Shaikh Yakubu Yahaya Katsina Ya Cika Shekaru 66: Yadda Aka Gudanar Da Taron Ranar Zagayowar Haihuwarsa A Bana.
Daga Auwal Isa Musa.
A ranar Lahadin wannan Makon ne 16 ga Rajab, 1442 H (1 ga Maris, 2021 M) Iyalan Shaikh Yakubu Yahaya hadin guiwa da wani Kwamiti na shirya taron ranar haihuwarsa, suka shirya taron zagayoran ranar haihuwar Malamin, Malamin wanda yake cika shekaru 66 cif duniya.
Taron wanda farko ya soma gudana a zangon farko da misalin karfe 4:00 na Yammacin ranar da kuma zango na biyu wanda shi kuma ya gudana da misalin karfe 8:00 daren ranar (Majalisin Mawaka), ya samu halartar dimbin jama'a na ciki da na wajen Da'irar ta Katsina har ma da sassa daban-daban na wasu Da'irorin Kasar nan.
'Yan uwa na jini da na Addini (a cikin harka da wajen ta), Abokai, Makwafta, Abokan arzuka na Shehin Malamin duk sun halarci taron, inda wasu daga cikinsu suka gabatar da jawabai a taron dangane da tarayyarsu da Shehin Malamin tun tale-talen shekaru masu yawa da suka gabata a baya.
Malam Husaini, abokin Malamin ne tun na Kuruciya, ya kuma gabatar da jawabi a kan jajircewar Malamin wajen jure daukar nauyin da Allah ya aza ma sa na wa'azantarwa tun yana Saurayi.
"Wannan nauyi da Allah ya ba shi, ya san yana iyawa. Duk abin da Allah ya ba ka, ya san kana iyawa. Idan da mu aka ba, kila da yanzu ba mu nan duniya."
Alhaji Ghali, yayan Shaikh Yakubu Yahaya ne, shi kuma ya yi jawabi ne a kan abin da ya sani na baiwar da Allah ya yi wa Malamin da sika taso gida daya tun Yarintarsa, inda ya bada wasu Misalai dangane da haka.
"Tun da Allah ya sa ya tashi, Mutum ne mai baiwa wanda Allah ya yi ma shi baiwa mai yawa. Da yawa za mu yi tafiya da shi, wasu al'amurra na mamaki wadanda yake abubuwan da ba sa da iya su yi ta faruwa..."
Malam Mansur, shi kuma abokin tafiye-tafiyen Malamin ne a Harka. Ya tofa albarkacin bakinsa, inda ya ce wannan muhallin taron, ba wajen fayyace abubuwan da ya sani ba ne dangane da Malamin.
"Muna tafiye-tafiye da su Malam bakin gwargwado, amma nan ba wajen in bayyana abubuwan da suka faru ba ne. Su ma ma su shirya taron nan sun san haka. Fatanmu Allah (T) ya kar6i dan abin da muka yi, kada kusanci ya 6ata ayyukanmu."
Alhaji Yahaya, Makwafci ne a unguwar da Malamin ne yake zaune yanzu haka. Shi kuma ya bada shaida ne a kan irin zaman lafiyar da suke yi da Malamin da sauran 'yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky(H) a Unguwar.
"An gayyace ni in yi bayani a mamadin 'yan Unguwa. Ba abin da zan ce sai dai godiya. Allah Ubangiji ya kara ma shi lafiya da daukaka. Yana da son jama'a (Malam Yakubu). Mu 'yan Unguwa muna nan muna ta kokari mu zauna da Juna... Allah ubangiji ya kara ba mu zaman lafiya, Allah kuma ya ceto mana shugabanmu! Allah ya ceto mana shugabanmu!! Allah ya ceto mana shugabanmu(Malam Zakzaky) domin darajar Annabi Muhammadu!!!"
Daga cikin 'yan Darikar Kadiriyya mazauna Unguwar, wani da ake kira Injiniya, shi ma ya halarci taron, ya kuma yi jawabi a kan yadda Malamin ke kula da al'amarinsu da kuma wanzar da zumunci a tsakanin juna. Ya kuma yi bayani a kan dabi'un girma da Malam Yakubu Yahaya yake da su.
"Magana a kan dabi'u na su Malam sai dai in ce an tawaye. Iya zaman da mu ka yi a wannan Unguwa mun zama 'yan uwa ga Malam. Dukkan abubuwanmu a matsayinmu na Kadirawa na wannan Unguwa ko na wannan Gari, akwai nauyin da sai dai mu ji Malam ya dauke mana. Malam baya ne, goya marayu. Mun zama daya. Nan gidanmu ne." Inji shi
Injiniyan ya ci gaba da cewa "Gaskiya, maganar kaskantar da Kai, maganar Kyauta, maganar Hakuri to duk Allah ya sa ya kwaikwayi Manzon Allah ne a ciki. Shiyasa za ku ga bai da matsala da 'yan Unguwa, bai da matsala da Samarin Unguwa, bai da matsala da Malaman Unguwa!" Ya karkare.
Ta nashi 6angaren, a lokacin da yake maida jawabin godiya, Shaikh Yakubu Yahaya, ya yi godiya da jinjina ga wadanda suka shirya wannan taro a garesa, sannan kuma ya yi wa kowa fatan alkhairi.
A cikin jawaban da ya gatar, shehin Malamin, ya bayyana wadannan shekaru da ya yi a rayuwarsa a matsayin wata kyauta da Allah ya yi ma sa wadda bai yi ma wasu ba duk da cewa ba don ya cancanci hakan daga wajen Allah ba, kawai dai ganin damar Allah ne wanda shi kuma ya san dalilin yin haka, domin akwai wadanda tuni sun rika shi tafiya gidan gaskiya amma shi Allah yake ta sake ranta ma sa wasu shekarun.
Malam Yakubu Yahaya ya kuma bayyana wasu hadarurraka da ya tsallake a baya da ma na baya-bayan nan wanda da ba don kiyayewar Allah ba da yanzu wani zance ake yi daban ba wannan ba, inda ya bayyana hakan a matsayin wani tagomashi ne da Allah ya yi ma sa a rayuwa.
Daga karshe Malamin ya bayyana wani babban tagomashi wanda ya fi dukkan wadanda ya zayyano da Allah ya yi ma sa a rayuwa, wato yadda Allah ya hada shi da jagoran shiriya, Sayyeed Ibraheem Zakzaky(H), inda rayuwarsa ta inganta da samun shi wanda kuma shi ne tsirarsa a ranar gobe Kiyama.
"...Sai kuma Allah ya hada Ni da Jagora. Allah yana cewa, 'Walan tajida lahu waliyyan murshida...' akwai wanda za ka ga shi ba wanda ya ji6inci lamarinsa, ballantana ya sa shi hanya. Ni, sai Allah ya hore ma ni wanda ya ji6inci lamarina, ya sa Ni hanya; shi ne Assayyeed Ibraheem Zakzaky(H), wanda yake da mu Masoya da ma Makiya; mun tabbatar da cewa abin da yake kira shi ne daidai, kuma shi ne a kan hanya."
Haka nan kuma dai a yayin taron, an saurari jawabin Jagora Shaikh Ibraheem Yaqoub Alzakzaky(H) a kan "Wanene Shaikh Yakubu Yahaya", jawabin Jagoran ya gabatar a waki'ar 19th Aprilu mai taken "Jan kunnen Madaki" inda kowa ya saurare shi ta 'Audio'.
Taron 'Birthday' din dai ya samu halartar Yara da Manya, Malamai da Dalibai, Tsaffi da Matasa, Maza da Mata, Mawaka da Marubuta da sauransu.
Daga cikin Manya bakin da suka halarci taron akwai Malam Husaini (Abokinsa), Alhaji Ghali (Yayansa), Alhaji Yahaya (Makwafcinsa) da sauransu.
Comments
Post a Comment