KO KUN KARANTA CEWA; Mace Mutum Ce, Kuma Dai-Dai Ta Ke Da Namiji?...

KO KUN KARANTA CEWA; Mace Mutum Ce, Kuma Dai-Dai Ta Ke Da Namiji?...

Wani abu shi ne; Minene dalilin da ya sa aka ce mata su kauda ganinsu daga  maza? Mi yasa kuma aka ce maza su kauda ganinsu daga mata? “QUL LIL MUMINEENA YAGUDDU MIN ABSARIHEEM WA YA'ANFITU FURUJAHUM... WA QUL LIL MUMINATI YAGBIDHNA...” Mi yasa aka fadi wannan?.

Na (1) saboda duk lokacin da mutum ya kalli macen da ba tasa ba kuma ba tare da hijabi ba to sai wani juzu’i (bangare) na sha'awarsa ya tafi (cikin sha’awarsa 100 za a kasa a dauki wani bangare a watsar da shi. Idan ya zama shi ne al'adarsa to za a wayi gari ko matarsa ya gani ba ya sha’awarta, ko tazo kusa da shi bai jin komai.

Haka nan macen da ta saba ganin maza, su tsura ma maza ido, to ita ma za a wayi gari yau da gobe sha'awarta na tafiya, sha'awarta na tafiya za a wayi gari ko mijinta bata sha’awa. Akwai hikima cikin dokokin Allah, da tsarin Allah. 

To ba zamu biyewa ’yan duniya ba masu ganin cewa; ’yancin mata shi ne a saki mace tayi shigar da ta ga dama, mu muna da ’yanci na kashin kammu na farko ’Awwalus-Shai'i’ Mutuntaka, mace mutum ce, ’yanci na farko kenan. 

Mace mutum ce, kuma dai-dai ta ke da namiji. Idan namiji ya kuskura (Wa’iyazu billahi) ya kashe mace, shima kasheshi za a yi. Idan mace ta aje kudi a hirzi (abinda ake ce ma hirzi:- inda hannu ba ya kaiwa wajen sai an bi ta wasu hanyoyi, akwai sharuda wajan guda 17 na cikar sharuddan daukar abin wani) to wannan sharudan in ya cika cewa, ya dauke mata abu to dole a yanke masa hannu. Amma idan ita ta dauka ba za a  yanke mata ba saboda akwai shubuha cikin dukiyarsa (cikin dukiyarsa akwai abincinta a ciki) amma in shi ya sace mata aka gano shi ya dauka sai a yanke hannunsa kaga Mutum ce an bata wannan damar. (Amma ita ma kada ta dauki nasa din sai ta tambaya... Domin aikata hakan Ha’inci ne).

An bata damar ta fita yadda shara'a ta yarda, (1) ta fita da hijabi, (2) da sanin mijinta ko mahaifinta ko wani waliyyinta mai kula da ita (3) kuma a san inda zata. Wadannan sharuddan guda 3 in suka cika mace zata iya fita.

Tana da damar ta je neman Ilimi, tana da ’yancin ta je neman Ilimi, wane ’yanci kuma kuke so a ba mace banda wannan? 
-Tana da 'yancin mallakar dukiya, 
-Tana iya zama mai kudi. 
-Tana iya bude shago. 
-Tana iya zama a kanti. 
-Tana iya kafa rumfa a kasuwa tayi kasuwanci.
-Tana iya zuwa gona tayi aiki.
Zata iya zama direba.
-Zata iya zama direban jirgin kasa, da na sama da mota. Duk zata iya yi amma cikin kudud na shari'a, da kamewarta.

Kai babu wani aikin da Musulunci yace mace ba zata iya yin wannan aikin ba sai dai idan ya saba ma shari'a ko zai keta mutuncinta wannan shi ne abinda shari’a ta hana kooomi zata iya yi...”

- An yanko daga jawabin Shaikh Yakubu Yahya Katsina.

{Bin Yaqoub Katsina}

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky