Hana Bara Ko Almajiranci: Shaikh Yakubu Yahaya Katsina Ya Maganta Tare Da Ba da Mafita Akan Haka.

A cikin wasu Jawaban Maulidai da shahararren Malamin Addinin Musuluncin nan kuma wakilin 'yan uwa musulmi Almajiran Ibraheem Alzakzaky da ke a Jihar Katsina,Shaikh Yakubu Yahaya ya yi a kwanakin baya a loacin da aka soma rufe wasu makarantun horo da gyara tarbiya a Katsina,Daura da Kano bisa zargin ana abubuwan assha a wadannan cibiyoyi,Malamin ya maganta tare da aike wa da sako mai dauke da samar da mafita ga hukumomi akan kokarinsu na dakile bara ko almajiranci a jihohi da ma kasa baki daya.

Duk mabambantan Jawaban nasa,Malamin ya kuma bayyana ra'ayinsa da yadda yake kallon za a magance wannan matsala tsakanin 6angarorin biyu;hukuma da kuma su masu bara ko almajirancin

Ga dai wani yanki na Jawaban nasa da muka gutsuro maku:

“To abin da muke kallon wannan(rufe makarantun Allo) shi ne mukaddima na rufe makarantun Allon duk kasar nan baki daya.Domin yanzu abin da gwamnati ke 6a6atu akan shi shine makarantun allo sun dame su da bara;ba su son bara.

Ba mu ce bara addini ne ya kawo ta ba, ba mu ce bara daidai ne ba;yin bara ba ba daidai ba ne.Amma menene ya sanya musulmi suka zama mabarata?

Ai da can kasar a hannun su(malamai) take.Gidan Malam ake biyawa aci abinci har a dauka akai gida.Da bature yazo ya kar6e komai a hannun Malami,sai Malami ya ga babu abin da zai yi,sai ya koma yana tsare addinin shi,yana bara yana cin abinci yana rayuwa.Wannan shi ne ya haifar da bara.

Saboda haka, idan ana so ayi maganin wannan matsalolin,kamar yanzu wannan makarantu(na mari) da aka rufe.Tun da an san da su tsawon shekaru ba rana tsaka suka bulla ba,abin da gwamnati ya kamata suyi in da suna da hankali sai ta rubuto takarda da   bayanai cewa; Allah gafarta Malam muna ganin abubuwan da ba su dace ba makarantarka, mun ba ka wata uku ka gyara.Haka muke so,da bayanan a ciki.

Sai shi kuma ya duba ya gani idan zai iya gyarawa ya gyara.Idan ba zai iya ba,sai ya sallami kowane yaro yace sai na samu hali na gyara ku dawo saboda ban cika wadanan "conditions" ba. Wannan shi ne abin da ya kamata suyi ian ba har ya kasa ba.Tun da yana amfanar da jama'a. Iyaye ne ke kamo hannun yaransu su kawo.Wasu manyan Daraktoci ne, wasu manya ne, su ne suke dauko yaransu saboda sun gagaresu su kawo su,su kuwa Malamai su kwancesu su koya musu karatun Alkur'ani da Ibada har su zama mutanen kirki.(Malamin Allo) yana amfanar al'ummar Anguwa kuma an sani, a titi ake yi ba a gida ake yi a boye ba.

Idan ana ganin Dakunan da suke kwana yayi kadan wuri kaza da kaza, to shike nan yanzu abin da za ayi sai gwamnati ta taimaka masa da matasai,wasu gidaje ko a ba shi wani fili ayi gini ayi masa azuzuwwa ayi masa komai da komai,sai ace to dawo nan ka ci gaba da karantarwar ka kuma ban da kaza ban da kaza.Sai a rika aiko 'supervisors' su rika bi suna ganin menene ake yi.Wannna shi ne abin da ya kamata gwamnati ta yi kenan.

“Amma tun da 'UNICEF' ta sanyo almajiranci a gaba tana cewa wai akwai mutum miliyan goma sha wani bu ba su da ilimi suna yawo a arewacin Najeriya kaza da kaza, almajirai suke nufi.Har ma nake cewa almajiran allo su shirya ta su tana zuwa, an faro ne domin azo kansu.Wannan shi ne gaskiyar magana.

Amma idan an ce ko ana luwadi da yara, kaje makarantun Boko ka gani menene ba ayi? Nan a ke yin 'lesbian' mata na auren mata,maza na auren maza, 'yan mata da ciki hada ma malamai suna taimakawa.

Kwanan nan ba kuji a BBC an yi ra'ayi riga ba Malaman jami'a suna yi wa dalibansu ciki?

Saboda haka, wannan abin kunyar da ake tuhumar makarantun da shi kaje na gwamnati can ma ana yi. Kaje gidan yari ka ga yadda ake kwanciyar kifi 'siding' iyakar kunci kenan.

Mu ba za mu ba wa gwamnati uzuri ba.Tun da almajiran allo suna da amfani,almajiranci yana da amfani,duk wani limami ko wani babban malami ko wani mashahuri... kaje gidan yari ka kilga ka gani dan fashi da makami da almajirin allo guda nawa ne? masu shaye-shaye almajiran allo guda nawa ne? amma ka tambaya kaji dan Sakandire guda nawa ne wanda ya gama jami'a babu aiki,guda nawa ne?.

Mu ba mu ce makarantun allo su tafi yadda suke ba, amma idan za a kawo gyara da ci gaba ba da karfin tuwo a keyi ba, lallashin mutane ake har su fahimta. Su Malaman a ba su dama su yi magana a Radiyo kamar yadda ake yi da yawunsu mana. Kullum duk mutane sun yi shiru, Malamai da sarakuna kamar an ba wa kowa rashawa domin yayi shiru. Su Iyayen ba su ta6a kai kara ba cewa an cutar da yaransu,amma wani daga nesa saboda 'UNICEF' ba ta son ta ga almajirai.

To azo a inganta makarantun allo mana ayi musu 'Borehole', wajajen karatu, makewayi da tsafta ayi musu Uniform'.

Kaje ka tambaya kaji almajiran allo nawa ne cikin 'yan Boko Haram?”

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky