Muzaharorin Qudus: Dubun-dubata Suka Halarta A Katsina

Muzaharorin Qudus: Dubunnai Suka Shiga A Katsina.
@Daga A.I Musa Voice of Sheikh

Kamar yadda duk duniya a juma'ar karshen watan Ramadhan na kowace shekara, Musulmin duniya kan gudanar da Muzaharorin nuna goyon bayansu ga Palasdinawa daga cin zarafin da Isra'ila ke yi ma su a kullum, bana ma, 'yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Yaqoub Alzakzaky(H) na garin Katsina a tarayyar Nijeriya, sun bi sahun tagwarorinsu Musulmin na sauran Kasashe, wajen gudanar da jerin goyon bayan Palstinawan.

Jerin gwanon Muzaharar wanda ya fara da misalin Karfe 9:00 daidai na safiyar Juma'ar nan 25 ga Ramadhan 1442H (7 ga Mayu, 2021) ya samu halartar dubun-dubatar al'ummar Musulmi.

Muzaharar dai ta tashi daga Unguwar Madawaki inda kaitsaye da wuce zuwa Babban Masallacin Juma'a, ta kuma karkata ta bi ta Mobil, ta zagaya ta zo Sabon layi, inda aka tuke ta Tashar Gagare.

A lokacin gudanar da Muzaharar, dinbin al'umma ne dauke da hotunan Palasdinawa da hotunan Sayyeed Ibraheem Alzakzaky(H) da kuma hotunan irin kisan gillar da Isra'ila ke yi wa Palasdinawan, da kuma hotunan kisan gillar da gwamnatoci tare da hukumomin Najeriya ke yi wa Almajiran Shaikh Alzakzaky(H) musamman na shekarar 2015 inda gwamnatin Buhari ta kashe Musulmi sama da 1000, da kuma sauran hotunan Shahidan harkar Musuluncin da aka shahadantar a lokuta daban-daban musamman a Waki'ar Kudus da shekarar 2014 a Zariya.

Bugu da kari, masu muzaharar suna tafe suna rera wakokin alhini na kisan da ake yi wa Palasdinawa da kuma wanda ake yi wa 'yan uwa Musulmin a Najeriya, tare da jadda kiranye ga gwamnatin Buhari a kan ta saki Shaikh Ibraheem Zakzaky(H) da mai dakinsa Malama Zeenatu Ibraheem, wanda take tsare da ssu shekara da shekaru tare da raunukan halbin bindiga da ake a jikinsu, alhali tuntuni Kotu ta yi umurni cewa a sake su har ma a biya su diyya keta 'yancinsu da gwamnatin ta yi, amma dai gwamnatin Buhari ta shure wannan umurnin da kafa, ta kuma yi kunnen uwar shegu da batun.

Shaikh Yakubu Yahaya Katsina, Wakilin 'yan Uwa Musulmi a Katsina shi ne wanda ya rufe Muzaharar jerin gwanon nuna goyon Palasdinawan da Jawabinsa mai ratsa zuciyar mai Imani dangane da abin Isra'ila ke yi wa Palasdinawa da kuma wanda gwamnatin Buhari ke yi wa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky(H) a Najeriya.

Bayan kammala Jawabin, Shaikh Yakubu Yahaya ya kuma jagorancin kona Tutar Isra'ila wadda ya cinna wa wuta da hannunsa, a yayin da kabarbari masu amo da sauti suka cika Wajen.

Abin da ke biye, kundin Hotunan da muka dauka ne a yayin Muazaharar.

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky