HAƘURI DA HANKALI DA IRAN TA NUNA SHINE BABBAN MATAKIN NASARAR FARKO GA MUMINI- Nasir Isa Ali

Nasir Isa Ali.
Hakuri da Hankalin da Iran ta nuna, babban matakin nasarar farko ga muminai.
--------------
Da dama daga mutane (har da wasu yan Shi'a) sun zaci cewar,daga ranar da Amurka ta halaka Janar Qassem Sulaimani Iran zata fara kai hare hare kan Amurkawa da kadarorinsu domin yin ramuwar kisan Janar Sulaimani din.
Amurka ta halaka Janar din ne a ranar Juma'a 3/1/2020 da misalin karfe 2 na daren juma'a a kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin saman Bagadaza (Baghdad) tare da wasu muhimman mutane ciki har da mataimakin kwamnadan PMU Abul Mahdi Almuhandis da kuma mijin 'Yer shi Janar Sulaimani din.
-
Akwai Wani abokina wanda ya bugo min waya tun daga kasar Kanada yake tambayata cewar "shin Iran ta fara kai harin ramuwarta kan Amurka ne? Sai nace masa a'a. Sai yace min wai yaga wasu labarai suna yawo wai ana luguden wuta a barikokin Amurka da sauransu?
-
Sai nace masa a'a bata fara ba.
-
Sai yace min 'to wai me take jira har yanzu bata fara kai harin ramuwar ba?
-
Anan sai nace masa ana maganar tattaro bayanai,da kuma maganar hada jikkunan shahidan da kuma fuskantar yadda za'ayi jana'izarsu da bincika wasiyoyin da suka bari. Tare da tuntubar iyalansu domin samun wasu bayanan su da suka barwa iyalansu.
Duk wadannan na nan cikin litattafan shari'ar musulunci,kuma saba musu,yana cikin sabawa Allah da sabawa ka'idojin addinin musulunci.
-
Sai nace masa " A ka'ida ta hankali da tsaro,idan mutun ya lababo ya kaftara maka adda a cikin duhun dare,kana ya shige cikin duhu ya buya,to bai kamata kai ka bi shi cikin duhun ba. Bari zakayi har sai gari ya waye sai ka ga irin shirk da tanadinsa,kila in kayi sa'a mutane su fito su tayaka a kamashi. Kafin sannan kai kuma kayi magani ga raunin da yayi maka cikin duhun sannan ka sake yi masa shirk da tanadi sosai,sannan sai ka fuskance shi ido na ganin ido.
-
Sai wannan abokin nawa yace min "wallahi na gamsu sosai kuma na kara fahimtar Iran da irin kaifin basirar jagorancin kasar,da kuma yadda suke yin amfani da shari'ar musulunci wajen bibiyar lamuransu.
-
Sai na kara masa da cewa " da ace cikin Daren da lamarin ya faru Iran ta harbo jirgin da ya kai harin ko ta harbi daya daga cikin barikokin Amurka,to da sun murguda labarin da cewar, Iran ce tayi takalar,kuma kila da sun kai hari wuraren da Trump ya ambata cewar zasu kai hari. Kuma kila sune ma da kansu suka fara yin wancan luguden da kake magana akai,domin su kafa hujja. Kuma kila hakan yana cikin ajandarsu tun farko.
-
Sannan da har yanzu ba'a kai ga samu damar yi wa Janar Sulaimani da sauran shahidan sallah da jana'iza ba,kuma koda an samu yar damar yin sallar,da ba'a tara irin wannan jam'ar da tausayawar ba.
Kuma da yanzu Allah ne kadai ya san halin da duniyar nan take ciki game da halin yaki.
Amma matakan jinkirin,hankali,shari'a wanda Iran din ta dauka sai ya kara sama mata goyon bayan al'ummar Iran da duniya, ciki har da mutanen Amurka, Turai da kasashen larabawa. Kuma hakan sai ya mayar da Amurka cikin zullumi da kariyar kai,sannan yan kanzaginta sun shiga damuwa ainun na rashin sanin ta inda Iran din zata bullo musu.
-
Kafofin sadarwar da Saudiya ta biyasu kudade masu yawa domin yin farfaganda kan Iran da Janar Sulaimani,duk sai suka yi kwantai,aka jika musu aiki,aka jefasu kogin nadama da hasara.
Wannan shi ne amfanin addini ga mai addini,da kuma bambancin mai addini da kuma mara addini sin.
Sai abokina yayi min godiya,muka yi addu'a sannan muka yi sallama.
-
Nasir Isa Ali

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky