SHEKARARSA 70 A DUNIYA...A cikin wannan shekarun ya kwashe da yawansu cikin Ibtila'I na zalumcin azzalumai- Rahama Abdulmajid

SHEKARARSA 70 A DUNIYA...
A cikin wannan shekarun ya kwashe da yawansu cikin Ibtila'I na zalumcin azzalumai.
1 Shekara shida kenan da aka daure shi daga shi har matarsa 
2 A cikin wannan shekarunsa Saba'in Gwamnatoci suka karar da 'ya'yansa.
3 A cikin wannan shekarun an kashe dubban mabiyansa maza da mata manya da yara har da na goye da suke asalin yan Najeriya masu hakkin tsaro da kare lafiya a wuyan gwamnati.
4 A cikin wadannan shekarun aka rushe duk wani waje da ya mallaka 
5 a cikin wannan shekarun ne Kotu ta rika bayar da belinsa gwamnati na take umarnin kotu.
6 A cikin wannan shekarun duka bai kira mabiyansa da su dauki makami kamar yadda inyamurai ke dauka su kwana lafiya, yarbawa ke dauka su kwana lafiya, Fulani ke dauka su kwana lafiya. 
7 Laifinsa daya shine ya zabi hanyar da ya ke ganin ita ce addininsa a kasar da kundin tsarin mulkinta  yace kowa na da 'yancin yin addini yadda yake so cikin walwala.

DA INA DA DAMAR BAYAR DA AWARD HAKIKA ZAN BAIWA SHEKH ZAKZAKY AWARD DIN JAGORAN ZAMAN LAFIYA A KASAR NAN. 
ALLAH YA KUBUTAR DA KAI YA BAKA LAFIYA, YA SAKA MAKA

Comments

Popular posts from this blog

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEIKH YAQUB YAHYA KATSINA

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky