IBN TAIMIYYA NE JAGORAN ZAGIN SAHABBAI

 IBN TAIMIYYA NE JAGORAN ZAGIN SAHABBAI, KARYATA HADISAN ANNABI MUHAMMAD(SAW), TAJSIM (MAYAR DA ALLAH JIKI)... -  A MAHANGAR KALAMAN AL-BANI, AZ-ZAHABI, IBN HAJAR AL-ASKALANI...


MAFI YAWAN SAHABBAI DA TABI'AI MUNAFIKAI. - A MAHANGAR KALAMAN IBN TAIMIYYA:


IBN TAIMIYYA ZINDIKI (MARAR ADDINI) NE, MUNAFIKI NE... A MAHANGAR MALAMAN AHLUS-SUNNAH. INJI IBN HAJAR AL-ASKALANI:


IBN TAIMIYYA BAI DA AMANAR ILIMI, YA KAN KARYATA HADISAI INGANTATTU... - A MAHANGAR KALAMAN AL-BANI, IBN HAJAR AL-ASKALANI...


Al-bani ya tabbatar da Ibn Taimiyya ya kan karyata hadisai ingantattu. Lokacin da Al-bani ya ke ta'aliki akan hadisi ingantacce, mutawaturi (hadisin Ghadir); wanda Ibn Taimiyya ya karyata, sai Al-bani ya ce:


"Abin mamaki ne sosai, Ibn Taimiyya ya runtse ido; ya yi inkarin (ingancin) hadisin (Ghadir), har ma ta kai ga ya karyata wannan hadisin, a littafinsa (Minhajus-Sunnah, j 4, s 104), kamar yanda (Ibn Taimiyya) ya karyata hadisin da ya gabace shi [wanda Annabi(saw) ya ke cewa: Ali(as) ne shugaban dukan muminai a bayana]. (Al-bani ya ce) ban san dalilin da zai sa Ibn Taimiyya ya karyata wannan hadisi ba, face gaggawa (rashin natsuwa ta ilimi) da wuce gona-da-iri wajen yiwa 'yan Shia raddi, Allah ya gafarta mana da shi (Ibn Taimiyya)":


قال الألباني


فمن العجيب حقا أن يتجرأ شيخ الإسلام ابن تيمية على إنكار هذا الحديث وتكذيبه في "منهاج السنة" (4 / 104) كما فعل بالحديث المتقدم هناك [أن رسول الله(ص) قال لعلي: " أنت ولي كل مؤمن بعدي]. فلا أدري بعد ذلك وجه تكذيبه للحديث إلا التسرع والمبالغة في الرد على الشيعة، غفر الله لنا وله.


- سلسلة الأحاديث الصحيحة وشيء من فقهها وفوائدها : الألباني، ج 5، ص 261 - 264، ح 2223.


Cewar Al-bani yayi: ﻓﻼ ﺃﺩﺭﻱ ﺑﻌﺪ ﺫﻟﻚ ﻭﺟﻪ ﺗﻜﺬﻳﺒﻪ ﻟﻠﺤﺪﻳﺚ ﺇﻻ ﺍﻟﺘﺴﺮﻉ ﻭﺍﻟﻤﺒﺎﻟﻐﺔ (ban san dalilin da zai sa Ibn Taimiyya ya karyata wannan hadisi ba, face gaggawa (rashin natsuwa ta ilimi) da wuce gona da iri...), hakan ya na tabbatar da; Ibn Taimiyya ko dai jahilin ilmin Hadisi ne ko mai tsaninin son rai akan Hadisai, ko mai tsananin kin Imam Ali(as), hakan ne kadai zai sa Ibn Taimiyya ya runtse ido ya karyata mutawaturin hadisi.


Abinda ya bawa Al-bani mamaki shine; Ibn Taimiyya ya karyata hadisin ba tare da hujja ingantatta daga ilimin hadisi ba.


Al-bani ya tabbatar da Ibn Taimiyya ya yi babban zunubi ta hanyar karyata ingantaccen hadisin Ghadir, hakan ya sa Al-bani ya ce; ﻏﻔﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻨﺎ ﻭﻟﻪ [Allah ya gafarta mana da shi (Ibn Taimiyya)].


Ibn Taimiyya ya karyata hadisin Ghadir, wai hadisin Ghadir sam bai da asali, doriya akan da'awar hadisin bai zo a littattafai ingantattu ba, wai wasu malamai ('yan kadan) ne su ka riwaito shi, wai ma akwai sabani akan ingancin hadisin:


قال بن تيمية:


قَوْلُهُ: مَنْ كُنْتُ مَوْلَاهُ فَعَلِيٌّ مَوْلَاهُ. فليس هو فِي الصِّحَاحِ، لَكِنْ هُوَ مِمَّا رَوَاهُ الْعُلَمَاءُ، وَتَنَازَعَ النَّاسُ فِي صِحَّتِهِ...


...وَأَمَّا من كُنْتُ مَوْلَاهُ فَعَلِيٌّ مَوْلَاهُ فَلَا يصح مِنْ طَرِيقِ الثِّقَاتِ أَصْلًا. 


- منهاج السنة النبوية : ابن تيمية : الفصل الثالث في الأدلة الدالة على إمامة علي(ر) بعد رسول الله(ص) : الثاني حديث الغدير، ج 7، ص 319 - 320.


Az-Zahabi ya karyata Ibn Taimiyya; yayinda ya tabbatar da hadisin Ghadir Sahihi ne, hasalima mutawaturi ne, (ba shakka akan ingancinsa):


...فقال: كنا بالجحفة بغدير خم... فخرج علينا رسول الله(ص)... فأخذ بيد علي(ر) فقال: من كنت مولاه فعلي مولاه. (قال الذهبي) هذا حديث حسن عال جدا، ومتنه فمتواتر.


- سير أعلام النبلاء : الذهبي، ج ٨، ص ٣٣٤ - ٣٣٥. تاريخ الوفاة : ٧٤٨. تحقيق : إشراف وتخريج : شعيب الأرنؤوط / تحقيق : نذير حمدان. الطبعة : التاسعة. تاريخ النشر : ١٤١٣ - ١٩٩٣ م. مؤسسة الرسالة بيروت.


Kadan daga cikin malaman Ahlus-sunnah da su riwaito Hadisin Ghadir: Tirmizi, Hadisi mai numba 3713, Nasaa'i, Hadisi mai numba 8089, Ibnu Majah, Hadisi mai numba 121, Ahmad a Musnad, Hadisi mai numba 18,502, Al-Bazzar Hadisi mai numba 4298, Abu Ya'ala Hadisi mai numba 567, Al-Haakim Hadisi mai numba 4577, At-Tabraani Hadisi mai numba 2977, Ibnu Abi Shaibah Hadisi mai numba 23,737. Al-baani ya inganta a Al-Jaami'us Sagir Wa Ziyaadaatih : 11,469...


MAFI YAWAN SAHABBAI DA TABI'AI MUNAFIKAI NE - A MAHANGAR KALAMAN IBN TAIMIYYA.


IBN TAIMIYYA YA NA CEWA:


"MAFI YAWAN SAHABBAI DA TABI'AI BA SA SON IMAM ALI(AS); HASALIMA ZAGINSA SU KE":


قال ﺍﺑﻦ ﺗﻴﻤﻴﺔ:


"...ﺃﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻗﺪ ﺍﺧﺒﺮ ﺍﻧﻪ ﺳﻴﺠﻌﻞ ﻟﻠﺬﻳﻦ ﺁﻣﻨﻮﺍ ﻭ ﻋﻤﻠﻮﺍ ﺍﻟﺼﺎﻟﺤﺎﺕ ﻭﺩﺍ ... ﻭ ﻟﻢ ﻳﻜﻦ ﻛﺬﻟﻚ ﻋﻠﻲ ﻓﺎﻥ ﻛﺜﻴﺮﺍ ﻣﻦ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﻭ ﺍﻟﺘﺎﺑﻌﻴﻦ ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻳﺒﻐﻀﻮﻧﻪ ﻭ ﻳﺴﺒﻮﻧﻪ ﻭ ﻳﻘﺎﺗﻠﻮﻧﻪ..."


- ﺍﺑﻦ ﺗﻴﻤﻴﺔ : ﻣﻨﻬﺎﺝ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺍﻟﻨﺒﻮﻳﺔ : ﺍﻟﻔﺼﻞ ﺍﻟﺜﺎﻟﺚ ﻓﻲ ﺍﻷﺩﻟﺔ ﺍﻟﺪﺍﻟﺔ ﻋﻠﻰ ﺇﻣﺎﻣﺔ ﻋﻠﻲ(ﺭ) ﺑﻌﺪ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ(ص)؛ ﺍﻟﻤﻨﻬﺞ ﺍﻟﺜﺎﻧﻲ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﺮﺍﻓﻀﻲ ﻓﻲ ﺍﻷﺩﻟﺔ ﻣﻦ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ ﻋﻠﻰ ﺇﻣﺎﻣﺔ ﻋﻠﻲ(ﺭ)؛ ﻓﺼﻞ ﺍﻟﺒﺮﻫﺎﻥ ﺍﻟﺜﺎﻧﻲ ﻋﺸﺮ... : ﻣﻜﺘﺒﺔ ﺍﺑﻦ ﺗﻴﻤﻴﺔ : ﺳﻨﺔ ﺍﻟﻨﺸﺮ 1406 : ﻫـ / 1986 ﻡ : ﻋﺪﺩ ﺍﻷﺟﺰﺍﺀ : ﺗﺴﻌﺔ ﺃﺟﺰﺍﺀ : ﺝ 5 / ﺹ 42.


Ko dai Ibn Taimiyya makaryaci ne, karya ya yiwa Sahabbai da Tabi'ai; ko kuma mafi yawan Sahabbai da Tabi'ai Munafikai ne.


Idan aka ce; da yawa daga cikin Sahabbai su na kin Imam Ali(as), (kamar yanda Ibn Taimiyya ya ce), hakan daidai ya ke da a ce da yawa daga cikin Sahabbai Munafikai ne, Saboda ya inganta Annabi Muhammad(saw) ya na cewa da Imam Ali(as):


"Babu mai Sonka sai Mumini, babu mai kinka sai Munafiki":


"لَا يُحِبَّنِي إِلَّا مُؤْمِنٌ، وَلَا يُبْغِضَنِي إِلَّا مُنَافِق"


Ga nassin hadisin kamar yanda Muslim, Tirmizi, Ahmad Bin Hambal... su ka ruwaito:


حَدَّثَنَا  أَبُو بَكْرِ بْنُ أَبِي شَيْبَةَ، حَدَّثَنَا  وَكِيعٌ،  وَأَبُو مُعَاوِيَةَ، عَنِ  الْأَعْمَشِ  ح وَحَدَّثَنَا  يَحْيَى بْنُ يَحْيَى، وَاللَّفْظُ لَهُ، أَخْبَرَنَا  أَبُو مُعَاوِيَةَ، عَنِ  الْأَعْمَشِ، عَنْ  عَدِيِّ بْنِ ثَابِتٍ، عَنْ  زِرٍّ، قَالَ: قَالَ: عَلِيٌّ   وَالَّذِي  فَلَقَ  الْحَبَّةَ، وَبَرَأَ  النَّسَمَةَ  إِنَّهُ لَعَهْدُ النَّبِيِّ الْأُمِّيِّ(ص)َ إِلَيَّ أَنْ لَا يُحِبَّنِي إِلَّا مُؤْمِنٌ، وَلَا يُبْغِضَنِي إِلَّا مُنَافِقٌ.


- صحيح مسلم  كتاب : الإيمان  | باب : حب الأنصار وعلي من الإيمان : 78 ( 131 ) : الجزء رقم : 1 : الصفحة رقم : 60.


- سنن الترمذي ( 3736 ).


- سنن النسائي ( 5018, 5022 ).


- سنن ابن ماجه ( 114 ).


- مسند أحمد ( 642, 731, 1062 ).


Idan aka ce: da yawa daga cikin Sahabbai su na zagin Ali(as) (kamar yanda Ibni Taimiyya ya ce), to hakan daidai ya ke da a ce; da yawa daga cikin Sahabbai su na zagin Annabi Muhammad(saw), saboda Annabi(saw) ya na cewa:


"...Duk wanda ya zagi Ali(as); to ni ya zaga..."


Ga nassin hadisin kamar yanda Ahmad bin Hambal ya riwaito daga Ummul-Mu'uminin Ummu Salma:


حَدَّثَنَا  يَحْيَى بْنُ أَبِي بُكَيْرٍ، قَالَ: حَدَّثَنَا  إِسْرَائِيلُ، عَنْ  أَبِي إِسْحَاقَ، عَنْ  أَبِي عَبْدِ اللَّهِ الْجَدَلِيِّ، قَالَ: دَخَلْتُ عَلَى  أُمِّ سَلَمَةَ  فَقَالَتْ لِي: أَيُسَبُّ رَسُولُ اللَّهِ(صَ) فِيكُمْ ؟ قُلْتُ : مَعَاذَ اللَّهِ - أَوْ : سُبْحَانَ اللَّهِ. أَوْ كَلِمَةً نَحْوَهَا - قَالَتْ : سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ(صَ) يَقُولُ: "مَنْ سَبَّ عَلِيًّا، فَقَدْ سَبَّنِي".


- مسند أحمد  مسند النساء.  | حديث أم سلمة زوج النبي(ص) : 26748 : الجزء رقم : 44، الصفحة رقم : 328.


- حكم الحديث: إسناده صحيح، ﺭﺟﺎﻟﻪ ﺛﻘﺎﺕ. ﻗﺎﻝ ﺍﻟﺤﺎﻓﻆ ﺍﻟﻬﻴﺜﻤﻲ: ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺣﻤﺪ ﻭﺭﺟﺎﻟﻪ ﺭﺟﺎﻝ ﺍﻟﺼﺤﻴﺢ ﻏﻴﺮ ﺃﺑﻲ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺠﺪﻟﻲ ﻭﻫﻮ ﺛﻘﺔ. ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﺤﺎﻛﻢ ﺍﻟﻨﻴﺴﺎﺑﻮﺭﻱ: ﻫﺬﺍ ﺣﺪﻳﺚ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻻﺳﻨﺎﺩ ﻭﻟﻢ ﻳﺨﺮﺟﺎﻩ، ﻭﻗﺪ ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻨﺪ ﺍﻻﻣﺎﻡ ﺃﺣﻤﺪ : 6 /  323. ﺍﻟﻤﺴﺘﺪﺭﻙ: 3 / 121. ﺗﺎﺭﻳﺦ ﺩﻣﺸﻖ : 42 / 266. ﻣﺠﻤﻊ ﺍﻟﺰﻭﺍﺋﺪ: 9 / 130. ﺻﻔﺤﻪ 301.


Idan aka ce: da yawa daga cikin Sahabbai su na yakar Ali(as), (kamar yanda Ibni Taimiyya ya ce), to hakan daidai ya ke da a ce: da yawa daga cikin Sahabbai kafirai ne, Saboda Annabi(saw) yana cewa:


"Zagin Musulmi Fasikanci ne, yakar Musulmi Kafirci ne".


"ﺳﺒﺎﺏ ﺍﻟﻤﺴﻠﻢ ﻓﺴﻮﻕ ﻭﻗﺘﺎﻟﻪ ﻛﻔﺮ"


Ga nassin hadisin kamar yanda Bukhari, Muslim... su ka riwaito:


حَدَّثَنَا  مُحَمَّدُ بْنُ عَرْعَرَةَ، قَالَ: حَدَّثَنَا  شُعْبَةُ ، عَنْ  زُبَيْدٍ، قَالَ: سَأَلْتُ أَبَا وَائِلٍ، عَنِ الْمُرْجِئَةِ فَقَالَ: حَدَّثَنِي  عَبْدُ اللَّهِ  أَنَّ النَّبِيَّ(ص)َ قَالَ:  "سِبَابُ الْمُسْلِمِ فُسُوقٌ، وَقِتَالُهُ كُفْرٌ".


- صحيح البخاري  كتاب : الإيمان  | باب خوف المؤمن (6044، 7076، 48) : الجزء رقم : 1، الصفحة رقم : 19.


- صحيح مسلم ( 64 ).


- سنن الترمذي ( 1983, 2634, 2635 ).


- سنن النسائي ( 4105, 4106, 4107, 4108, 4109, 4110, 4111, 4112, 4113 ).


- سنن ابن ماجه ( 46, 69, 3939 ).


- مسند أحمد ( 3647, 3903, 3957, 4126, 4178, 4262, 4345, 4394 ).


Idan ka dauki Imam Ali(as) a gama-garin Musulmi ne; to yakarsa kafirci ne. Doriya akan ingantattun hadisai da suka nuna cewa duk wadanda su ka yaki Imam Ali(as) a Jamal, Siffin, Nahrawan... duk azzalumai ne. Misali, Hadisin Fi'atul-bagiyah...


Kenan Ibn Taimiyya ya na zagin Sahabbai? Ko siffata Sahabbai da Munafinci ba zagi ba ne? Tunda Ibn Taimiyya ya ce: "Da yawa daga cikin Sahabbai su na 'kin Ali(as) (alhali Annabi(saw) ya ce 'kin Ali(as) Munafinci ne)". 


Kenan dai Ibn Taimiyya shima ya na zagin Sahabbai???


Ko Bukhari, Muslim da sauran malaman Ahlus-Sunnah da suka riwaito hadisan; makaryata ne? Ko suma duk su na zagin Sahabbai???


Wani rashin adalci da Ibn Taimiyya ya shahara da shi shine yiwa malamai karya, misali, a littafinsa Minhajus-Sunnah, da ya rubuta don yiwa Allama Al-Hilli radda wa littafinsa minhajul-karama, sai kaji Ibn Taimiyya yace Allama Al-Hilli yace kaza, alhali idan kaje ka duba minhajul-karama sai ka tarar Ibn Taimiyya karya ya ke jinginawa Allama Al-Hilla, ko ka tarar Allamah Al-Hilli ya yi gabas, Ibn Taimiyya ya yi yamma. Don haka malamai ke cewa; Ibn Taimiyya a saman iska ya ke sakin kalamansa ba tare da hujja ko dalili ba.


IBN TAIMIYYA ZINDIKI (MARAR ADDINI) NE, MUNAFIKI NE... A MAHANGAR MALAMAN AHLUS-SUNNAH. INJI IBN HAJAR AL-ASKALANI:


Ibn Hajar Al-askalani ya na cewa:


"Mutane (malaman Ahlus-sunnah) sun yi sabani akan matsayin Ibn Taimiyya:


Wasu su na ganin Ibn Taimiyya ya mayar da Allah(swt) jiki (Tajsim), tunda ya ce; Allah(swt) ya na da hannu, kafa, kori, fuska... na hakika (ba tawili)...


Wasu su na ganin Ibn Taimiyya marar addini ne kacokaf, saboda ya [alamta Annabi(saw) mutum ne kamar kowa]; don haka ba a tawassuli da Annabi(saw)...


Wasu su na ganin Ibn Taimiyya munafiki ne, saboda kiyayyarsa ga Imam Ali(as) da wasu muhimnan Sahabbai. Misali Ibn Taimiyya ya ce:


Imam Ali(as) ya yi muhawala bayyi nasara ba (duk yakin da Imam Ali(as) ya yi baya nasara...


Ibni Taimiyya ya ce:


Imam Ali(as) ya yi ta neman khalifanci bayyi nasara ba, ya na da son shugabanci, ya yi yaki don neman shugabanci.


Ibn Taimiyya ya ce:


Khalifa Usman ya na da son dukiya. Khalifa Abubakar ya musulunta ya na tsoho, yayinda bai san me ya ke ba, Imam Ali(as) ya musulunta ya na yaro, imanin yaro bai inganta":


قال بن حجر العسقلاني:


وَأطلق ابْن تَيْمِية إِلَى الشَّام وافترق النَّاس فِيهِ شيعًا فَمنهمْ من نسبه إِلَى التجسيم لما ذكر فِي العقيدة الحموية والواسطية وَغَيرهمَا من ذَلِك كَقَوْلِه أَن الْيَد والقدم والساق وَالْوَجْه صِفَات حَقِيقِيَّة لله وَأَنه مستوٍ على الْعَرْش بِذَاتِهِ...


وَمِنْهُم من ينسبه إلى الزندقة لقَوْله أَن النَّبِي(ص) لَا يستغاث بِهِ وَأَن فِي ذَلِك تنقيصاً ومنعاً من تَعْظِيم النَّبِي(ص)...


وَمِنْهُم من ينْسبهُ إِلَى النِّفَاق لقَوْله فِي عَليّ مَا تقدم وَلقَوْله إِنَّه كَانَ مخذولا حَيْثُ مَا توجه وَأَنه حاول الْخلَافَة مرَارًا فَلم ينلها وَإِنَّمَا قَاتل للرئاسة لَا للديانة وَلقَوْله إِنَّه كَانَ يحب الرِّئَاسَة وَأَن عُثْمَان كَانَ يحب المَال وَلقَوْله أَبُو بكر أسلم شَيخا يدْرِي مَا يَقُول وَعلي أسلم صَبيا وَالصَّبِيّ لَا يَصح إِسْلَامه... فألزموه بالنفاق لقَوْله(ص) وَلَا يبغضك إِلَّا مُنَافِق...


- الدرر الكامنة في أعيان المائة الثامنة : ابن حجر العسقلاني : ذكر من اسمه أحمد، ج 1، ص 180 - 182. مجلس دائرة المعارف العثمانية صيدر أباد، الهند، الطبعة الثانية، 1972 م. عدد الأجزاء : 6.


Tunda hadisin ya inganta; ba mai kin Imam Ali(as) sai munafiki:


ﻭﻻ ﻳﺒﻐﻀﻚ ﺇﻻ ﻣﻨﺎﻓﻖ.....


Kenan da Ibn Taimiyya munafiki ne; unda baya son Imam Ali(as)???


➖➖➖➖➖➖➖➖➖

Abdulrahman Murtala - abdulrahmanyj@gmail.com


🌹🌈🌹🌈🌹🌈🌹🌈🌹voiceofsheikh@gmail.com

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky