ZAMU HADA KAI DA IRAN DOMIN MUYAƘI AMURIKA-Banizuwala

Zamu hada kai da Iran wajen yakar Amurka (Banizuwala)
-
Kasar banizuwala (Venezuela) ta nuna goyon bayanta ga kasar Iran.
---Ministan tsaron kasar Banizuwala Gen. Vladimir Padrino Lopez ya tsine wa kasar Amurka bisa ta'addancin kashe shugaban masu yaki da yan ta'addan duniya,Laftana Janar Qassem Sulaimani,sannan ya yabawa Iran bisa kakkausar matakin martanin da ta dauka kan Amurkan. Janar Lopez ya bayyana harin da Amurka ta kai wa Janar Sulaimani da cewar'ta'addanci ne tsaba.
-
 Janar Lopez ya bayya wa ministan tsaron Iran,Janar Hatami ta wayar tarho cewar, da shi da mutanen Banizuwala suna mika jajensu tare da goyon bayansu ga kasar Iran,sannan suna yin Allah wadarai da Amurka da ta'addancinta.
Ya bayyana harin da Amurka ta kai wa Janar Sulaimani da cewar,zafi Amurkan taji na cewar Sulaimani ya kawo karshen yaranta yan ISIS,don haka bari ta daukar musu fansa.
Janar Padrino Lopez ya bayyana Janar Qassem Sulaimani da cewar 'mutumin kirki ne jarimin mara tsoro,kuma abin koyi ga sauran sojoji. Yace bayan kashe shi sai gashi nan wasu dubban Qassem Sulaimani din sun bayyana.
-
A madadin rundunar sojan Banizuwala, muna mika jaje da ta'aziyarmu gareku da kuma mutanen Iran baki daya. Zamu hada kai da Iran domin yakar Amurka da yan ta'addanta a duniya.
-
A nasa bangaren,Ministan tsaron Iran Janar Hatami ya gode wa Janar Padrino Lopez a madadin jumhuriyar musulunci ta Iran,ya nemi da ya Isar da sakon gaisuwar Iran ga shugaban Banizuwala (commandante) da al'ummar Banizuwala.
-
Nasir Isa Ali

Kanada labarin da kakeso asanya maka a wan'nan shafin? Maza ka tuntubemu ta email din mu.voiceofsheikh@gmail.com

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky