HALIN DA IS'RAILA DA YAHUDAWA SUKE CIKI TUN BAYAN HARIN SOJIN IRAN A SANSANIN AMURIKA A IRAQ

Nasir Isa Ali.
-Halin da Israila da Yahudawa ke ciki tun bayan kashe Janar Qassim Sulaimani.
--
Rahotanni sun tabbatar da cewar,manyan jami'an gwamnatin Isaraila sun shiga wasan buya,tare da yin kaffa-Kaffa wajen yin tafiye tafiye da yawan bayyana wajen taro tun bayan harin da Iran ta kai kan sansanonin sojan Amurka dake cikin kasar Iraqi. Domin hakan ya nuna cewar,Iran din zata hararsu a ko'ina cikin yankin Asiya.
Daya daga cikin hujjojin dake tabbatar da hakan shine, kafin kai harin na Iran kan Amurka,an shirya cewar Ministan harkokin kasashen waje na H.K.Israila, Mr.Yisrael Katz zai ziyarci birnin Dubai dake UAE domin halartar wani taron baje koli a tsakiyar wannan watan na Junairu,amma sai aka janye ziyarar,kuma babu wani dalili kan janyewar.
Amma jami'an ma'aikatar tasa ta harkokin waje sun sanar da cewar,an yi hakan ne bisa wasu manyan dalilai na tsaro.
-
Tun dai bayyanar wani rahoton sirri dake nuna cewar,shugaba Trump yayi amfani ne da wani rahoton sirri na MOSSAD wanda suka fara tattarowa tun a shekarar 2011 kan Janar Qassim Saimani, wajen yi masa kisan gilla. Da kuma kashedi da gargadin da Shugaban kungiyar Hizbullahi,Hassan Nasrullah ya yi wa Israilan cewar,su kuka da Kansu,domin kuwa wannan harin da Iran din ta kai kan sansanonin Amurka gargadi ne ga Israilan. Tun sannan ne dai jami'an Israialan suka sha jinin jikinsu wajen yawan yin zirga zirga a idon duniya.
-
Wani jami'in tsaron Israila ya tsegunta wa kamfanin dillancin labarai na "Routers" cewar,wasu jami'an tsaron Israilan ne suka gargadi Mr.Yisrael Katz da ya janye tafiyarsa zuwa Dubai din,domin akwai matsalar tsaro,kuma komai na iya faruwa. Sun kara da cewar,suna da labaran sirri dake nuna cewar,akwai sunayen wasu jami'an Israila kan teburin IRGC,don haka ne ministan ya shafawa kansa ruwa ya soke tafiyar.
Sun bayyana masa cewar,Iran na iya  daukar ransa ko su harbo jirgin nasa,duk a cikin daukar fansar kisan Sulaimani. Tunda jagoran Iran din ya bayyana wancan harin da cewar,somin tabi ne (Mari ne ga Amurka)  Har yanzu dai ba a sake saka wata ranar ziyarar ta minista Katz ba.
Shi dai Mr.Katz ya taba rike mukamin ministan tsaron Israila,wanda kuma ake kyautata zaton a lokacinsa ne aka fara bude shafin tattara bayanan sirri kan Janar Sulaimani da kuma yadda za'a za'a yi masa kisan gilla.
-
Rahotanni sun bayyana cewar, a lokacin da suke tattara bayanan sirrinkan janar Sulaimani,MOSSAD ta iya gano hanyoyin da janar Sulaimani yake bi wajen yin tafiye tafiyensa daga Iran zuwa Lebanon,Syria da Iraqi,kuma sun iya tsara yadda za'a iya yi masa kisan gillar,amma sun kasa kai masa hari saboda tsoron abin da zai biyo bayan hakan. Don haka sai suka nemi alfarmar Trump da ya aikata kisan gillar a madadin Israila.
Don haka Iran tana nan tana yin nazarin wadannan bayanan da kuma irin martanin da zata mayar kan Israilan.
Yanzu dai hukumomin Dubai din sun yarda Israilan ta tura wasu kananan jami'anta gwamnatinta domin wakiltar ministan nata,sakamakon janye ziyarar tasa.
-
Ba wai shi Mr.Yisrael Katz ba,akwai wasu ministocin da dama da suka shiga wasan buya tare da dan'uwansu bayahude Katz saboda gujewa makaman Iran. Rahoton ya bayyana cewar,a cikin ita kanta Israila ana kaffa kaffa da yin taro a fili,ko kuma bayyana fuskarsu a wajen taro saboda gudun saukar makaman Iran ko Hizbullahi.
-
Nasir Isa Ali

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky