Sheikh Zakzaky a Shekuru 70

SHAIKH ZAKZAKY A SHEKARU 70

Daga Saifullahi M. Kabir
Kimanin shekaru 220, lokacin jihadin Shehu Usman Dan Fodiyo (RH) kakannin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), suka dungumo suka zo kasar Hausa don su taimakawa wannan Mujaddadin na zamaninsu wajen kokarin tabbatar da addinin Musulunci a nahiyar yammaci.

A wancan lokacin, kakan Shaikh Ibraheem Zakzaky na uku, mai suna Liman Husaini, wanda yake daya ne daga cikin Sharifan da ake kira Idrisiyyawa, tsatson Imam Hasanul Mujtaba (AS) ta hanyar Nafsuz-Zakiyya wadanda Umayyawa da Abbasiyawa da ma Wahabiyawa daga baya suka rabo kakanni da iyayensu daga yankin Larabawa suka fantsama zuwa sassan duniya, Allah ya kaddara zamansu a garin Shingidi da ke tsohuwar daular Mali ta da.

Garin Shingidi, wanda yanzu an ce yana cikin Murtaniya ne, amma a da can duk kasashen suna karkashin wannan tsohuwar daula ta Malin da, wannan kakan na Shaikh Zakzaky ya kasance babban limaminsa. 

Bayan sun baro garin Shingidi, sun rika zama a wasu garuruwa daban-daban, daga ciki akwai wani gari da ake kira Mabruk, sannan suka zauni garin Tumbuktu da ke Malin yanzu, daga nan ne suka dungumo zuwa kasar Hausa domin su taimaki jihadin da Shehu Usman Danfodiyo ke jagoranta.

Bayan samun nasarar jihadin Shehu Danfodiye, sai ya tura Malam Musa Bamalli don ya zama Amir din mutanen Zazzau, wanda cikin tawagar da Shehu ya tura ne akwai wannan kakan na Shaikh Zakzaky, wato Liman Husaini. Inda bayan isowarsu Zazzau a karshen shekarar 1804, Liman Husaini a matsayinsa na mahaddacin Alkur’ani kuma Malamin addinin Musulunci, kawai sai ya cigaba da karantar da Alkur’anin.

Bayan Allah ya wa Amir din Shehu na Zazzau, wato Malam Musa Bamalli rasuwa a shekarar 1821, bayan ya yi Amirancin kimanin shekaru 17 kenan, ba a jima ba sai Liman Husaini ya bar Zariya inda ya koma Mali, komawar da bai dawo ba, sai Dansa ne Sharif Muhammad Tajuddeen ya dawo Zazzau a wajajen shekarar 1853, bayan da Mulkin Zazzau ya koma hannun ‘Dan Malam Musa din, mai suna Malam Abdulkadir Dan Musa (Sarkin Zazzau Sidi).

Sarki Sidi Abdulkadir bai ko shekara a kan karagar mulki ba, sakamakon wasu rigingimu da suka auku a lokacinsa wanda ya ja za aka cire shi a kan karagar mulkin a lokacin kamar yadda tarihi ya sajjala. Sai dais hi Sharif Tajuddeen ko da ya zo sai ya zauna a wani kauye da ke kusa da Zariya din wanda ake kira Likoro. Nan ya rayu har Allah ya masa rasuwa, kabarinsa na nan a gidansa da ke garin Likoro din.

An ce a lokacin da Sharif Tajuddeen yaruka biyu ya iya, Fulatanci da Larabci, Hausarsa kadan ce har ya koma ga Allah, da yake shima Mahaddacin Alkur’ani ne, ya kafa tsangayar Alkur’ani a gidansa inda ya rika karantarwa har karshen rayuwarsa.

Bayan ya auri wata baiwar Allah, Bafullatana ‘yar kasar Bauchi mai suna A’isha, Allah ya azurta Sharif Tajuddeen da ‘ya’ya biyar da ita; Abdulkadir (wanda ake kira Sidi), Yaqoub (wanda ake kira Kwasau), Zubairu, Muhammad da kuma Ali.

Ali shine kakan Shaikh Ibraheem Zakzaky, wato mahaifin baban Malam (H), wanda kasancewarsa ya taso a gidan mahaddatan Alkur’ani ne, shima ya riki karatun Alkur’ani din, har ma ya tafi yankin Gabas (ana cewa Borno), inda ya haddace Alkur’ani ya cigaba da karantar da shi ga almajiransa, bai dawo Zazzau ba sai da labarin rasuwar mahaifinsu Malam Tajuddeen ya riske shi sannan ya zo don yin ta’aziyya.

Dawowar Malam Ali kasar Zazzau ta dace da lokacin mulki ya dawo hannun jikan Malam Musa, wato Sarki Ali Dan Sidi Abdulkadir. Da yake akwai dangantaka da zumunci mai karfi a tsakanin gidan na kakannin Shaikh Zakzaky da gidan Malam Musa Bamalli, don haka sai Sarki Ali Dan Sidi, ya nemi da Malam Ali Dan Tajuddeen ya zauna a Zazzau ba tare da ya koma ba, ya bashi makaranta da nufin ya koyar, amma sai ya zama ya zabi ya koyar da yayan gidansu kawai da kuma wasu daga yayan gidan Sarkin.

Sarki Ali Dan Sidi sai ya ba Malam Ali Dan Tajudden auren wata baiwar Allah, Malama mai suna Hajara (wacce tsaban karatunta ake kiranta da Mai Karatu). Da wannan baiwar Allah din ne Allah ya azurta su da samun ‘ya’ya hudu, uku mata; Halima (Guggon Zango), Haajara, Fatima, sannan sai namiji guda daya auta, shine Yaqoub (wanda ake cewa Magaji).

Malam Yaqoub, kamar sauran mahaifansa, shima ya taso ne da karatun Alkur’ani da kuma noma a matsayin hanyar tafiyar rayuwa. Allah ya azurta shi shima da haddar Alkur’ani mai girma, sai dai shi bai karantar da sauran mutane ba in banda ‘ya’yansa na cikinsa.

Shima ya auri mata, daga cikin matansa akwai wacce ake kira da Fulatanci da Hari Jamo, wacce ta Haifa masa ‘ya’ya 11; Zubairu, Abdulkadir, Maryam (Mairo), Fatima (Binta), Ibraheem (Zakzaky), Badamasi, Basiru, Halima, Abubakar, Yahya, Maimuna. Wasu daga yaran sun rasu tun suna kanana, kamar Halima, ta rasu tun bata fi shekaru biyu da haihuwa ba.

Ibraheem (Zakzaky) shine da na biyar a wajen mahaifansa biyu; Malam Yaqoub da Malama Hari ‘Yar Malam Jamo. An ce asalin sunanta Saliha ce, sai ake kiranta Hari da Fulatanci. Sannan sunan babanta Muhammad Mustapha, amma ana kiransa da Jamo. Kuma su ma asalinsu Toronkawa ne da suka zo daga Mali bayan da Malam Musa Bamalli ya auri ‘yar uwarsu. Don haka kakanta sunansa Malam Abdulkadir (shima ana ce masa Sidi, da yake a da duk mai suna Abdulkadir a kan masa lakabi da Sidi saboda sunan Sidi Abdulkadir Jilani (RA).

A asubahin rana mai kamar yau, 15 ga Sha’aban 1372H Allah Ta’ala ya azurta Malam Yaqoub da Malama Saliha da samun jariri ma’abocin haiba da kwarjini, lafiyayye ma’abocin hasken shiriya, wanda aka radawa suna Ibraheem (Shaikh Zakzaky). 

Yau ne mahaifin ‘ya’ya tara, baban shahidai shida, wanda ya shafe shekaru kusan 15 na rayuwarsa ana tsare shi a kurkuku saboda addinin Allah, mai da’awar a komawa tsarin Allah, dalilin shiriyar miliyoyin al’umma zuwa ga riko da sahihin addini, Shaikh Ibraheem Zakzaky ke cika shekaru 70 cur da haihuwa a kidayar Hijiriyya. 

Allah Ya kara lafiya, juriya, tsawon kwana, imani, hakuri da dakewa da biyayyar Allah (T) Abbah! Allah Ya gaggauta kubutarka daga hannun azzalumai. Ya maka sakayya a kan su. Allah ya tabbatar da mu a bayanka har karshen rayuwarmu.

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky