HOTUNAN GASAR FARETIN SAYYIDA FATIMA A KATSINA 21/2/2021
Get link
Facebook
X
Pinterest
Email
Other Apps
-
Yan uwa musulmi Al'majiran Sheikh Ibrahim Zakzaky na yankin katsina sun gudanar da Faretin girmamawa ga Diyar manzon Allah sayyida Fatima a garin katsina, ga Hotunan
Wane Ne Sheik Abul Fatahi Maiduguri? Daga Aliyu Ahmad . Cikakken sunansa shine Sheik Ahmad Aliyu Yarwa amma ana yi masa lakabi da Sheik Abul Fatahi. Ya rayu a duniya shekaru 82, kenan an haife shi a shekarar 1919. Da rasuwarsa yau shekaru 17 kenna, domin ya rasu ne a shekarar 2003. . An haife shi a wani kauye da ake kira Sandiya amma an fi saninshi da Shanduwa a yanzu, a gundumar Konduga ta jihar Borno. A nan ya taso har ya iya hawan doki da al'adun kauye. NASABARSA: Sheikh Ahmad bin Aliyu bin Ahmad bin Aliyu bin Muh'd Mustapha bin Muh'd Mukhtar bin Adam bin Dawud bin Abdulganiyyu bin Zubair bin Abbas bin Hussain bin Suleiman bin Ishaq (ta kan wannan suka hada kaka daya da Sheik Ahmad Tijjani) bin Aliyu Zainul Abideen bin Ahmad bin Muh'd Nafsu-Zakiyya bin Abdullahil-Khamil bin Hasanul-Musanna Bin Hassan bin Aliyu wa Fadima Bintu RASULILLAHI SAW. . Ta bangaren mahaifiya kuwa jikan Yarima Zubairu ne Sarkin Adamawa, sunanta Aishatu bintu Alh Muh'd wa Hauwa'...
Tarihin Shaikh Yakubu Yahaya Katsina A Takaice. Da sunan Allah mai Rahma mai Jinkai. Tsira Da Amincin Allah Su Kara Tabbata Ga Fiyayyen Halitta, Manzon Tsira Da Iyalan Gidansa Ma'abota Shiriya Da Shiryarwa. Garin, Shekara Da Wajen Da Aka Haifi Shaikh Yakubu Yahaya Katsina. An haifi Shaikh Yakubu Yahaya Katsina a ranar 15 ga watan Rajab,1376 Hijiriyya (1955 Miladiyya) a Unguwar Adoro da ke gab da Unguwar-madawaki a tsakiyar birnin Katsina. Mahaifansa. Maihaifinsa Alhaji Malam Yahaya, haifaffen karamar hukumar Rimi ne ta Jihar Katsina. Malama Maryam, mahaifiyarsa, 'yar asalin karamar hukumar Mani din Jihar Katsina ce. Ita 'ya ce ga Malam Zubairu, shi kuma Malam Zubairu da ne ga Malam Aliyu, dukansu haifaffun Karamar hukumar Rimi ta jihar Katsina ne. Iyalansa. Yanzu haka Shaikh Yakubu Yahaya yana da Mata biyu da 'ya'ya shatakwas: Tara Maza, Tara Mata. Ya aurar da guda Tara (tsakanin Maza da Mata), Yanzu Saura guda Tara. Karatunsa. A farkon farawa Malamin y...
Taron Matasa Karo Na 27 A Garin Bauchi: Rahoto Na Biyu: Nasihohin Sheikh Yakubu Yahaya Ga Matasa Daga Bilya Hamza Dass “Ba sai anzo wajan taro (Mu'utamar) kafin a dinga tashi ana sallar dare ba, wannan wani abu ne muhimmi, hasalima yana daga cikin manyan alamomi da ake gane mumuni” inji shi. A wani bangare na jawabin nashi babban bako me jawabi a wajan Sheik Yakubu Yahaya yaja hankalin matasa wajan kula da Ibada musamman a shekarun su na matasan taka. Yace “Abinda su Mallam suke so shine su samar da wasu mutane wadan da Allah zai damka musu amanar al'umma, wadanda zasuce Allah yayi kuma yayin” kuma wannan alkawari na shi. Yakawo misalai yanda Allah yake zabar wasu dai-daikun bayin shi ya damka musu amanar al'umma, yayin da yaga tsaran su greshi da kuma amanar su. Misali Imam Kumai ni (R) da Shehu 'Dan Fodiyo wadanda wadanan sun faru shekaru kadan baya. Yace to wannn shine hankoron su Mallam (H) yace ya bayyana ba sau daya ba, cewa babbn gudumawa da wani zai baya...
Comments
Post a Comment