TAKARDAR SANARWAR MANEMA LABARU AKAN BATUN SHEIKH ZAKZAKY(H)

TAKARDAR SANARWAR MANEMA LABARAI
*BATUN SHAIKH ZAKZAKY BA A HANNUN
GWAMNA EL-RUFA’I YAKE BA*
Muna so mu bayyana karara tare kuma da yin
watsin baro da kalaman Antoni-Janar na
Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a na
kasa, Abubakar Malami SAN na cewa batun
Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh
Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa Malama
Zeenah, batu ne wanda yake a hannun
gwamnatin Jihar Kaduna da kuma Gwamnan
Jihar, Nasiru Ahmed El-rufa’i. Ba za a iya taba
yaudarar mu ba da kowane irin salon makirci
na nuna cewa wannan gwamnatin ta
Muhammadu Buhari ba ta da hannu a cikin
batun auka wa Shaikh Zakzaky da kuma ci
gaba da tsare shi.
Da farko, ba wani abin da akwai shakku a kai
ba ne cewa gwamnatin tarayyar Nijeriya ita ce
ta kaddamar da kisan kiyashin Zariya wanda
aka yi a cikin watan Disamba, 2015, lamarin da
ya sabbaba kisan ’yan’uwa Musulmi na Harkar
Musulunci a Nijeriya sama da mutum dubu
daya haka siddan, tare kuma da kamawa da
tsare Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya,
Shaikh Ibraheem Zakzaky.
Wannan lamari ya fito fili tare kuma da
tabbatuwa Janar Muhammadu Buhari a yayin
hirar da gidan Talabijin da ke Qatar ya yi da shi
a lokacin da ya kai wata ziyara a cikin watan
Mayu na shekarar 2016. Haka nan kuma
Yarima mai jiran gado na Kasar Saudiyya ya
kara tabbatar da hakan a yayin da ya kai wata
ziyara Kasar Amurka, a inda ya bayyana tare
da tabbatar da cewa, bakin zalunci na kisan
kiyashi da aka yi a garin Zariya da kuma ci
gaba da tsare Shaikh Ibraheem Zakzaky na
daga cikin manyan kuduri na alfahari da suka
cimmawa a kan sha’anin kudurorin mu’amalar
kasa da kasa, ga shi kuwa lamari na Kasa da
Kasa batu ne wanda ake gudanarwa da
gwamnatin Tarayya ba wata jiha ba.
Shin wannan ba shi ne dalilin da ya sanya
Sarkin Saudiyya ya zama na farko ba wanda
ya kira Janar Buhari a cikin watan Disambar,
2015, jim kadan bayan kaddamar da Kisan
kiyashin Zariya, domin yi masa murna da kuma
jinjina ta musamman ba dangane da abin da
ya kira nasarar da ya samu a kan murkushe
ta’addanci? Shin ba shi ne dalilin da ya sanya
Janar Buhari ya yi yunkurin shigar da tarayyar
Nijeriya ta barauniyar hanya cikin kawancen
yaki da ta’addanci wanda Saudiyya ke wa
jagoranci ba? Shin ba shi ne dalilin da ya sanya
Ministan tsaron ciki gida a lokacin, Mansur Dan
Ali ya samu lambar yabo ba daga Mahukuntan
Kasar Saudiyya a madadin gwamnatin tarayyar
Nijeriya sabili da irin rawar ganin da rundunar
Sojojin Nijeriya ta taka, alhali daya daga cikin
Hukumomin gwamnatin tarayya ne?
Dalili na biyu, kaddamar da hare-haren, kamu
da kuma tsare Shaikh Zakzaky da ya biyo baya
dukkanin su lamurra ne wanda Jami’an tsaro
mallakin gwamnatin tarayya suka aiwatar.
Tsawon shekaru hudu da suka gabata,
Jami’an tsaro na farin kaya (DSS) su ne suke
tsare da
Shaikh Zakzaky da mai dakinsa tun da suka
karbe su daga hannun Jami’an tsaro Sojoji.
Babu wanda ke da damar ganin su face sai ya
samu izini da yarjewa daga wadannan
Hukumomin gwamnatin tarayya. Wani lokaci
ma sai mutum ya samu izini daga Antoni-
Janar na Tarayya; kamar yadda ya faru da
Hukumar Bincike wadda gwamnatin Jihar
Kaduna ta kafa a yayin da take bukatar ganin
Shaikh
Zakzaky.
Haka zalika, a yayin da babbar Kotu da ke
Abuja ta yanke hukuncin cewa tsarewar da ake
yi wa Shaikh Zakzaky da mai dakinsa, Malama
Zeenah haramtacciya ce, wadda ba bisa ka’ida
ba, wanda kuma ya saba wa Kundin tsarin
Mulkin Kasa, ta kuma zartar da umarnin
gaggawar sakin su daga inda ake tsare da su,
to ta bayar da umarnin ne ga Hukumar tsaro ta
farin kaya (DSS), hukumar tsaro ta ’yan Sanda
da kuma Antoni-Janar na Tarayya, wadanda
dukkanin su suna wakiltar gwamnatin tarayya
ne. Gwamnatin Jihar Kaduna ba ta da ruwa a
cikin wannan lamari kwata-kwata. Don haka
wa Antoni-Janar na tarayya yake so yanzu
kuma ya wawaitar da furucinsa na cewa wai
batun Shaikh Zakzaky lamari ne wanda yake a
hannun Jihar Kaduna?
Babu ta yadda za a iya gabatar da wani bayani
wanda sahihin hankali zai dauka dangane da
tsame ko wanke Shugaban Nijeriya, Janar
Buhari da mukarrabansa na gwamnatin
tarayya a kan batun ci gaba da yi wa Shaikh
Zakzaky da mai dakinsa haramtacciyar
tsarewa ba bisa ka’ida ba da ake ci gaba da yi.
Duk da cewa gwamnati bisa makirci ta shigar
da kara a Kaduna, shekaru uku bayan ana
tsare da su ba bisa ka’ida ba, ana tukumar su
da laifin taimakawa wajen tayar da fitina da
kuma kisan kai a gaban babbar Kotu ta Jihar
Kaduna, to ai irin wadannan tuhume-tuhumen
ne tuni wannan Kotun ta yi watsi da su a
lokacin da ta saurari shari’ar daruruwan
wadanda aka gabatar mata, ta sallame su, ta
kuma wanke su fes daga aikata wannan laifi da
aka tuhume su da aikatawa. Don haka wannan
tuhuma da ake yi wa Shaikh Zakzaky ba komai
ba ce face wani makircin yunkuri yi wa
Jagoranmu haramtacciyar tsarewa ba bisa
ka’ida ba ta dindindin.
A karshe, muna kira tare da bayar da shawara
ga gwamnatin Buhari da ta daina yaudarar
al’umma ta hanyar yunkurin tsarkake kanta
alhali ayyukanta a bayyane suke sun fi na
Shaidan ma muni. Wannan gwamnatin ta bi
umurnin kotu kawai, ta saki Jagoranmu wanda
muke
girmamawa, Shaikh Ibraheem Zakzaky, a daina
ci gaba da shari’ar boge da nufin ci gaba da
tsare shi.
SA HANNU:
IBRAHIM MUSA
SHUGABAN DANDALIN YADA LABARAI NA
HARKAR MUSULUNCI A NIJERIYA
SKYPE: Ibrahim.musa42
29/12/2019
Fassarar Zaharaddeen Sani Malumfashi.

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky