DAKARFIN TSIYA AKA NEMI BATAR DA IMAM ALI AMMA BAI ƁATU BA

DA KARFIN TSIYA AKA NEMI A BATAR DA IMAM ALI (A.S) AMMA BAI BATA BA.

Inji Sheikh Ibraheem Zakzaky (H)
Ga link din da zaku bi mu turo muku videon jawabin https://chat.whatsapp.com/DqxEcgD8udZKgQQIsyc9LT

Da karfin tsiya aka nemi batar da imam Ali (As) Amma bai bata ba aka dauki darajijinsa duk aka ba kowa amma duk da haka dai sai da yayi banbaro yafita daban, to yanzu lokacin da Allah yaga daman asan gaskiya ne kuma yaga damar a fada,
Na'am har yanzu munajin tsoro akwai abinda bama fada, ba domin munajin tsoron mahukunta ba don su mahukuntan sunce ba ruwan su da addini amma da'ace mahukunta sun tabbatar da addinin da ransu yake so ne ko kayi ko a yanka ka to da shi ne amma yanzu mahukunta sunce ba ruwansu da addini mutum yayi addinin da yaga dama 
Na wani hakimi yace ko kyankyaso kake so sai ka bauta mar, tsabar isgili ma yace wannan kazamin kwaron ma yana iya zama uban giji   

To ba su mukejin tsoroba tsoron mu shine kar mu gayawa mutum magana domin ya shiriya yazo ya bace to muna ji masa wannan tsoron don gudun kar mu gaya masa magana ya fitinu mai makon ya shiriya ya bace,to shine sai muyi shiru don haka har yanzu ana nan ana boye boye badon komai ba sai don kar a fitini munini 
Domin Shi Amiril muminin yana cewa  KUYI MAGANA DA MUTANE DAI DAI HANKULAN SU KO KUNA SO SU KARYATA ALLAH NE? Sai ka gayawa mutum Allah yace sai wani yace  karya ne, to waya karyata? Ya karyata Allah sabo da haka bazakayiwa mutum maganar datafi karfin hankalinsa ba don zai ce karya ne in yace karya ne kuma ya halaka sabo da haka kayi magana dashi daidai yadda zai iya fahimta sabo da haka wasu abubuwa dole daidai yadda zaka iya fahimta za'a gaya maka.

Kamar yadda Amiril muminin yake cewa AL'AMARIN MUFA ABU NE MAI WAHALAR GASKE ABU NE MAWUYACI BA MAI KARBAR SA SAI MUMINI DA ALLAH YA TATSO IMANI DAGA ZUCIYAR SA Abu ne da in an fada zuciya nan da nan zata ce dan me aka gaya Amma sassaukan abu ne in Allah ta'ala ya hore maka daraja ce Allah ya amince, to meye naka nace miyasa Allah yayi kaza meyasa Allah yayi Aljanna meyasa yayi wuta meyasa zai kona wasu babu dalili ne? akwai yawwa.
Amma kai ne wayene zaka ce Allah meyasa yayi kaza meyasa wane da wane ne allah ya zaba suka zama annabawa, allah ta'ala baya zalunci amma ba'a tambayar sa dangane da meyasa yayi kaza duk abin da yayi yana dorashi bisa hikima ne,to wannan abu ne mawuyaci sai wanda Allah ya tatso imani a zuciyar sa ..

Wani bangare na jawabin Sheikh Ibraheem zakzaky kenan, masu bukatar Videon jawabin suna iya Shiga link din mu na whatapp mai  suna JAWABAN SHEIKH ZAKZAKY A RUBUCE.

✅Mujaheed D Umar Giwa.

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky