SHAWARA GA 'YAN MATA- Sheikh Yaqub Yahya katsina

SHAWARA GA 'YANMATA: '...Yan Mata Su Nisanci Karbar Kudi A Hannun Samari' - Shaikh Yakubu Yahaya.

Daga Auwal Isa Musa.

A wata 'yar gajeruwar shawara da ya ba Matasa Mata da yazo a kan wata ga6a a cikin karatun Tarbiyya da yake gabatarwa Matasa 'yan Uwa Musulmi Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky na Mako-Mako a gidansa da ke Katsina,duba da yadda ake samun gur6atar Tarbiyya da kuma Mu'amala Marar kyau tsakanin Samari da 'yan Mata a wannan Shu'umin Zamani, Shaikh Yakubu Yahaya Katsina, ya an karar da 'yan Mata wani abu da ba su dauke shi bakin komai ba amma shi ne d'an Ba da ke kai su ga fadawa tarkon Shaidan da shaidanun Samari.

A lokacin da yake an karar da su wannan Matsalar,Shaikh Yakubu Yahaya yace, ita Mace tana da wani abu a rayuwar; wanda ke ba ta shi ne nata.

Ya ci gaba cewa,shiyasa idan ka cire Mahaifin Mace,ko yayanta,ko 'Kanenta,ko Kane da Wan Uba,ko Kane da Wan Uwa da sauran Muharramanta,to, ba a yarda Saurayi ya dauki Kudi ya ba wa Mace haka diddan ba don kawai yana Son ta.

Da ya koma ga 6angaren Samarin su ma,nan ma,Shehin Malamin ya gargade su da daukar Kudi su ba wa Mace don suna sonta,in ma har za su yi hakan,to,lazim ya kasance a gidansu yarinyar an san da haka,an kuma san da wane dalili suka ba ta,ba haka nan kara-zube ba.

Bugu da kari Malamin ya kuma ce,Kudin da Shara'a ta yi bayani a ba wa Mace su ne; Kudin Sadaki.Saboda haka ya ce: "Akwai bukatar 'yan Mata su nisanci Kar6ar kudi a Hannun Samari"

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky