TAKAITACCEN TARIHIN ABUL FADALUL ABBAS; BABBAN GWARZO, JURUMI, DAN SADAUKI IMAM ALI(AS). KANIN IMAM HASAN(A.S) DA HUSAIN(AS):

A ruwayar da ya fi shahara, an haifi Sayyid Abul Fadhl al-Abbas ne a garin Madina, a ranar 4 ga watan Sha’aban, shekara ta 26 bayan hijirar Annabi Muhammad(saw).

Mahaifinsa dai shi ne Imam Ali Ibn Abi Talib(as), mahaifiyarsa kuwa ita ce Fatima bint Hazam bn Khalid bn Rabi’ ibn Amir Kalbi wacce aka fi sani da Ummul Banin, wacce ta fito daga kabilar Kilah, daya daga cikin mafiya daukakan daga cikin Bani Hashim da aka sansu da jaruntaka a fagen fama.

Lokacin da labarin haihuwarsa ya kai ga mahaifinsa Imam Ali(as), Imam(as) ya yi sujada don nuna godiyarsa ga Allah Madaukakin Sarki. Bayan kwanaki bakwai da haihuwar, kamar yadda sunna ta tanadar Imam Ali(as) ya sanya wa wannan jariri suna Abbas.

Tarihi ya tabbatar da cewa bayan shahadar Fatima al-Zahra(as), Imam Ali(as) ya bukaci dan’uwansa Akil da ya zaba masa wata mace wacce ta fito daga gidan ma’abuta jaruntaka don ya aura, don haka Akil ya zaba masa Fatima bint Hazam (Ummul Banin) don ya aure ta, haka kuwa lamarin ya kasance inda ya aure ta, Allah kuma Ya arzurta su da ‘ya’ya hudu maza, wato Abbas, Abdullah, Ja’afar da Usman, wadanda dukkansu sun yi shahada a Karbala wajen taimakon Musulunci da kuma dan’uwansu Imam Husain(as). An ce dalilin da ya sa Imam Ali(as) ya bukaci a sama masa macen da ta fito daga gidan ma’abuta jaruntaka shi ne don ta haifa masa da namiji wanda zai taimaki dansa Husain(as) a nan gaba yayin da zai kasance shi kadai cikin makiya a Karbala.

Ummul Banin dai ta kasance mai nuna tsananin kauna ga ‘ya’yan Fatima Hasan da Husain(as) ta yadda tun farko-farkon shigowarta gidan Ali(as) ta bayyana musu cewar ita baiwarsu don haka tana fatan za su karbi wannan bukata tata, hakan kuwa ta ci gaba hatta bayan haihuwar ‘ya’yanta. Har ila yau ta kasance mai mika wuya da bin Iyalan Gidan Manzon Allah (s) sau da kafa, musamman Imam Husain (a.s) wanda ta kasance tana sonsa fiye da ‘ya’yanta, ta yadda hatta lokacin da labarin shahadar ‘ya’yanta a Karbala ba ta damu ba, abin da ke fita a bakinta kawai shi ne ‘ina dana Husain ya ke’.

Abul Fadhl al-Abbas ya kasance kyakkyawan mutum ne don haka ne ma ake kiransa da sunan Qamar Bani Hashim (Watan Bani Hashim) saboda kyaun da Allah Ya yi masa, ga shi kuma jarumi, mai juriya, mai hakuri da kuma imani da Allah.
Kamar yadda aka saba, Abbas ya tashi ne karkashin kulawar mahaifinsa Ali (a.s) har na tsawon shekaru 14, wato har zuwa lokacin da mahaifin nasa ya yi shahada.

Daya daga cikin burin Imam Ali (a.s) shi ne wannan da nasa da ya sanya masa suna Abbas zai tashi ya kasance wa dan’uwansa Imam Husain (a.s) kamar yadda shi ya kasance ga Manzon Allah (s), wato dan’uwana kuma mabiya mai bi sau da kafa kana kuma garkuwa mai kare Ma’aiki daga dukkan wani sharri, saboda masaniyyar da yake da ita, kamar yadda Manzon Allah (s) ya sanar da shi, na abin da zai samu dansa Husain a Karbala. Daga nan kuma sai kulawarsa ta koma hannun dan’uwansa Imam Hasan al-Mujtaba (a.s) har na tsawon shekaru goma, sauran shekaru goma na rayuwarsa kuma karkashin dan’uwansa kuma shugabansa Husain (a.s). Don haka ba abin mamaki ba ne idan aka ga Abul Fadhl al-Abbas da halaye na kwarai da madalla, da suka hada da kwarjini, ban tsoro (ga makiya), karfin gwuiwa, jaruntaka da fuskantar makiya babu tsoro ba ja da baya da ya gada daga wajen mahaifinsa Ali (a.s), hakuri da juriya da ya gada a wajen dan’uwansa Hasan (a.s), da kuma ruhin sadaukarwa da tsayin daka da da’a ga shugaba da ya samo daga wajen dan’uwansa Husain (a.s). Don haka ana iya cewa a kowani bangare, Abbas (a.s) a shirye yake don fuskantar kalubalen da ke gabansa na taimaka wa Musulunci a lokacin da makiya suka yunkuro wajen hadiye shi, kamar yadda mahaifinsa ya yi a lokacin Manzon Allah (s). Hakan kuwa ba ya ga dimbin ilmin da yake da shi da kuma ruhin taimakawa marasa shi da yin biyayya ga dokokin Allah.

A hakikanin gaskiya ana iya cewa matsayin Abbas a wajen Imam Husain tamkar matsayin Ali ne a wajen Manzon Allah (s), sanin hakan ne ya sanya tun farko Ali (a.s) ya yi kokarin kulla alaka ta kut da kut tsakanin wadannan ‘yan’uwa biyu da samar da yanayi ta shakuwa tsakaninsu. Daya daga cikin abin da ke dada tabbatar da hakan shi ne abin da aka ruwaito yayin da Imam Ali (a.s) yake kwance a gadon shahadarsa bayan sarar da la’anannen Allah Ibn Muljam ya yi masa a masallaci. An ce a wancan lokacin Ali (a.s) ya yi umarnin da a kira masa dukkanin iyalansa. Bayan isowarsu gaba daya sai ya mika kulawarsu ga hannun babban dansa Imam Hasan (a.s) in banda Abul Fadhl al-Abbas, wanda a lokacin bai wuce dan shekara 12 a duniya ba. Ganin haka sai Abbas ya koma gefe yana kuka, sai Ali (a.s) ya kira shi kusa da shi ya kama hannunsa da mika shi ga Imam Husain (a.s) yana mai cewa: “Ya Husain, ya mika kulawar wannan yaro gare ka. Zai wakilce ni a ranar da za ka yi gagarumar sadaukarwa, zai ba da rayuwarsa wajen kare ka da sauran na kurkusa da kai”.

Daga nan sai ya juya wajen Abbas ya ce masa: “Ya kai dana Abbas, na riga da na san irin kaunar da kake yi wa Husain, duk da cewa a halin yanzu shekarunka sun yi karinci wajen gaya maka abin da zai faru, amma dai idan wannan rana ta zo, ka da ka dauki duk wata sadaukarwar da za ka yi wajen kare Husain da ‘ya’yansa a matsayin sadaukarwa mai girma da ta wuce su”. Sanin hakan ne ma ya sanya mahaifiyar Abbas, Ummul Banin, jin kadan kafin Husain (a.s) ya bar Madina a hanyarsa ta zuwa Karbala ta kira ‘ya’yanta da bayyana musu cewar: “Ya ku ‘ya’yana, ku sani cewa, a daidai lokacin da na ke matukar sonku, Imam Husain shugabanku ne. Don haka idan kuka bari wani abu ya same shi ko ‘yan’uwansa mata ko kuma ‘ya’yansa alhali kuna raye to ban yafe muku ba”.

Don haka a gaskiya ba za a iya siffanta irin biyayya da kaunar da Abbas ke nuna Imam Husain (a.s). An bayyana cewa wata rana Imam Husain ya ji kishirwa a lokacin suna tare da mahaifinsa a masallacin Kufa, don haka ya bukaci Qambar, daya daga cikin masu hidima wa Imam Ali (a.s), da ya taimaka masa da ruwa. Jin haka sai Abbas ya mike da gudu don ya kawo wa Husain (a.s) ruwa, saboda gaggawar da yake yi wajen kawo ruwan duk ya jika jikinsa da ruwan. Ganin haka sai Imam Ali (a.s) wanda a lokacin yana cikin huduba ne a masallaci ya yanke hudubar hawaye na zubo masa. Lokacin da aka tambaye shi dalilin kukansa sai ya bayyana cewar: “Saboda wannan Abbas din da a yau ya jika jikinsa da ruwa a kokarin da yake yi na kashe kishirwan dan’uwansa Husain, wata rana zai jika jikinsa da jininsa a kokarin kashe kishirwar ‘ya’yan Husain”.

Jaruntakar Abul Fadhl al-Abbas (a.s):
Rayuwar Abbas (a.s) cike take da biyayya da kuma ruhin kare Musulunci sakamakon irin jaruntakar da yake da ita. To ai hakan ba abin mamaki ba ne idan aka yi la’akari da waye mahaifinsa wanda ake kiransa da sunan ‘Zakin Allah’ saboda irin jaruntakarsa. Don haka Abbas ma haka ya taso cikin irin da irin wannan jaruntaka. Bari mu ga kadan daga cikin jaruntakarsa a fagen fama.

Yakin farko da Abbas ya fara halarta shi ne Yakin Siffin da ya gudana tsakanin rundunar gaskiya karkashin jagorancin mahaifinsa da kuma ta karya da wuce gona da iri karkashin jagorancin Mu’awiyya bn Abi Sufyan alhali a lokacin yana dan shekaru 11 ne a duniya. An bayyana cewar wata rana Abbas ya rufe fuskarsa ya fito filin daga ba tare da an gane ko wane ne ba. Ganin haka sai daya daga cikin jaruman sojojin Mu’awiyya da ake kira da Ibn Shasa ya umarci daya daga cikin ‘ya’yansa da sare wuyansa (saboda ganin yaro ne), nan take Abbas ya aika da shi lahira. Ganin haka sai ya sake turo wani dan nasa, haka dai Abbas ya dinga gamawa da su har ya’yansa bakwai suka kare amma ba tare da sun sami nasarar kashe Abbas ba. Ganin haka sai shi da kansa ya fito, Abbas ya yi nasara a kansa, wannan ya sanya kowa da ke wajen mamaki, don haka suka tsorata babu wani da ya iya sake kusato shi. Sai bayan da ya cire abin da ya rufe fuskansa ne mutane suka fahimci ko shi wane ne.

Wani abu kuma da ke nuni da jaruntakar Abul Fadhl al-Abbas (a.s), a bangare guda kuma da irin kauna da mika wuyarsa ga Imam Husaini (a.s), shi ne batun afuwa da kariyar da Shimr bn Zil Jawshan, daya daga cikin manyan kwamandojin Yazid a Karbala (wanda kuma yake matsayin kawu ga Abbas), ya nemi ya bai wa Abbas da sauran ‘yan’uwansa. Lamarin dai ya faru ne lokacin da Shimr din ya taho sansanin Imam Husain (a.s) ya ce: “Ina ‘ya’yan ‘yar’uwata, wato Abbas, Abdullah, Ja’afar da Usman? Amma yayi shiru bai ce masa komai ba har sai lokacin da Imam Husaini (a.s) ya ce masa: “Ka amsa masa mana ko da dai fasiki ne, amma ai yana daga cikin kawunanku”. Sai Abbas ya ce masa: “Me kake so”? Sai ya ce: ” Ya ku ‘ya’yan yar’uwata kuna cikin aminci, na bukaci kariya gare ku daga Ibn Ziyad, amma me ya sa kuke son kashe kanku tare da Husain? Me zai hana ba za ku shigo cikin dakarun Yazid ba? Nan take sai Abbas ya amsa masa da cewa: Allah Ya la’ance ka, Ya kuma la’anci kariyarka (amincinka), shin za ka ba mu kariya ne alhali dan Manzon Allah ba shi da kariya?

Har ila yau wani lamari makamancin hakan ya faru, wato lokacin da wani dan’uwar mahaifiyar su Abbas din mai suna Jarir bn Abdullah, wanda shi ma ya bukaci Ibn Ziyad da ya yi afuwa wa ‘ya’yan ‘yar’uwar tasa wato Abbas da ‘yan’uwansa, don haka bayan da Ibn Ziyad ya amince masa sai ya rubuta wasika ga Abbas yana kiransa da su bar rundunar Husain (a.s) su dawo ta Yazid don su ceci rayukansu (Kamar yadda ya ce). A nan ma dai Abbas ya bula masa kasa a ido lokacin da ya yaga wannan wasikar ya ce a je a gaya masa cewa: Ba za mu taba barin Husain mu nemi kariyar Ibn Ziyad ba. Muna neman taimako da yardar Allah, don haka a shirye muke mu sadaukar da rayukanmu ga abin kaunarmu Husain da kuma Musulunci”.

Ko ba a fadi ba wadannan matsaya guda biyu da Abbas ya dauka suna nuni da jaruntakarsa da kuma kaunarsa ga Imam Husain (a.s), saboda a lokacin ya tabbatar da cewar suna fuskantar mutuwa ne, babu makawa cikin haka, amma yana da zabin ya yi watsi da Husain (wal iyazu billah) ya koma rundunar makiya don ya tseratar da rayuwarsa, kamar yadda ma shi kansa Imam Husain din ya bukaci mabiyansa da su yi, inda yake ce musu: Bayan haka, hakika ban san da wasu sahabbai da suka fi sadaukarwa da alheri kamar sahabbaina ba…….ga dare ya yi don haka kuna iya amfani da shi wajen gudu, kowannenku ya dauki iyalansa ya tafi ku barni da wadannan mutane, don ba wani suke nema in ba ni ba”, amma Abbas (da sauran sahabban Husaini) ba su yi haka ba, saboda jaruntaka da kuma mika wuya ga Husain (a.s).

An ruwaito daga Imam Jafarus Sadiq(as) yana cewa: “Amminmu Abbas ‘Dan Ali(as) ya kasance mai kaifin basira, mai tsarkakakken imani, ma’abocin jahadi tare da Abu Abdullahil Husaini (AS), kuma ya fuskanci manya manyan jarabawowi, daga karshe ya kasance Shahidi.”

Abbas (AS) ya kasance shi ne marikin tutar Imam Husaini (AS) yakin Karbala, ko ba komai tuta itace babban alami a yayin mubaraza ko gumurzu, dan haka ba’a taba baiwa wani rikon tuta face Jarumin gaske da aka aminta da jarumtarsa a yayin kwamawa. To Sayyid Abbas (AS) ne marikin tutar Imam Husaini (AS) kamar yadda na ambata.

Mahaifiyar Abbas (AS) tana da yara hudu ne da Imam Ali (AS), Sune kamar haka: (1) Abbas {Abul Fadal} (2) Abdullahi (3) Jafar (4) Usman. Imam Ali (AS) ya ambata da bakinsa cewa “Na saka masa suna Usman ne saboda tunawa da Sunan Usman ‘Dan Maz’un.”

Usman ‘Dan Maz’un kuwa shi ne Sahabin Manzon Allah (S) wanda ya rasu tun lokacin Manzon Allah (S) na raye. Har ma aka ce mana shi ne farkon wanda aka fara biznewa a makabartan Baqi’a a cikin sahabban Annabi (S). 

Abbas (AS) ya kasance mafi daraja a cikin yayan Imam Ali (AS) baki dayansu baya ga ‘Ya’yan Sayyida Zahara (SA). Kuma mahaifiyarsa ta kasance mai girmama ‘ya’yan Sayyida Zahara (SA), har ma tana daukar su a matsayin shuwagabanninta ne. kuma ma har ta tarbiyantar da yayanta akan kar su dauki ‘ya’yan Fatima (AS) a matsayin Yayyinsu ko ‘Yan’uwansu, face su dauka cewa su shuwagabanninsu ne.
Wannan Waliyiyar Allah din, wacce itace Mahaifiyar Sayyid Abul Fadal (AS), ta kasance mai tsananin kauna da damuwa da Imam Husaini (AS), ta yadda hatta ma bayan da aka kawo musu labarin an kashe iyalan Annabi (S) a Karbala, cikinsu har da dukkan ‘ya’yanta fa, amma Sayyida Ummu Banin, sam bata tambayi kowa ba face Husaini (AS), an ace mata an kasha shit a fashe da kuka.

Sayyid Abul Fadal Abbas (AS) ya yi shahada tare da ‘Yan’uwansa (‘Yan Uwa daya) su uku, a yayin da yake da shekaru 34. Shi kuwa kaninsa Abdullahi yana da shekaru 25, Usman kuwa yana da shekara 21, a yayin da Jafar kuwa yake da shekaru 19.
Don karin bayani:
1. Abu Mikhnaf, Lut b. Yahya. Waq’at al-taf. Hadi Yusifi Gharawi. Qom: Majma’ Jahani Ahl al-Bayt, 1433AH-1390Sh.
2. Tabari, Muhammad b. Jarir al-. Tarikh Tabari (Trikh al-Umam wa al-Muluk). Muuhammad Abu l-Fadl Ibrahim. Beirut: 1378-1382 H -1962-1967 M.
3. Amin, sayyid Muhsin al-. A’yan al-shi’a . Beirut: Dar al-Ta’aruf, 1406 H.
4. Dinawari, Ahmad b. Dawud al-. Akhbar al-tiwal . ed. ‘Abd al-Mun’im ‘Amir

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky