YAKIN BADAR BABBAR NASARACE GA MUSULUNCI

Yakin Badar Babbar Nasara Ce Da Ke Tabbatar Da Kafuwar Daular Musulunci, Inji Farfesa Danladi Daga Ammar M. Rajab Farfesa Abdullahi Danladi, Malami a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya ya bayyana cewa yakin Badar babbar nasara ce da ke tabbatar da cewa daular Musulunci ta kafu babu mai iya nuna mata dan yatsa. Farfesan ya bayyana hakan ne a yayin muhadara kan ranar Badar da ya gudana a jiya Alhamis 17 ga watan Ramadan 1442 a garin Zariya. Taron ya gudana ne a muhallin Fudiyya dake Babban Dodo Zariya. A kowacce rana cikin watan Ramadan, ana gudanar da Tafsirin Alkur’ani mai girma wanda Shaikh Abdulhameed Bello ke jagoranta, sai dai a jiyan an gudanar da muhadara ce kan ranar Badar wanda Farfesa Abdullahi Danladi ya gabatar da jawabi. Farfesa Abdullahi Danladi ya kawo tarihin yakin Badar tiryan-triyan, harma ya nuna yadda tun daga yakin Badar da aka yi, aka samu fasahar amfani da ‘camouflage’ da dakarun sojoji suke amfani da shi a yau. A wani bangare na jawabinsa, Fa...