Sabunta Muzaharorin 'Free Zakzaky' A Nijeriya: Yadda Muzaharar 5 ga Maris 2021 Ta Zo Da Sabon Salo A Da'irar Katsina.

Daga Auwal Isa Musa.

Kamar sauraran takwarorinta, Da'irar Katsina ita ma ta bi sahunsu wajen gudanar da jerin gwanon #Freezakzaky a ranar Juma'ar nan 21 ga Rajab, 1442 H (5 ga Maris, 2021), Muzaharar wadda aka gudanar a fadin Kasar baki daya.

Muzaharar ta Katsina wadda ta motsa a lokaci guda da misalin karfe 3:00 na rana, ta samu halartar daruruwan 'Yan uwa Musulmi daga sassa daban-daban na Da'irar.

Wani sabon salon da Muzaharar ta zo da shi a wannan karon shi ne, yadda aka kalkasa ta zuwa Yankuna  guda Hudu (Zones) na Da'irar, wato Yankin Gabas, Yankin Yamma, Yankin Arewa da Kuma Yankin Kudu, tayadda kowanne Yanki ya gudanar da tashi Muzaharar a lokaci guda da salon da ya dace, aka tashi a inda ya dace, kuma aka tuke ta a inda ya dace.

Yankunan masu sunaye kamar haka: Zone 'A', Zone 'B', Zone 'C' da kuma Zone 'D', salon yadda kowannensu ya gudanar da tasa Muzaharar ya bada Natija, domin ta isar da sako ba kadan ba.

Yankin Gabas wato 'Zone 'A', sun taso ne da Kofar Dur6i inda suka tuke ta a Kasuwar Gwangwan.

Yakin Yamma kuwa wato Zone 'C', su kuma sun taso da tasu Muzaharar ne daga Kofar 'Yandaka, inda suka tuke ta a Sabon Titin 'Yankyaure.

A yayin da Yankin Arewa suka taso da tasu Muzaharar daga Unguwar Iyatanchi suka tuketa Tsohuwar Stadium, kan Titin Saulawa.

Sai kuma Yankin Kudu wato Zone 'D' wadanda suka taso da tasu Muzaharar daga Danhako (farin Masallaci) Kofar Kaura, inda suka tuke ta a Sha-tale-talen Titin Sabon layi.

A yayin gudanar da wadannan Muhazori na #Freezakzaky wadda aka kalkasa zuwa 6angarorin hudu, 'yan uwa Musulmi na tafiya ne cikin tsari tare da rera wakoki 'FreeZakzaky'da take na musamman, inda suke dauke da kwalaye masu rubutun 'Free Zakzaky' a jikinsu da Hotunan jagora Sayyeed Ibraheem Zakzaky(H), a yayin da saukin Kabarbari masu razana makiya Allah ke dagawa sama, a lokaci guda kuma Matasa Maza da Mata Yara da Kanana cikin kakkausar Murya ke kara jan kunnen gwamnatin Buhari da cewa lallai fa ta bi umurnin Kotu ta saki Shaikh Alzakzaky da Mai dakinsa Malam Zeenatu ba tare da wani sharadi ba wadanda take tsare da su shekara da shekaru ba bisa Zalinci, tsarewar da za ta ja wa gwamnayin yin Nadama da yin da-na-sani muddin suka ci gaba da yin ta.

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky