SAYYID ZAKZAKY (H) GA ALLAH YA DOGARA

DOGARO GA ALLAH SHINE BABBAN MAKAMIN JAGORANMU

Ina iya tunawa, ance a daren Waki'ar Zariya, lokacin da Sojojin Nigeria suka fara shela ga yan uwa da ke Husainiyyah akan su fito su mika wuya (Surrender) ba za a musu komai ba. Sun nemi Jin ta bakin Jagora, akan su fita ko su ki? Amsar Jagora, Sayyid Zakzaky garesu shine su dake su dogara ga Allah.

Washe gari da safe, da wasu 'yan uwa masu Iklasi suka je suka roki Jagora Zakzaky (H) akan za a samar da hanyar da za a fitar da su, abin da Malam ya nuna shine ya fita ya je ina? Sauran wadanda aka kashe ba mutane bane? Su Malam suka ce; "Mu tsaya kawai mu dogara ga Allah."

Ba ku ji audio din wayar da Shaikh Zakzaky (H) ya yi da wani Brother Husain ba a safiyar Waki'ar? A yayin da yake cewa Malam ya zai yi da rayuwarsa alhali tana cikin hadari? (Dama a lokacin Sojoji sun kashe mafi yawan yan uwa sun fara saka wuta a gidan Shaikh Zakzaky alhali yana cikin gidan), Amma abin da Malam Zakzaky yace masa shine; "Babu wani Abu da zan iya yi, face Allah ne kawai zai kubutar da ni."

Mu kara gane al'amarin bawan Allah din nan na Allah ne, a yayin da ya mika cikakkiyar sallamawa ga Allah (T), sai Allah ya Isar masa. Malam Tahir Ibrahim daya ne daga cikin masu hidima a gidan Jagora (H), ya fada min cewa shi ko da ya ji sanarwar cewa Sojoji sun kashe duk yan gidan Malam, har Malam da Malama sun yi Shahada da duk yara. Ya iya yarda kowa zai yi Shahada Amma bai yarda an kashe Malam ba. Sam zuciyarsa bata amince ba. Saboda iyakacin abin da ya sani shine Malam ma'aikacin Allah ne. In kaga ya tafi to ya gama aikin kenan.

Tsawon tsarewar da ake wa Jagora Zakzaky, duk Sanda ya yi magana da Iyalan, Dangi da yan uwa, cewa yake su dogara ga Allah. Wani Dan uwa da ya sha ziyartar Malam (H) tun farko farkon Waki'ar nan, ya fada min cewa su Malam (H) kullum suna addu'a akan Allah (T) ya cire tsoron abin halitta a zukatan 'yan uwa.

Tsoro na daga cikin abin da rashin sallamawa ke kawo shi. Wannan yasa a kullum Jagora ke mana adduar samun tabbata. Kuma Alhamdulillah na yarda da cewa Allah ya amshi adduar Bawansa, a yayin da in ka dubi Waki'ar Abacha da yawa wasu yan uwa sun kasa juriya sun gudu daga Harkar. Amma wannan karon ko a kauye ba mu samu labarin burazan da ya bar Harka Don tsoro ba, sai ma masu fahimtar Harkar dare da rana.

Lokacin da aka zo wa da Jagora Zakzaky (H) labarin hukuncin Kotu, cewa tace an Tsare shi bisa zalunci kuma a gaggauta sakinsa daga tsarewar a kuma biya shi diyya. Abin da Malam Zakzaky yace shine, Insha Allah, Allah ne kawai zai iya kubutar da mu. Alhamdulillah da sallamawar Jagora ga Allah (T), wanda hakan ne ya haifar da nasara a gare shi a zahiri da Badini a kowane yanayi.

Dogaro ga Allah shine babban sirrin tsayuwar Harkar Musulunci! Baka ganin shi yasa tsawon shekaru kusan 40 da Harkar nan, an kasa Murkusheta? Zakzaky ba shi da ubangida sai Allah da Majibintansa! Bai dogara ga kowa ba face Allah. Hakan yasa ko tsoro babu a tare da shi. Kuma bai yarda kowa na iya cutarwa ko amfanarwa gare shi ba sai da nufin Allah.

Wallahi, Tallahi, Billahillazi La'ilaha Illahuwa, Malam Zakzaky ne ajalin Buhari, Buratai, Elrufa'i da duk mataimakansu akan zalunci, nan da kwanaki kididdigaggu! Insha Allah.

Allah ne Majibincinmu.

— Saifullahi M Kabir
    27/12/2016https://youtu.be/NSQLm6Wrs0E

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky