Ranar:28 November, 1989 (30 Rabius Thani, 1410H)
Ranar:
A wannan ranar ne Shaikh Ibraheem Zakzaky ya fito daga kurkukun Fatakwal na kamun wakiar Kafancan, wanda Janaral Babangida ya yi masa.
Dama an kama Shaikh din ne a ranar 28 ga watan Maris 1987, sannan kuma aka yanke masa hukuncin dauri a ranar 28 ga Nuwambar 1987 din, don haka bayan shekara biyu cur da daure shi a ranar 28 ga Nuwambar 1989 aka sake shi.
Shaikh Zakzaky ya fito bayan ya shafe shekaru biyu da wata takwas a tsare kenan. Kuma yana wannan kurkukun ne aka haifa masa yarsa ta biyu mai suna Nusaiba.
— Daga littafin *Muhimman raneku 400 a Tarihin Harkar Musulunci*, na Cibiyar Wallafa.
Comments
Post a Comment