TARON MANYAN MALAMAN HAUZA AKAN WAYE EL'ZAKZAKY?
Taron manyan Malaman
Hauza da Dalibai kan kira a
saki Malam [H] a Tehran
GAGARUMIN GANGAMIN MANYAN
MALAMAN HAUZA DA DALIBAI NA YANKIN
TEHRAN-IRAN
_Karkashin kulawar Ayatullahi Aliy Akbar
Rashad._
*Wan nan wani sako ne na Musamman da
yafi shafar ‘yan’uwa almajiran Sayyid
Zakzakiy (H)*
Laraba:
5/Jimada Ula/1441
11/10/1398 Shamsiyya
1/1/2020. Miladiyya,
Kamar yadda aka saba gabatar da
Tarurruka, Gangami da sauran
Zamammaki don kiran a saki Jagoran
Harkar Musulunci na Najeriya Sayyid
Ibrahim Zakzaky (H) a Jamhuriyyar
Musulunci ta Iran, yau ma dimbin Malamai
da Dalibai ne na yenkin Tehran, suka
gabatar da Taro danagane da halin da
Sayyid din yake ciki .
Taron ya samu halartar _Sayyida Suhailat
Ibrahim Zakzaky_
GABATARWA.
Malami mai gabatarwa ya bayyana cewa,
taron yana kunshe da Wata farkawa ta
Malaman Hauza, don nuna cewa Sayyid
Zakzakiy (H) bashi kadai ba ne; Maraji’ai,
Malamai, da Daliban Hauza, suna tare da
shi.
kasantuwar da basu da masaniya dangane
da Malama (H), kuma basu san da’awar
sa ba, amma yanzu sun fahimci cewa
ashe shiukar da Imam Khomainiy (Qs) ya
yi ce ta tsiro a Afika, har ta girma basu an
kara ba, don haka bzasu bari Malam (H)
ya zama shi kadai ba. Suna rokon Allah ya
yafe musu kura-kuran da suka yi abaya,
na rashin bibiyar lamarin sa.
Mai gabatarwan wanda yake Malami ne
mai farin rawani, ya karanata Sakon
gaisuwa da jinjina ga Jagoran duniya
Sayyid Zakzakiy (H), -inji shi- a madadin
duk Malaman Hauza na Yenkin Babban
birnin na Tehran, wadan suka halarta da
ma wadan da wani Uzrin ya tsare su basu
samu zuwa ba. *Dakin Taron make yake
fal da Malamai masu rawani!.*
JAWABIN SAYYIDA SUHAILA.
Sayyida Suhaila ta gabatar da Malama
Badiyyah, don ta yi bayani cikin Harshen
Farisanci, game da hali da yanayin da su
Sayyid (H) Suke ciki ahalin yanzu.
Ganin ido ya tabbatar da Malamai “Sadat”
watan Sharifai wadan da suka kai
matsayin Ijtihadi da sauran manyan
Malamai, wadan da suma Sun kai
mukamin Ijtihai a tsarin Hauza, suna zubar
da hawaye don yadda suka ji wahalar da
Azzalumai suke ba dan’uwan su Malamin
Addini Allamah Sayyid Zakzakiy (H) daga
bakin Malama Badiyya.
Alokaci guda Kungiyoyin Dalban Jami’a na
Babban Birnin Tehran, suma suna can
wani babban Dakin taro nasu, suna zaman
nazari dangane da da’awar Jagora da
matakan da Azzalumai da munafukan
duniya suke dauka. Tunani suke da nazari
akan cewa wai *meke faruwa ne
Dawagitan duniya da munafukai suak lashi
takobin sai sun ga bayan Sayyid Zakzakiy
(H) da da’awar sa.*
*Ayatullahi Aliy Akbar Rashad (H) Tehran,
ya suffanta Malama Zeenah ta fuskacin
dakekwa da Sayyida Zahra, yayin da ta
dake ta kare Manzon Allah (saww), ya ce
wan nan dakewar da Malama Zinah ta yi
tare da Jagoran Addini Jarunta ce irin ta
Sayyida Zahra (as).*
Ya kuma suffata su Sayyida Suhaila a
wannan Jaular da suka gabatar, ta kusan
mako guda, inda suka ziyarci kusan
dukkan Fitattun Manyan Maraji’ai a Birnin
Qom Al muuqaddasah zuwa Birnin Teharn,
da cewa su ne Zainabawan wannan
Zamanin, kamar yadda Sayyida Zainab ta
yi Jaular yada mazlumiyar waki’ar Ashura,
kuma aikin su ya nuna cewa har yanzu
akwai zainabawa da kuma aikin Sayyida
Zainaba (as).
JAWABIN DR. ALIY RIZA FANAHIYAN.
Hujjatul Islam Fanahiyan, ya bayyana
cewa, Rashin Taimakawa Sayyid Zakzaki
ta fuskacin shimfida yanayin da zai
tursasa Azzalumai su saki shi, zai iya jawo
rushewar Nizamin Musulunci na Iran,
wanda a halin yanzu yake da karfin gaske.
Ya kara da cewa nuna halin ko – in – kula
akan lamarin Sayyid Zakzakiy (H), zai iya
jawoma dukkan kasashen Musulmi
kaskanci da dawwama cikin danniyar
kurayen duniya, masu rarraba duniya don
su ci riba da kwashe arzikin kasashen
Musulmi.
Fanahiyan ya karanta wani sashe na fikirar
Imam Komaini (R), wanda yake nuna
wazifar Malamai da Daliban Addini, cewa
wajibi ne su yi tunani akan samuwar
Babbar daular Musulunci ta duniya, dole ne
karatu da nazarin littafai da fafutukar Gwa-
gwarmaya da ake ta faman yi ayau, su
maida hankali akan janye iyakokin da
makiya suka shata, don rarraba duniya da
zaluntar al ummar Musulmi baki daya.
Shahararren Malamin Dr. Fanahiyan ya
kara da cewa, a gaskiya mu daliban addini
a kasashen Musulmi mun yi abin kunya
sosai, ta yadda muka rabu da Shekh
Zakzakiy (H) muka kyale shi, har takai
yanzu gashi yana lunfashin da yayi kama
da na karshe, yana neman ya yi bankwana
da mu, dole ne mu farka mu yi abin da ya
dace akan wan nan bawan Allah (Sayyed
Zakzaky).
Dr. Fanahiyan ya cigaba da cewa, ba dai-
dai ba ne, Daliban Addini su maida hankali
kawai akan karatu da nada Rawunna, su
kyale tafarkin muqawama bata da
ma’aikata, ya ce ba daidai ba ne, Malamai
su bar Sheikh (H), a matsayin cewa shi na
Nigeria ne, wannan rashin fahimta ne,
Sheikh Zakzaky ya fi karfin ace ma na
Afrika ne, aikin sa na duk duniyar
Musulunci ne, kuma ya wajaba ga
Malaman duniyar Musulunci su farka tun
kafin su rasa wanda ya kafa musu
harsashen gini mai karfi, su taimaka masa,
suma suyi aiki da wazifar su.
An kammala Zaman tare da Yima Jagora
addu’o’I da Kuma jaddada kira ga Malamai
da Dalibai da duk Al’ummar Musulman
duniya da su tashi tsaye da addu’o’i, da
duk abin da zasu iya yi don ganin Jagora
Sayyid Zakzakiy (H) ya samu Yanci.
MURYAR MALAMAN MU
*VOICE OF SHEIKH*
Hauza da Dalibai kan kira a
saki Malam [H] a Tehran
GAGARUMIN GANGAMIN MANYAN
MALAMAN HAUZA DA DALIBAI NA YANKIN
TEHRAN-IRAN
_Karkashin kulawar Ayatullahi Aliy Akbar
Rashad._
*Wan nan wani sako ne na Musamman da
yafi shafar ‘yan’uwa almajiran Sayyid
Zakzakiy (H)*
Laraba:
5/Jimada Ula/1441
11/10/1398 Shamsiyya
1/1/2020. Miladiyya,
Kamar yadda aka saba gabatar da
Tarurruka, Gangami da sauran
Zamammaki don kiran a saki Jagoran
Harkar Musulunci na Najeriya Sayyid
Ibrahim Zakzaky (H) a Jamhuriyyar
Musulunci ta Iran, yau ma dimbin Malamai
da Dalibai ne na yenkin Tehran, suka
gabatar da Taro danagane da halin da
Sayyid din yake ciki .
Taron ya samu halartar _Sayyida Suhailat
Ibrahim Zakzaky_
GABATARWA.
Malami mai gabatarwa ya bayyana cewa,
taron yana kunshe da Wata farkawa ta
Malaman Hauza, don nuna cewa Sayyid
Zakzakiy (H) bashi kadai ba ne; Maraji’ai,
Malamai, da Daliban Hauza, suna tare da
shi.
kasantuwar da basu da masaniya dangane
da Malama (H), kuma basu san da’awar
sa ba, amma yanzu sun fahimci cewa
ashe shiukar da Imam Khomainiy (Qs) ya
yi ce ta tsiro a Afika, har ta girma basu an
kara ba, don haka bzasu bari Malam (H)
ya zama shi kadai ba. Suna rokon Allah ya
yafe musu kura-kuran da suka yi abaya,
na rashin bibiyar lamarin sa.
Mai gabatarwan wanda yake Malami ne
mai farin rawani, ya karanata Sakon
gaisuwa da jinjina ga Jagoran duniya
Sayyid Zakzakiy (H), -inji shi- a madadin
duk Malaman Hauza na Yenkin Babban
birnin na Tehran, wadan suka halarta da
ma wadan da wani Uzrin ya tsare su basu
samu zuwa ba. *Dakin Taron make yake
fal da Malamai masu rawani!.*
JAWABIN SAYYIDA SUHAILA.
Sayyida Suhaila ta gabatar da Malama
Badiyyah, don ta yi bayani cikin Harshen
Farisanci, game da hali da yanayin da su
Sayyid (H) Suke ciki ahalin yanzu.
Ganin ido ya tabbatar da Malamai “Sadat”
watan Sharifai wadan da suka kai
matsayin Ijtihadi da sauran manyan
Malamai, wadan da suma Sun kai
mukamin Ijtihai a tsarin Hauza, suna zubar
da hawaye don yadda suka ji wahalar da
Azzalumai suke ba dan’uwan su Malamin
Addini Allamah Sayyid Zakzakiy (H) daga
bakin Malama Badiyya.
Alokaci guda Kungiyoyin Dalban Jami’a na
Babban Birnin Tehran, suma suna can
wani babban Dakin taro nasu, suna zaman
nazari dangane da da’awar Jagora da
matakan da Azzalumai da munafukan
duniya suke dauka. Tunani suke da nazari
akan cewa wai *meke faruwa ne
Dawagitan duniya da munafukai suak lashi
takobin sai sun ga bayan Sayyid Zakzakiy
(H) da da’awar sa.*
*Ayatullahi Aliy Akbar Rashad (H) Tehran,
ya suffanta Malama Zeenah ta fuskacin
dakekwa da Sayyida Zahra, yayin da ta
dake ta kare Manzon Allah (saww), ya ce
wan nan dakewar da Malama Zinah ta yi
tare da Jagoran Addini Jarunta ce irin ta
Sayyida Zahra (as).*
Ya kuma suffata su Sayyida Suhaila a
wannan Jaular da suka gabatar, ta kusan
mako guda, inda suka ziyarci kusan
dukkan Fitattun Manyan Maraji’ai a Birnin
Qom Al muuqaddasah zuwa Birnin Teharn,
da cewa su ne Zainabawan wannan
Zamanin, kamar yadda Sayyida Zainab ta
yi Jaular yada mazlumiyar waki’ar Ashura,
kuma aikin su ya nuna cewa har yanzu
akwai zainabawa da kuma aikin Sayyida
Zainaba (as).
JAWABIN DR. ALIY RIZA FANAHIYAN.
Hujjatul Islam Fanahiyan, ya bayyana
cewa, Rashin Taimakawa Sayyid Zakzaki
ta fuskacin shimfida yanayin da zai
tursasa Azzalumai su saki shi, zai iya jawo
rushewar Nizamin Musulunci na Iran,
wanda a halin yanzu yake da karfin gaske.
Ya kara da cewa nuna halin ko – in – kula
akan lamarin Sayyid Zakzakiy (H), zai iya
jawoma dukkan kasashen Musulmi
kaskanci da dawwama cikin danniyar
kurayen duniya, masu rarraba duniya don
su ci riba da kwashe arzikin kasashen
Musulmi.
Fanahiyan ya karanta wani sashe na fikirar
Imam Komaini (R), wanda yake nuna
wazifar Malamai da Daliban Addini, cewa
wajibi ne su yi tunani akan samuwar
Babbar daular Musulunci ta duniya, dole ne
karatu da nazarin littafai da fafutukar Gwa-
gwarmaya da ake ta faman yi ayau, su
maida hankali akan janye iyakokin da
makiya suka shata, don rarraba duniya da
zaluntar al ummar Musulmi baki daya.
Shahararren Malamin Dr. Fanahiyan ya
kara da cewa, a gaskiya mu daliban addini
a kasashen Musulmi mun yi abin kunya
sosai, ta yadda muka rabu da Shekh
Zakzakiy (H) muka kyale shi, har takai
yanzu gashi yana lunfashin da yayi kama
da na karshe, yana neman ya yi bankwana
da mu, dole ne mu farka mu yi abin da ya
dace akan wan nan bawan Allah (Sayyed
Zakzaky).
Dr. Fanahiyan ya cigaba da cewa, ba dai-
dai ba ne, Daliban Addini su maida hankali
kawai akan karatu da nada Rawunna, su
kyale tafarkin muqawama bata da
ma’aikata, ya ce ba daidai ba ne, Malamai
su bar Sheikh (H), a matsayin cewa shi na
Nigeria ne, wannan rashin fahimta ne,
Sheikh Zakzaky ya fi karfin ace ma na
Afrika ne, aikin sa na duk duniyar
Musulunci ne, kuma ya wajaba ga
Malaman duniyar Musulunci su farka tun
kafin su rasa wanda ya kafa musu
harsashen gini mai karfi, su taimaka masa,
suma suyi aiki da wazifar su.
An kammala Zaman tare da Yima Jagora
addu’o’I da Kuma jaddada kira ga Malamai
da Dalibai da duk Al’ummar Musulman
duniya da su tashi tsaye da addu’o’i, da
duk abin da zasu iya yi don ganin Jagora
Sayyid Zakzakiy (H) ya samu Yanci.
MURYAR MALAMAN MU
*VOICE OF SHEIKH*
Comments
Post a Comment