TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Saura Kwanaki 15 Shaikh Zakzaky Ya Cika Shekaru 70
-Saifullahi M. Kabir

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Ranar Talata 15 ga Sha’aban, 1372 aka haifi Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), a unguwar Kwarbai da ke birnin Zariya ta jihar Kaduna.

Mahaifinsa shine Malam Yaqoub dan Malam Ali dan Sharif Tajuddeen, shi kuma dan wani babban limami da ake kiransa da Liman Husaini. Kakan Shaikh Zakzaky na uku ya kasance daga cikin mutanen Shaikh Usman Danfodiye, wadanda ya tura su garuruwa a matsayin wakilansa, sai ya zama shi Malam Muhammad Tajuddeen Shaikh Danfodiye ya turo shi Lardin Zazzau ne a matsayin mai ba Amir din Zazzau, Malam Musa shawara da taimakonsa wajen tafiyar da harkokin al’umma akan tsarin Musulunci.

A wata hira da aka yi da Shaikh Zakzaky dangane da tarihin rayuwarsa a shekarun baya, ya bayyana cewa: “Mahaifina Malamin Alkur’ani ne, haka ma kakana shima Malamin Alkur’ani ne, haka ma uban kaka na. Sai dai shi uban kakana da kakana a lokaci guda suna karantar da karatun littafi baya ga karantar da Alkur’ani, amma duk cikansu mahaddata Alkur’ani ne, kuma kwararru a bangaren karanta shi. Har ila yau su kan hada da yin noma a matsayin hanyar rayuwa, baya ga koyar da karatun Alkur’ani.”

Shaikh Zakzaky yace: “Haka ita ma mahaifiya ta bangaren gidansu suma Malamai din ne. Da yake a tsarin rayuwa a wajenmu a da kusan abu kowanne gida da abin da suke yi, akwai wanda suke Sarakai ne, akwai wanda suke Malamai ne akwai ‘yan Kasuwa da sauransu. Amma ni ta bangaren uwa da uba dukkansu suna bangaren abin da ya shafi Malunta ne. Eh, akwai dangantaka da Sarakai, iyayenmu su suka rika koyar da nasu iyayen, tafiya din kamar tare ake yi, illa iyaka kowanne da abin da yake kai.”

Dangane da asalin Shaikh Zakzaky, har ila yau, ya fadi cewa: “Asalin iyayenmu sun fito ne daga Magrib, Maroko kenan na wanan lokacin, ‘Khususan’ ma daga wani birni wanda ake ce mishi Shingidi, wanda yanzu yana cikin Murtaniya ne. amma a wancan lokacin (da suka taso) babu Murtaniya, Shingidi din ake ce masa, kuma sun tashi daga sassa zuwa sassa, har suka zauna a Mali ta da, kuma daga nan suka zo nan. Ana cewa su suna daga cikin tsatson Imam Hasanul Mujtaba (AS) wanda suka zauni wannan kasar ta Magrib, suka gangaro suka yi Mali, suka fado nan.”

Yayin da muke zantawa da kani kuma shakikin Shaikh Zakzaky, Sayyid Badamasi Yaqoub ya kara bayani a kan tasowar Shaikh Zakzaky da cewa: “Ya taso a gaban mahaifinsa ya fara karatun Alkur’ani a gabansa, a lokaci guda kuma, Mahaifin nasa ya tura shi wasu makarantu wanda suka hada da makarantar sarkin Ladanan Zazzau, da makarantar Malam Sani Abdulkadir, ta yadda idan da safe zuwa yamma Malam ya je Makarantar sarkin Ladanai, da daddare kuma sai ya je makarantar Malam Sani Abdulkadir.”

Malam Badamasi ya kara da cewa: “Mahaifinmu bai saka mutum a gona sai ka yi karatu, lokacin da su Malam suka kai wani mataki na fahimtar karatu sai aka saka shi a aikin gona, sai ya zama Malam ya taso a gaban mahaifinsa da abu biyu ne; yin karatu da kuma aikin noma.”

Yace: “Kasantuwar shi Malam Allah (T) ya mishi wani hazaka na daban, gaskiyar magana Allah ya kaddara shi Malam haziki ne, domin a cikinmu ba haziki kamarsa, domin kuwa akwai yayyinsa wadanda suka grime shi, kuma sukai nesa da shi a karatu, amma abin mamaki shi yake tuna musu karatu idan sun manta. A lokacin da ake biya musu shi nan take yake dauke karatun, saboda haka zai iya biya musu karatun da aka musu idan suka manta.

“Bayan Malam ya sauke Alkur’ani, ya shiga karatun Littatafai, ya yi karatun littatafai a wajen mutane daban-daban. Amma a takaice daga cikin Malamansa na littafi a Zariya akwai Malam Sani Abdulkadir, Malam Sani Na’ibin Zazzau, Malam Isa na Madaka, Malam Ibrahim na Kakaki, akalla ya yi karatu a wajen wadannan a nan Zariya.

“A Kano kuwa ya zama yana karatu a wajen Malamai daban-daban, zan iya tunawa ya yi karatun littafai a wajen wani da ake ce masa Malam Nuhu limamin Yola, wanda (Yola din) wata unguwa ce a cikin Kano, sannan ya yi karatu a wajen Malam Isa Waziri, da kuma wajen Malam Nasiru Kabara.”

Sayyid Badamasi yace: “Za mu iya cewa, ba wani littafi da ake karanta shi a zaure na mazhabar Malikiyya wanda Malam (Zakzaky) bai karanta ba. Babu wannan littafin. Tun daga littafan Fikihu da suka fara da Kawa’idi, Ahalari har zuwa Muktasar. Haka ma Tafsiri tun yana karami ya sauke Jalalaini, ya karanta shi a wajen Malamai daban-daban, daga ciki akwai Malam Sani Na’ibi. Baya ga wannan kuma babu wani littafi na Luggar Larabci wanda su Malam ba su karanta shi ba. Bayan Shu’ara sun karanta Muqama, sun yi Nahawu. Kai babu wani littafi wanda ake karanta shi a zaure face su Malam sun karane shi a gaban Malamai.”

Bincike ya tabbatar da cewa Shaikh Zakzaky ya karanta fannoni daban-daban na Luga, Nahawu da Sarfu, Fiqihu da Tafsirin Alkur’ani da sauransu. Tun bai fi shekaru 20 da haihuwa ba ya karance littafan da ake karanta su a zaurukan ilimi irinsu Ajuruma, Murha, Saja’i, Alfiyan Danmaliki, da wasu littafan da suka shafi Luggan Larabci kamar Ishiriniya, Witiriya, Ashariya har ma da Makamatul Hariri da Shu’ara’ul Jahiliyya. Haka ma a bangaren Fiqihun Malikiyya, Shaikh ya kai ma sauke har Muktasar a wannan lokacin.

— Daga littafin Muhimman Ranaku 200 a Tarihin Harkar Musulunci. Na Cibiyar Wallafa

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky