TAYA MURNAR ZAGAYOWAR RANAR HAIHUWAR YESU ALMASIHU( A.S)

DAGA ZAUREN JAWABAN MALAMANMU.

Amamadin Ma'aikatan wannan Zaure mai suna a sama "JAWABAN MALAMANMU", muna taya 'yan uwanmu a dan' Adamtaka da kuma kasancewa 'Kasa daya wato Kiristoci, Murnar zagayowan ranar Haihuwar daya daga cikin Manya-manyan Manzannin Allah a doron Kasa,Annabi Isa Almasihu(A.s),kamar yadda yake a Lissafin Shamsiyya.

Mu(Musulmi) da ku (Kiristoci),mu yi amfani da wannan rana wajen fahimtar da junanmu muhimmancin dorewar zamantakewarmu akan zaman lafiya da ci gaban Kasa, da kuma wanzar da sada zumunci irin na Adamntaka a tsakaninmu.Mu kuma yi amfani da wannan damar wajen kara yin kiraye-kirayen wanzuwar zaman lafiya a tsakaninmu, duba da yadda Allah ya 'kaddara kasancewarmu A Kasa daya wadda ake kira Najeriya,ba mai korar wani.


Da fatan za a yi shagulgulan Ranar Kirsimeti Lafiya a kare lafiya.


Tsarki ya tabbata ga Mahaliccin sammai da Kassai,wanda ya fifita sashen Annabawa akan sashe.Allah ya kara girman Daraja da daukaka ga tsarkakken bawansa,Ruhinsa,Yesu Almasihu,dan Maryam (A.s).www.youtube.com/voiceofsheikhtv

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky