Limamin Zamani Imam Mahadi (AJ)

LIMAMIN WANNAN ZAMANI; IMAM MAHDI (AJ)

Daga Saifullahi M. Kabir

Shine Imami na 12 kuma na karshe a jerin halifofin Manzon Allah shiryayyu goma sha biyu da Annabi (S) ya ce za su zo a bayansa.

Shaikh Mufid a cikin Al’irshad ya kawo cewa, wanda ya kasance Imami a bayan Imam Hasan Al’askari shine Imam Mahdi (AS), wani bai gaji Imam Askari ba face shi, ya kasance shekarunsa biyar a lokacin wafatin mahaifinsa, Allah (T) ya sanya shi mai hukunci tun yana ƙarami kamar yadda ya sanya ga Annabi Yahya tun yana dan karami. Sannan kuma Allah ya sanya (Imam Mahdi) ya zama Imami a yayin da yake karami (dan shekaru 5) kamar yadda ya sanya Annabi Isa Dan Maryam ya zama Annabi tun yana tsumman goyo a jariri. Ruwayoyi daga Manzon Allah da Amirulmuminin da sauran A’imma Tsarkaka (AS) sun zo dangane da al’amarinshi. Shi ne ma’abocin takobi, tsayayye, wanda ake sauraro.

Bayan haihuwar Imam Mahdi (AJ) ya shiga Ghaiba guda biyu, na farko mare tsawo, sannan bayan ita ya shiga mai tsawo wacce ya shafe shekaru fiye da dubu a cikinta zuwa yanzu, kuma Allah (T) ya yi alkawarin bayyanarsa a lokacin da ya so a harshen Annabinsa Muhammad (S), kamar yadda ruwaya ta zo a littafai da dama, daga ciki akwai Musnad din Ahmad, Zaka’iru Ukba na Dabari, Fara’idus Simdain na Alhamiyuni da sauransu cewa;

Manzon Allah (S) yace: “Allah Ta’ala ba zai gusar da ranaku da darare ba har sai ya tayar da wani mutum daga Iyalan gidana, sunansa zai dace da sunana, wanda zai shimfida kasa da adalci da daidaito bayan (ko kamar) yadda ta cika da zalunci da danniya.”

Me littafin Kashful Gumma, ya kawo ruwaya daga Zurarata yace, Na ji Abu Jafar (AS) yana cewa: “Imamai goma sha biyu ne dukkansu daga iyalan Muhammad (S), Aliyu Dan Abudalib da mutum goma sha daya daga yayansa na tsatso.”

Wata rana wani sahabin Imam Askari (AS) mai suna Abu Hashim Aljafari ya tambaye shi cewa, jin nauyinka ya sa na ji nauyin na tambaye ka, shin ka min izini na tambayeka? Sai Imam yace masa ya yi tambayar. Sai yace masa Ya Shugabana shin kana da magaji (da)? Imam yace masa Eh. Sai Aljafariy yace wani abu ya faru a bayanka a ina za mu ganshi mu tambaye shi? Imam yace masa a cikin wannan garin nan (Samarra).

An haifi AbulQaseem Imam Muhammad AlHujja dan Imam Hasan Askari ne a asirce a asubahin daren tsakiyar Sha’aban (Nisf Sha’aban) a shekara ta 255 bayan Hijira. 

Sunansa Imam Muhammad Al-Mahdi (AS) dan Imam Hasan dan Imam Ali Alhadi, dan Imam Muhammad Jawad, dan Imam Ali Arridha, dan Imam Musal Kazeem, dan Imam Jafarus Sadiq, dan Imam Muhammad Baqir, dan Imam Aliyu Zainul Abidin, dan Imam Husaini, dan Imam Ali dan Abidalib Amincin Allah ya tabbata a gare su baki dayansu.

Mahaifiyarsa kuwa ita ce Sayyida Narjees. 

Ana ma Sahibuz Zaman, Imam Mahdi Al-Hujja al-Qa’im Al-Muntazar, alkunya da irin alkunyar Kakansa Manzon Allah (S) wato Abul Kasim (AS).

A wani Hadisi da Abu Dauwa ya ruwaito a Sunan dinsa, Hadisi na 4283, Manzon Allah (S) yana cewa: “Da duniya za ta kasance sauran kwana daya ta tashi, Allah zai tsawaita wannan ranar har sai ya bayyanar da wani mutum daga iyalan gidana wanda zai cika duniya da adalci bayan ta cika da zalunci.”

A hadisi nag aba, wato na 4284 a Sunani Abu Dawuda sai ya kawo ruwaya daga Manzon Allah (S) yana cewa “Mahdi daga tsatsona yake, daga ‘ya’yan Fatima.”

Don mu san ko wane ne wannan mutumin da Allah zai bayyanar. Sai Abu Dawuda ya kawo ruwaya a hadisi na 4285 daga Manzon Allah (S) yace: “Al-Mahdi daga tsatsona yake, zai kasance mai fadin goshi da dogon hanci (kinaya ga kyau), zai cika duniya da adalci da daidaito kamar yadda ta cika da zalunci da danniya. Zai yi mulki na tsawon shekaru bakwai.”

Ka ga in ma muna tunanin shin wane ne wannan mutumin da zai zo daga tsatson Annabi wanda zai cika duniya da adalci bayan ta cika da zalunci, to ba kowa bane face Imam Mahdi (AS), wanda aka haife shi a irin wannan lokaci na tsakiyar watan Sha’aban a shekara ta 255 bayan hijira.

Wannan shugaba namu, wanda kamar yadda Ibn Shirawaih al-Dilami ya kawo ruwaya a littafinsa ‘Al-Firdaus’ da sanadinsa daga Abdullahi Ibn Abbas (RA) cewa, Manzon Allah (s) yace: “Al-Mahdi shine Dawisun mutanen Aljanna.”

A wata ruwaya kamar yadda mai littafin Fusulul Muhimma ya nakalto a shafi na 455, Daga Huzaifatul Yamani (RA) yace, Manzon Allah (S) yace: “Al-Mahdi da na ne, fuskarsa na haske kamar wata, launinsa irin launin Larabawa ne, jikinsa kuma irin na Isra’ilawa, zai cika kasa da adalci kamar yadda ta cika da zalunci, mutanen sammai da kassai da tsuntsayen da ke sararin samaniya duk za su yarda da halifancinsa, zai yi mulki na tsawon shekaru 10 (ko 20 a wata ruwayar)”

Akwai kuma sanannen Hadisi a Sahihul Bukhari da Muslim da Musnadin Ahmad da wasunsu daga Abu Hurairata yace, Manzon Allah (s) yace: “Ya za ku kasance idan kuka wayi gari kuka ga Isa Dan Maryam a cikinku, kuma Imaminku na daga cikinku.”

Ma’ana, za a wayi gari Annabi Isa (AS) zai dawo duniya a wannan zamanin na Manzon Allah (S), kuma ko ya dawo din zai kasance akwai Halifan Manzon Allah wanda shi zai kasance Limamin Musulmi baki daya shi ma Isa din zai zama a karkashinsa ne.

A Hadisin da Ibn Maja ya ruwaito a Sunan dinsa, da Hakim a Mustadraku da wasunsu, Manzon Allah (s) yana cewa: “Mu ne ‘ya’yan Abdulmudalab shugabanni a Aljanna, Ni da Hamza da Jafar da Ali da Hasan da Husaini da Mahdi.”

Amincin Allah ga shugabanmu Imam Mahdi (AS). Allah Ya sanya mu cikin mabiyansa.

Insha Allah za mu cigaba.

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky