Posts

TARIHIN SHEIKH ZAKZAKY DAGA BAKIN SA 2

Image
TARIHIN SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY DAGA BAKINSA (2) — Daga Littafin HARKAR MUSULUNCI Na Cibiyar Wallafa Cigaba.... A lokacin da nake jami’a akwai wani yanayi da na samu, wanda kuma shi ya taimaka wajen canza rayuwata. Lokacin da na shiga (jami’a) kamar kowane dalibi, fatata shine na kammala jami’a wala’alla na je na kama aiki, ko kuma ma na cigaba da karatu a nan jami’a din, to amma yanayin da muka samu kanmu a ciki a wannan lokacin na karshen 70s, kamar za a iya cewa akwai musayar ra’ayi dangane da abin da ya dace ya zama makomar kasa. Lokacin kwaminisanci na tashe sosai, kuma da yawan dalibai da suke nuna sun waye, Kwaminisanci suke yi. Haka suma cikin Lakcarori wadanda suke nuna su cigababbu ne to Kwaminisanci suke. Saboda haka Kwaminisanci kamar shine wata alama ta cigaba. Kuma Kwaminisanci na da matsalar cewa suna ganin addini kamar wani mummunan abu ne. Kuma su kan ta yin hujumi a kan addini baki daya, da kuma musamman ma Muslunci. Suna ta sukan Musulunci, suna nuna kamar ...

TAURARUWAR AREWACIN NIGERIA-Nana As'ma'u

Image
Tauraruwan Arewacin Nigeria A Qarni Na Sha Tara: Nana Asma'u  Bint Fodio. By Anas Lawal A tarihin ƙasar nan anyi jarumai Maza da yawan gaske amma Mata Kadan ne tarihi ya tuna dasu, a ƙarni na Sha Tara, an samu jajirtacciyar mace, Malama, yar uwa, gimbiya, uwa, kuma marubuciya daga gidan mujaddadi shiekh Usman Dan Fodio (1754-1817) wato Nana Asama'u bnt Fodiyo. Haihuwar Ta An haifi Nana Asama'u ne shekarata 1793/4, shekaru 11 Kafin kafa Daular Sakwkkwato, a garin Ɗegel ga shehu mujaddadi, an haifeta ne a matsayin tagwaye amma Dan uwanta ya rasu tun Suna qanana. Shehu ya sanya mata Suna Asama'u ne Domin tuna Sahabiyyar nan Mai daraja Nana Asama'u bnt Abubakar Saddiq. Nana Asama'u ba fullatana ce yar Qabialar Toronkawa. Gidan Su kuwa gidan Malamai, Abdullahin Gwandu Baffanta  ne Muhammad Bello kuma Yayanta ne Dan Fodio kuma Mahaifinta. Karatun Ta Malama Asama'u tayi karatun addini Mai zurfi  awurin mahaifinta Dan Fodio, da sauran malaman gidansu. Ta...

TARIHIN SHEIKH ABUL FATHI MAIDUGURI

Image
Wane Ne Sheik Abul Fatahi Maiduguri? Daga Aliyu Ahmad . Cikakken sunansa shine Sheik Ahmad Aliyu Yarwa amma ana yi masa lakabi da Sheik Abul Fatahi. Ya rayu a duniya shekaru 82, kenan an haife shi a shekarar 1919. Da rasuwarsa yau shekaru 17 kenna, domin ya rasu ne a shekarar 2003. . An haife shi a wani kauye da ake kira Sandiya amma an fi saninshi da Shanduwa a yanzu, a gundumar Konduga ta jihar Borno. A nan ya taso har ya iya hawan doki da al'adun kauye. NASABARSA: Sheikh Ahmad bin Aliyu bin Ahmad bin Aliyu bin Muh'd Mustapha bin Muh'd Mukhtar bin Adam bin Dawud bin Abdulganiyyu bin Zubair bin Abbas bin Hussain bin Suleiman bin Ishaq (ta kan wannan suka hada kaka daya da Sheik Ahmad Tijjani) bin Aliyu Zainul Abideen bin Ahmad bin Muh'd Nafsu-Zakiyya bin Abdullahil-Khamil bin Hasanul-Musanna Bin Hassan bin Aliyu wa Fadima Bintu RASULILLAHI SAW. . Ta bangaren mahaifiya kuwa jikan Yarima Zubairu ne Sarkin Adamawa, sunanta Aishatu bintu Alh Muh'd wa Hauwa'...
Image
🌐 *Kauna Da Yanke Kauna* 🌐 Kafin bayyanar Musulunci, dan’Adam dai ya rayu cikin yanayi na jahiliyya mai tsanani cikin karnoni da dama, kafin daga baya hasken Musulunci da shiriyar da Manzon Allah (s.a.w.a) ya zo da ita ta bayyana ta kuma haskaka duniya. A wancan lokacin dai dan’Adam yana rayuwa ne cikin yanayi na dar-dar da yanke kauna, sai dai kuma lokacin da ya ji kalmar ‘yanci daga bakin Mai Albishir, Manzon Allah (s.a.w.a) yana kiransa zuwa ga shiga jirgin ‘yan’Adamtaka, nan take ya bude zuciyarsa, ya kuma karbi wannan kira na kauna da fatan alheri. Haka dai lamarin yake, a duk lokacin da aka samu duhun jahiliyya ya mamaye duniya, al’umma suka yanke kauna da fata, sai a samu wani sako na Ubangiji da zai zo ya yaye wannan duhu daga kan al’umma ya kuma dawo musu da kauna da kuma fatan da suke da shi. *وَ إِنْ مِنْ أُمَّةٍ إلاّ خَلاَ فِيها نَذِيرٌ* *“Kuma babu wata al’umma face wani mai gargadi ya shude a cikinta”.* (Surat Fatir: 24). Haka dai hasken Alqur’ani ya ratsa...

Iman Mahdi Al' muntazar

🌐 *Imam Mahdi Al-Muntazar (a.s)* 🌐 Rikici tsakanin alheri da sharri a doron kasa dai ya faro ne tun daga farko-farkon wannan duniya kuma wannan gasa da rikici zai ci gaba tsakanin tafarkuna bbiyn; wato tafarkin shiriya da tafarkin bata; tafarkin Annabawa da tafarkin ma'abota girman kai. Hakika sakon Musulunci ya samu nasara ta hannun Manzon Allah (s.a.w.a) kuma haka wannan tafarki ya ci gaba har ya gina tafarkin tauhidi, ya ciyar da dan’Adam gaba bisa tushen ilmi da imani, ya haskaka shi  da wannan haske kana kuma ya shiryar da shi da wannan shiriya madaukakiya. To sai dai kuma daga baya wannan tafarki ya fara yin rauni, lokacin da wasu akidu da wayewa na jahiliyya suka fara kunno kai, aka fara samun koma baya a wayewa ta Musulunci, aka hana dan’Adam rayuwa karkashin inuwar imani, gaskiya, adalci da zaman lafiya. A bangare guda kuma zalunci ya ci gaba da yaduwa a fadin duniya, al’adun jahiliyya suka fara samun gindin zama, har muminai suka fara yanke kauna, idan da ba don s...

TARIHIN SHEIKH ZAKZAKY DAGA BAKIN SA

Image
TARIHIN SHAIKH ZAKZAKY DAGA BAKINSA (1) — Daga Littafin Harkar Musulunci na Cibiyar Wallafa Bismillahir  Rahmanir Raheem. Sunana Ibraheem Zakzaky. An haife ni ne a Zariya an shekara ta 1953 Miladi, wanda yayi daidai da Hijiri Kamari 1372. Mahaifina Malamin Alkur’ani ne, haka ma kakana, shima Malamin Alkur’ani ne, haka ma shima uban kakana. Sai dai shi uban kakana da kuma kakan nawa a lokaci guda suna karantar da karatun littafi irin su Fiqihu da ire-irensu baya ga karatun Alkur’ani. Amma duk cikarsu mahaddata ne, kuma kwararru a kan Alkur’ani din. Kuma har wala yau su kan hada da yin noma a matsayin hanyar rayuwa, baya ga koyar da karatun Alkur’anin. To, haka nan kuma ita ma mahaifiyata, bangaren gidansu suma Malamai din ne. Da yake tsarin rayuwa a wajenmu a da, kusan kowane abu iyali ke yi. Wato akwai wadanda suke sarakai ne, akwai wadanda suke Malamai ne, akwai wadanda kuma ‘yan kasuwa ne. To, ni ta bangaren uwa da ubana duka abin da ya shafi Malinta suke yi. Na’am, a...

TARIHIN SHEIKH ZAKZAKY (H)

Image
TAKAITACCEN TARIHIN SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H) Daga Cibiyar Wallafa An haifi Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky a cikin birnin Zariya, a ranar 15 ga Sha’aban 1372 (May, 1953). Iyayensa Malaman Alkur’ani ne, suna karantarwa da kuma yin noma a matsayin hanyar gudanar da rayuwa. Don haka Shaikh Zakzaky yana tasowa ya fara karatun Alkur’ani a wajen Mahaifinsa. A daidai lokacin da yake karatun Alkur’ani a wajen mahaifinsa, an kuma saka shi a wata makarantar Alkur’ani a lokaci guda, yana zuwa makaranta yana kuma yin karatu a gida. Sannan kuma yana raka mahaifinsa tare da ‘yan uwansa zuwa gona don aiki. A ka’idar gidan su Sayyid Zakzaky a wancan lokacin sai yaro ya sauke Alkur’ani sannan yake saka littafan addini ya karanta a zaurukan Malamai. Don haka lokacin Shaikh Ibraheem Zakzaky yana dan shekaru 14 ya sauke Alkur’ani, nan take ya saka littafai ya fara karatun addini a wajen Mahaifinsa, mahaifiyarsa da kuma wasu Malamai a zaurukansu a cikin birnin Zazzau. ...