SHAIKH YAƘUBU YAHAYA YA YI WA RAUNI KASHEDI.

SHAIKH YAƘUBU YAHAYA YA YI WA RAUNI KASHEDI. 
An buƙaci 'yan uwa da kada su sakar wa rauni fuska har su ɗauka cewa akwai abinda basu iyawa.

Shaikh Yaƙub  Yahaya ya bayar da wannan shawarar alokacin da yake jawabi  alokacin da 'Yan lajnar islamiyyu suka kaimasa ziyarar shekara - shekara da suka saba kaimasa. 
Malamin ya bayar da misali da lmam Khumaini alokacin da aka kafa daula aka rasa masu gyaran jiragen sama,  saboda ɓarnar da Amerikawa sukayi a ƙasar inda ya buƙacesu da suje su gyara jiragen zasu iya.

 Da kuma misalin Fital castro na cuba wanda ya ɗauki ƙarfafa ilimi musamman na likitoci,  da injiya, a matsayin hanyar fitar da ƙasarsa daga cikin ƙunci da maysaloli.

Malamin ya yi kira ga Malaman islamiyyu da suƙara zage damtse wirin ba 'ya 'yan 'yan uwa karatu sosai musamman akan Ƙur'ani da Tajwid,   sai Tauhid,  da Akhlaƙ.  Waɗannan sunada mahimmaci sosai ga al'umma. 

Shaikh Yaƙub Yahaya ya bayyana haka ne alokacin da  Shugan Lajnar ta Islamiyyu  na Da'irar Katsina, Malam Yaƙub Idris ya zayyano jerin matsalolin da Lajna ke fuskanta.

Har ila yau a jawabin nasa Malam Yaƙub  Idris ya kawo ɗinbi nasarorin da lajnar ta samu waɗanda suka haɗa da yaye ɗaliban ajin  haidar primary da haidar secondary da kuma haidar college masu matakin N. C. E kuma sun samar da tsare-tsaren karatu Ajin corona, alokacin da aka kulle makarantu,  yanzu haka lajna ta samar da azuzuwa da Malamai da tsarin karatun da suka dace da yanayi na kullen corona ta gyara masu tsari ta yadda koda za'a samu wani kullen  nan gaba ba zai shafi karatuttukansu ba. 

Ya kuma kawo ƙima da matsayin karatun nasu inda ya yi nuni da cewa a duk lokacin da ɗalibansu sukaje koyarwa ta gwaji a makarantu akan yaba ƙwarai da karantarwarsu.

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky