SAKON JAGORAN JUYIN JUYA HALI NA IRAN.

Sakon Jagoran Juyin Juya Hali Na Kasar Iran Sayyid Khamne'i Kan Bikin Haihuwar Annabi Isa (AS) .......

Shafin twitter na Ofishin Jagoran juyin Musulunci a Iran ya mika sakon taya murna kan zagayowar bukukuwan Kirsimeti ga dukkanin mabiya addinai da aka saukar daga sama.

A cikin sakon Jagoran, ya bayyana cewa:

"Kauna da girmamawa da Musulmi suke yiwa Annabi Isa Almasihu (AS) bai gaza wanda mabiya addinin Kirista suke yi masa ba".

Jagoran ya isar da makamanciyar irin wannan sako a harshen Farisanci wanda ya kunshi dogon jawabi.

Shafukan isar da sakon Jagora da harsunan Turanci, Larabci, Faransaci, Hausa, da dai sauran manyan yaruka na diniya sun fassara da wadan nan yauruka domin sakon ya isa ga masu jin wadan nan yaruka.

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky