KALAMAN AISHA DIKKO: Wasu 'yan uwa sun ja kunne gami da nasiha.

KALAMAN A'ISHA DIKKO: Wasu ba'alin 'Yan uwa Musulmi Almajiran Shaikh Zakzaky sun yi gargadi tare da Nasihantar Kwamishiniyar Shari'a ta Kaduna,Aisha Dikko.

Ga abin da suke cewa kamar haka:

"A'isha Dikko! Ya kamata ki shiga taitayinki sosai akan al'amarin Jagoranmu Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).

Kila ke kina da Uba, kina da miji ma kila, kila kuma kina da 'ya'ya, kuma kina da rai kina son ranki, kina bukatar ki cigaba da cin duniya ko?

Kila kina da dan ragowar mutumci a idon wanda suke ganin irinku da mutunci kuma."

Sun ci gaba da cewa:

"Muna miki nasiha kan ki yi kokarin ganin baki biyewa su Elrufa'i akan zaluncin da suke wa Shaikh Zakzaky ba. Kar ki yarda ki saka kanki a cikin Baqin Littafin makasan mutum fiye da 1,000 da Sojojin Nijeriya suka kashe a Zariya a shekarar 2015.

Ki yi kokarin ganin baki nuna hannunki a cikin umurnin Elrufa'i na bizne daruruwan gawarwakin yan uwammu Musulmi a ramin bai daya a garin Mando ba."

Sun kara da cewa:

"Kar ki yarda sunanki ya bayyana a cikin masu hannu wajen tsare Shaikh Ibraheem Zakzaky bayan an dira a gidansa an kashe almajiransa an kona gidan, an kama shi an harbi Yayansa a gabansa, an kashe yayarsa a kan Idonsa, an ja shi an tafi da shi ba."

Daga Karshe sun kuma ce:

"A'isha Dikko, ki kiyayi kanki da bayyana cikin masu hannu a tsare Shaikh Zakzaky da kashe almajiransa a tsawon shekaru hudun nan. Ki wa kanki kiyamul-laili wan-nahari kan zama daga cikin masu hannu a yunkurin kashe Shaikh Zakzaky a cikin gidan kurkuku ko da sunan wata tsiya wai shari'ar da ku kanku ba mutunta kuke yi ba.

Wallahi ki janye daga ciki, ki bar fasikai, fajirai, tsinannun masu gidanki su cigaba da rike garwashin da suka debo. Shaikh Zakzaky jan layin rayuwar al'umma ne, akwai bukatar ki kiyaye sosai."

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky