YAKIN BADAR BABBAR NASARACE GA MUSULUNCI

Yakin Badar Babbar Nasara Ce Da Ke Tabbatar Da Kafuwar Daular Musulunci, Inji Farfesa Danladi

Daga Ammar M. Rajab
Farfesa Abdullahi Danladi, Malami a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya ya bayyana cewa yakin Badar babbar nasara ce da ke tabbatar da cewa daular Musulunci ta kafu babu mai iya nuna mata dan yatsa. Farfesan ya bayyana hakan ne a yayin muhadara kan ranar Badar da ya gudana a jiya Alhamis 17 ga watan Ramadan 1442 a garin Zariya. Taron ya gudana ne a muhallin Fudiyya dake Babban Dodo Zariya.

A kowacce rana cikin watan Ramadan, ana gudanar da Tafsirin Alkur’ani mai girma wanda Shaikh Abdulhameed Bello ke jagoranta, sai dai a jiyan an gudanar da muhadara ce kan ranar Badar wanda Farfesa Abdullahi Danladi ya gabatar da jawabi. 

Farfesa Abdullahi Danladi ya kawo tarihin yakin Badar tiryan-triyan, harma ya nuna yadda tun daga yakin Badar da aka yi, aka samu fasahar amfani da ‘camouflage’ da dakarun sojoji suke amfani da shi a yau. 

A wani bangare na jawabinsa, Farfesa Danladi ya nuna yadda muminai suka kasance ‘yan kadan a ranar Badar, amma sakamakon dogaro da muminai suka yi da Allah, Allah ya sanya wa mushrikai firgici suke ganin Muminai da yawan gaske. 

Sannan ya karanto yadda aka fara yakin a matsayin mubaraza kafin daga bisani a hadu a gwabza. Ya yi bayanin yadda Imam Ali da Sayyidina Hamza suka fafata a yakin, da yadda wuri ya yamutse har Manzon Allah (SAWW) ya shiga Haima yana addu’a cikin magiya, yana rokon Allah cewa; “Ya Allah wadannan sune kadai musulmi a doron kasa, idan ka bari aka yi galaba a kan su, babu mai kara bauta maka a doron kasa”. Farfesa Danladi ya kawo yadda Manzon Allah (SAWW) ya fito daga Haima yana murmushi saboda alkawarin nasara da Allah ta’ala ya yi masa. 

Farfesa Abdullahi Danladi ya kawo yadda aka shahadantar da muminai guda goma sha hudu, inda aka kashe muhajirun guda shida, ansar kuma guda takwas. Sai dai ya yi bayanin cewa; muminai sun yi nasarar kashe kafirai har guda saba’in, a yayin da suka kama guda saba’in a matsayin ribatattun yaki. Ya kawo ruwaya da ke nuni da cewa; cikin Kafirai saba’in da muminai suka kashe a yakin Badar, Imam Ali (AS) shi kadai ya kashe mutum talatin da biyar. 

Sannan har wala yau a wani bangare na jawabinsa, ya nuna yadda a wannan yakin na Badar yadda muminai suka kashe manyan Kwamandojin Kuraishu, wanda ta kai ma babu wani gida a kuraish da yakin Badar bai ta ba. Ya nuna yadda wannan nasarar da muminai suka yi akan mushrikai a yakin Badar ya sanya Abu Lahad ya shiga dimuwa da bakin ciki wanda ta kai a wannan rana shima ya mutu saboda bakin ciki. 

Farfesa Abdullahi Danladi ya kawo ruwayar yadda Manzon Allah (SAWW) ya sanya dukkanin mushrikai saba’in da muminai suka kashe a yakin Badar a cikin rijiya baki dayansu. Inda mushrikai a Makkah suka cika da bakin ciki. A yayin da kuma musulmi a Madinah muminai suka yi ta murna akan abin da ya faru, su kuma munafukai suma suka cika da bakin ciki. 

Har wala yau Farfesa Abdullahi Danladi, ya bada bayanin cewa; a yakin na Badar muminai guda 313 ne kacal, a yayin da kafirai suka zo da runduna ta mutum dubu daya. Wanda ya ce su muminai a lokacin ba su fito da niyyar  yaki ba shiyasa ma a tare da su rakumi biyu ne da dawakai biyu, inda duk sauran a kafa suke tafiya. A yayin da su kuma kafirai suka zo da runduna ta mutum dubu daya da shirin yaki da rakuma 600 da daruruwan dawakai, amma bisa taimakon Allah muminai suka samu nasara akan Kafirai; “me ya bai wa muminai nasara? Taimakon Allah! An yi badar a cikin watan Ramadan a rana ta 17 ga watan Ramadan”, ya lurantar. 

Har wala yau Farfesa Abdullahi Danladi da yake bayyana irin darussan da za a dauka a watan Ramadan, ya bayyana cewa; “Ramadan makaranta ce da ake samun shaidar tsoron Allah a ciki”, inji. Inda ya shawarci ‘yan’uwa da su maida dukkanin lamuransu ga Allah, inda ya ce; “idan aka yi wata waki’a Allah ya taimaka ka samu sabati, ka da ka yi alfahari, a kaskantar da kai ya zuwa ga Allah”, ya lurantar. 

Farfesa Danladi ya bayyana cewa; daya daga cikin darasin da ‘yan’uwa za su dauka a yakin Badar shi ne; a lokacin da Manzon Allah (SAWW) ya fahimci al’umma a shirye suke su bi shi, su kuma yi yaki a bangarensa, sai Manzon Allah (SAWW) ya cika da farin ciki, sai Farfesa Abdullahi Danladi ya ce; “haka ya kamata mu zama da jagoranmu. Mu bi shi ko da zamu rasa rayukanmu, mu kuma bi shi saboda Allah, mu kuma gyara tsakaninmu da Allah”. 

Har wala yau ya nusasshe da cewa; irin yanayin da yanzu ‘yan’uwa ke ciki magabatanmu sun fuskanci irinsa, ya ce; haka hanyar Allah take, dole sai an yi wa mumini jarabawa. Sai dai ya ce; “rana na zuwa da za a bai wa muminai dama su fafata. Azzalumai ba shi kuke ci, lokacin zai yi na ramawa, za ku ci ubanku”, ya tabbatar. 

Ya shawarci ‘yan’uwa da su bautawa Allah da yakini, inda ya ce; “in dai kana bautawa Allah a ko’ina kake, to ka yi nasara”. 

Farfesa Danladi ya nusashe da yadda ‘yan’uwa ake wasa da al’amarin jagora, inda ya nuna yadda wadansu a wasu kasashen suna neman jagora mai fikira, amma sun rasa,  amma mu mun samu jagora amma muna baganniya. Ya nemi da muminai su nemi sabati a wurin Allah a koyaushe irin yadda Ansar da muhajirun suka yi. 

Har wala yau dangane da yakin Badar, Farfesa Danladi ya ce; “yakin Badar babbar nasara ce da ke tabbatar da cewa daular Musulunci ta kafu babu mai iya nuna mata dan yatsa”. 

Da yake ta’aliki, Shaikh Abdulhameed Bello ya nuna cewa tabbas Badar babbar nasara ce gare mu. Inda ya yi addu’ar cewa; “Allah ya nuna mana namu Badar din a karkashin jagorancin Shaikh Zakzaky”.

Ya kuma wadansu abubuwa da suka faru a rana irin ta 17 ga Ramadan wanda ya hada yadda Manzon Allah (SAWW) ya yi mi’iraji a irin wannan rana, sai dai ya ce dama ba sau daya Manzon Allah ya yi mi’iraji ba, ya yi a lokuta da dama. 

Sannan ya kawo cewa; a irin wannan rana ta 17 ga Ramadan ne, Mu’awiyyah dan Abu Sufyan ya kashe matar Manzon Allah (SAWW), Uwar Muminai Sayyidatuna Aisha. 

Sannan ya tunatar da cewa a yau Juma’a daren Sha Tara ga Ramadan za a fara raya dararen Layalil Kadri a muhallin Na Fudiyyah Zariya.

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky