LABARI MAI MATUƘAR SOSA RAI

Labari Mai Sosa Rai.
DA MUN SAN BAKU DA MAKAMAI DA MUN KASHE KU TUN CIKIN DARE.

      Inji Aliyu Adamu Tsoho Jos

      --Idishia Jos.

Wannan maganar ta fito ne daga bakin Sojojin Da Suka Zo Kisan 'yan'uwa Hussainiyyah Bakiyatullah.

-Akwai wani dan uwa da na Ganshi yana salloli da addu'a a zaune tun zuwa na Hussainiyya har aka kammala wakiya bai tashi a wannan wajen ba.

-Tun isowa na Hussainiyya Bakiyatullah ake budewa wuta akan 'Yan'uwa haka muka kwana ba su bari ba.

-Munyi waya da Malam Turi a lokacin da nake cikin Hussainiyya yake tambaya na ina inane nace ina Zariya yace kun koma makaranta ne nace mai a Amma yanzu haka ina Hussainiyya sai yace to kace abin ya ritsa daku nace mai a.

-To, bayan kallama Kammala Muzaharar Kano sai Malam Turi ya kara kira yake tambaya yanzu wani hali kuke ciki ? sai nace mai gasu nan sai harbi suke kuma mun samu labari sun wuce gyellesu a take yace muma gamu nan mun taho Zariya insha Allah.

-Washe gari bayan Sallah Asuba sun zagaye 'yan'uwa a Hussainiyyah Bakiyatullah suka balla "Get" din Hussainiyyah da Motar Igwa anan suka bude wuta sosai akan 'Yan'uwa anan ma sun shahadantar da dama daga cikin wanda suke wajen. Amma sai ya zama basu iya shigowa cikin Hussainiyyah ba saboda a tunanin su muna da makamai a ciki.

-Iya kallonka 'Yan'uwa ne Jingim wanda aka harba wasu sunyi shahada wasu kuma suna ta motsi. Abin ban tausayi yadda naga wasu sistoci bayan su da goyo an harbi Iyayen su. Duk da haka mun samu tausayawa daga bakin wasu Kiristocin Sojoji a Hussainiyyah har ta kai ga sun tseratar da wasu daga cikin mu.

-Sun bigeni a kafan dama har ta kai bana iya takawa sun nausheni a kai na daga nan ban sake sanin inda nake ba, suka zuba mu a mota Maza da Mata  haka suka kai mu Barack na sojoji. Zuwan mu Barack na sojoji kamar an kawo mu ganima yadda su kai ta dukan mu suna ci mana zarafi musamman 'yan'uwa mata.

-Akwai wasu abubuwa na batanci da isgili wanda ba zan iya fada ba, musamman abinda suka yi wa mata a wajen a gaban kowa-da-kowa. A cikin mu wani dan'uwa ya mike tsaye yayi kabbara sau 2 saboda abin ya kona mai rai nan take wani soja ya harbeshi a kai ya fadi kasa a nan ya zama shahidi.

-Daga Barack na Zariya kai tsaye cikin daren aka kai ku Kaduna, misalin karfe 2 muka isa anan ne suka rabamu Police Station da suke cikin Kaduna. Daga baya kuma aka ce za'a kai mu prison na garin Kaduna.

   Daga Jawabin Aliyu Adamu Tsoho Jos wanda yayi  yanzu haka a wajen Taron Zikiran tunawa da wakiyar 12 December wakiyar Zariya.

#FreeZakzaky
@Media Forum Jos.
voiceofsheikh@gmail.com

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky