Posts

Showing posts from May, 2021

Muzaharorin Qudus: Dubun-dubata Suka Halarta A Katsina

Image
Muzaharorin Qudus: Dubunnai Suka Shiga A Katsina. @Daga A.I Musa Voice of Sheikh Kamar yadda duk duniya a juma'ar karshen watan Ramadhan na kowace shekara, Musulmin duniya kan gudanar da Muzaharorin nuna goyon bayansu ga Palasdinawa daga cin zarafin da Isra'ila ke yi ma su a kullum, bana ma, 'yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Yaqoub Alzakzaky(H) na garin Katsina a tarayyar Nijeriya, sun bi sahun tagwarorinsu Musulmin na sauran Kasashe, wajen gudanar da jerin goyon bayan Palstinawan. Jerin gwanon Muzaharar wanda ya fara da misalin Karfe 9:00 daidai na safiyar Juma'ar nan 25 ga Ramadhan 1442H (7 ga Mayu, 2021) ya samu halartar dubun-dubatar al'ummar Musulmi. Muzaharar dai ta tashi daga Unguwar Madawaki inda kaitsaye da wuce zuwa Babban Masallacin Juma'a, ta kuma karkata ta bi ta Mobil, ta zagaya ta zo Sabon layi, inda aka tuke ta Tashar Gagare. A lokacin gudanar da Muzaharar, dinbin al'umma ne dauke da hotunan Palasdinawa da hot