DANGANE DA WATAN RAJAB

*DANGANE DA WATAN RAJAB*


*Daga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)*

Rajab, idan mutum ya duba Mafatihul Jinan, a
yayin da yake kawo ayyukan shekara ya fara
da watan Rajab ne. Yana cewa; shi ne kamar
watan farko a ayyuka.

 Rajab, Sha’aban,
Ramadan, watanni masu ayyuka na ibada.
Saboda haka ya kamata mutum ya yi shirin
shiga Rajab.

Akwai ayyuka na musamman na daren farko
na Rajab. Kar mutum ya yi sake. Daren farko
da kuma, musamman azumin farkon Rajab din.

Ya tashi da azumi daya ga watan Rajab. Da
Rajab da Sha’aban da Ramadan, watanni ne
masu darajar gaske.

An samo hadisai daban-daban a kan
falalolinsu. A cikin Ikbal A’amal, na ga shi
Sayyid bn Dawus ya kawo wani dogon magana
a kan cewa; ka sani dangane da falala an
samo ruwayoyi da yawan gaske. To, ko da a
‘ka’idatul man balagah’. Idan ka san wata
ka’ida ana ce ma ta ‘ka’idatul man balagah,’
hadisi ne aka samu daga A’imma daban-
daban ma.

An samu daga Imam Bakir da Imam Ja’afar da
Ai’mma (AS) daban-daban cewa; idan ruwaya
ta zo maka dangane da wani aikin alheri, in ka
aikata, kana da ladan wannan abin da ka ji an
gaya maka din, ko da ba haka Annabi ya fada
ba. Saboda ita falalar Allah tana da yawan
gaske.

Wato a babin falala ana amfani da hadisi, ko
da bai inganta ba, ko da mai rauni ne. Hadisin
da ba za a yi amfani da shi ba a babin falala
kawai shi ne, ya tabbata kirkirarre ne. Hadisi
Maudu’i, za a iya amfani da shi? Sam! Amma
hadisi mai rauni, ba wani damuwa. In dai ya ce;
wanda ya karanta kaza, za a ba shi kaza.

Khalas! Karanta kawai, insha Allahu ka ma
samu ka gama.
Saboda Allah (T) abin da yake da shi yana da
yawan gaske.

Bisa yalwar Rahamarsa zai ba
ka wannan din. Yawwa! In dai aka samu
ruwayar. Ballantana mu muna da ruwayoyi ma,
wadanda suke ba a babin ‘ka’idu man balagah’
ba. Ainihin ma sun inganta ne ruwayoyin.

To, hatta ko ba su inganta ba a babin falala.
Don wasu ka ga ni ban san abin da ya same su
ba, da zaran watan wannan Azumin ya kama,
su kuma sun fara wa’azi ke nan, kar a yi
azumi. Wai azumin ana ce masa na tsofaffi.

Wannan azumi ne na tsoho? Sun fara wannan
abin ke nan. Ye-ye-ye, su yi ta ihu. Wai a
daina yi. Wai Annabi bai yi ba.
Kuma sai su zo su ce; to, Annabi bai yi Rajab
ba dai, amma ya yi Sha’aban.

To, su kuma ba
za su yi Rajab din ba, ba za su yi Sha’aban din
ba. Amma sun dunga ke nan, suna cewa
wadansu mutane sun kirkira ma kansu, suna
yin azumin wata uku. Duk wanda ya yi haka
nan, ya sabi Allah.

 Annabi bai taba wata uku
yana azumi ba.
To, ‘falyakun’. Wa ya ce maka azumin ba kyau
ne? Da Annabin bai yi ba, sai ya ce maka kada
ka yi? Uhm? Da kake shan fura da nono, Annabi
ne ya sha Fura da nono din? Da kake cin tuwo
miyar kuka din nan, shi ma Annabi ne ya ci?
To, ya ce maka kada ka ci ne? Ehen! Cewa
Annabi bai yi ba, ba shi ne magana ba. Annabi
ya ce; kada a yi?
To, ballantana an samu ruwaya.

Su suna da
ruwayar cewa; Annabi ya kasance ya kan yi
azumin Sha’aban duk cikarsa, ya sada shi da
Ramadan. Amma ba dayansu da zai yi. Yana
nan yana sukan kar a yi Rajab. Amma Annabi
yana Sha’aban. To, tunda yana sukar kar a yi
Rajab, sai ya bar Rajab din, sai ya yi mene? Sai
ya yi Sha’aban din.

 Amma ba zai yi wannan ba,
ba zai yi wancan ba. To, wannan buzines dinsu
ne. Su suka dauka ma kansu.

An ruwaito Manzon Allah (S) yana cewa; Rajab
watan Allah ne, Sha’aban watana, Ramadan
kuma watan al’ummata. Yana cewa; “wanda ya
yi azumin yini guda na Rajab, zai cancanci
yardar Allah. Kuma za a nesanta fushin Allah
gare shi. Za a dode masa kofa daga kofofin
wuta.”

Daga Imam Musa bn Ja’afar (AS) yana cewa,
“wanda ya azumci yini guda na Rajab, wuta za
ta yi nesa da shi shekara guda. Wanda ya yi
azumin kwana uku a Rajab, Aljanna ta wajaba
gare shi.”

To, ga su nan dai (ruwayoyi daban-
daban).
Akwai kuma ruwayar da ke cewa; “shi Rajab
din nan wata korama ce a Aljanna, ta fi nono
fari ta fi zuma zaki. Wanda ya azumci yini guda
na Rajab, Allah zai shayar da shi daga wannan
korama din.” Ga su nan, ga su nan, ruwayoyi
daban-daban.

Saboda haka mutum ya fara
kaimi. Insha Allahu ya shiga Rajab da ayyuka
na alheri da tuba ya zuwa ga Allah.
Wasallallahu Ala Muhammadin wa’alihid
dahirin.

*Shaikh Zakzaky (H)*
ya yi wannan jawabin a
karshen watan Jimadal Thani, a shekarun baya
a Husainiyya Baqiyyatullah.

Saifullahi M. Kabir Ya Naqalto Muku.
voiceofsheikh@gmail.com Ga wanda ke buƙatar Aiko mana da Wa'azi ko karantarwa ta hanyar rubutu ko video ko Oudio na malamai daban daban akowane fanni sai ya tintubemu ta Email din mu, idan karantarwar tayi daidai da ƙa'idojin shafin, Zamu sanya Insha Allah. Munagodiya.

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky