai sadaukar da rayuwarsa ya kafa Biafra state, kai a matsayinka mai cewa La'ilaha illallah Muhammadur Rasulallah ba za ka iya sadaukarwa a kafa kasar Allah da Annabi ba!?  Wane irin maha'inci maciyin amana ne kai? Wane irin munafuki ne kai?

"To Malam Zakzaky kasar Allah yake so ya kafa bisa ga sadaukarwa. In dai masu Oduduwa da Biafra za su sadaukar da rai da dukiya, to musulmi almajiran Malam Zakzaky sun shirya su sadaukar da rai da dukiya domin kafa kasar Allah, kasar Musulunci! In ya so Bature ya mutu! Ran Bature ya baci, a kafa kasar Allah. "Inna ardhiy wasi'a fa'iyyaya fa'aboduon. Wama kalaqatil jinn Wal Insi illa liya'abodoun."

"Kai munafukin ina ne!? In Sarki ne kai sarkin munafukan ina ne!? In gwamna ne mai gwamnan munafukan wane gari ne? In shugaban kasa ne, kai wane shugaban kasar munafukai ne? Mai matacciyar zuciyar da ba abin da ke gabansa illa ka ci banza ka ci hofi ka tara tarkacen banza da hofi ka karata da 'diabetes' da ciwon zuciya da hawan jini, kila ma ka kurumce baka ji. 

"Kasar Allah Malam Zakzaky ke so ya tabbatar, ba bugu ba zagi. Kira yake yi, al'umma yake so ya samar sabuwa a cikin gurbatacciyar al'umma. Don dai zagi ba kyau amma wallahi da na yi. Da na ce dan uban mutum in ya isa ya hana! 'Astagfirullah', kuma Insha Allahu sai kun ga abin da zai bakanta muku rai!

"Muna rokon Allah, wannan bawan Allah da ya tsamo mu daga duhun jahilci ya dora mu a kan hanya ya saita mu, Allah ka saka masa da alkairi maras iyaka, ka kasance tare da shi, ka kara masa hakuri da juriya, ka bashi sabati da Istikama, ka nuna masa karshen makiyansa, ka cika masa burinsa, ka yi amfani da mu wajen dafa masa."

— Sheikh Yakubu Yahya Katsina a yayin jawabin Nisfu Sha'aban 1442H jiya Litini a Markaz din Katsina.

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky